Ammie ke magana cike da bala'i.

Kowa turus yayi yana kallonta,kukan Jahda ne kaɗai ke tashi ,zuciyoyin kowa cike da  tunani da ruɗani ,Alhaji Jalal sam ya kasa magana,ya zira ma Jahda idone kawai yana nazarin maganan ta,yana kuma kallon mahaifiyarta,don ko kaɗan baiji maganan nan akwai ƙamshin gaskiya acikin ta ba.

"Da ƙyar ya iya cewa ku tashi muje gida ayi magana".

Adaƙile yai maganan,yana gamawa yasa kai ya fice fuuuuu,Jawahir tabi bayan shi,yayinda Juliet ta tashi a saluɓe tafita kamar kazan da ƙwai ya fashe mata aciki,Jasmin miƙewa tayi tabi bayan su.

"Ammie wai maike faruwa ne?.

Faɗar Jadida dake tsaye cike da mamakin jin Jahir yai ma Jahda ciki tayaya bayan ko kallonta bayayi.

"Ke muje gida zakiji komi".

Faɗar Ammie dake ƙoƙarin tada Jahda don ta taimaka mata sufito.

"Wai Ammie mai kuke ɓoyemin keda sis?.

Ta ƙara tambaya a hasale.

"Ke banson iskanci ,ciki bana Jahir bane kuma dole ya amsheshi ko yanaso ko baiso ni zaigwada mai iskanci,dole ya aure Jahda".

Cike da raɗa take ma Jadida magana.

Yayinda Jadida tai baya sabida tsoro lallai mahaifiyarsu ta wuce da saninta.

Bankaɗeta tayi suka wuce,jiki a sanyaye tabi bayan su,duk ta gama tsorata da lamarin mahaifiyar su.

hakanan tabi bayan su suka shiga motor har gida kowa da abinda yake saƙawa a zuciyar shi.

***** *AFTER SOME MUNITES*

Packing ɗin Dady kenan Jaheer ya fito daga side ɗin su yana ɗaura a gogon hannun shi,yana nufar motor shi da alaman fita zaiyi.

Ganin sun dawo da fara'an shi yana kallon Juliet yana mata murmushi mai kashe zuciya.

Sheƙeƙe ta kalle shi tana wurga masa harara tare da jan tsaki tayi gaba.

Da mamaki yake kallon ta ,kanshi yayi mugun ɗaurewa,ƙarfin hali yayi ya dubi  Alhaji Jalal yace Dady sannu da dawowa".

Wani kallo Alhaji Jalal ya watsa masa a daƙile ya amsa.

Ammie ko aikin harara take wurgin Jahir dashi ,yayinda Jawahir ta fashe da kuka ta ruga side ɗin Hajiya Mama da gudu.

Jahir kanshi ɗaurewa yayi,Juliet ta harare shi da jan tsaki abinda ko a mafarki bai zato ba,Dady ya amsa mai magana a daƙile,inda sabo ko ya saba da hararan Hajiya Jamila,amma kukan mai Jawahir takeyi?,tambayan da bashi da bashi da amsan ta.

"Kabiyo ni side ɗin Mama".

Dady yai maganan cikin haɗa rai mai ɗauke da kakkausar murya.

Ammie riƙe hannun Jahda tayi sukai hanyar side ɗinsu.

Hajiya Jasmin ko kamar ta haɗiye zuciya ta mutu,haushi takaici,cike da tausayawa take kallon Jahir don tasan sharrin Jamila ne,Jahir sam bazai aikata ba.

Da ƙyar taja ƙafarta tabi bayan mijinta,haka shima Jahir jiki a saɓule yabi bayan Dady su.

******
Faɗawa tayi kan cinyar kakanta tana matsanan cin kuka.

Hankalin Hajiya Kaka ya tashi tana tambayanta ko Jahdan ta mace ne?.

Kuka take sosai kamar  ranta zai fita.

Shigowan Jalal ne yasa Mamah ta maida tambayan da take ma Jawahir kan sa.

Zama yayi yai shiru,daidai lokacin Jahir ya shigo bayan shi Hajiya Jasmin ne.

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now