Cike da rashin mutunci take magana.

Abie kota kanta baibi ba ya daka ma Jahda tsawa dake zaune tana turo baki aiko zabura tayi ta miƙe da gudu ta tafi ɗauko ruwan.

Ƙwafa tayi ta koma ta zauna taci gaba da jan tsaki.

Aladafce Jahda ta kawo ruwan ta aje ma Juhurah da cup ,kafin ta koma ta zauna  tana turo baki ƙasa-ƙasa.

Gyaran murya Hajiya Mama tayi kafin ta fara magana kamar haka.

"Dafarko dai bari mi abinda ya haɗa ma,ba hayaniya da ɗaga  murya ba,Jabeer kai masu bayani ko kai Jibiril".

Cikin sanyin murya Hajiya Mama ke maganan.

Alhaji Jibiril mahaifin su Jaheer shine ya muskuta yai gyaran murya yace," dafarko dai afara buɗe taro da addu'a.

Addua ya rinƙa kwararowa tsawan minti goma kafin aka shafa.

Daganan yaci gaba da faɗin,a matsayin mu na iyaye masu zumunci kuma wa ƴanda suka isa da ƴaƴan su ,mude dattawa ne na gari in mun yanke hukunci ba wanda ya isa yace ba haka ba ko ya juyamana ra'ay".

"Hakane" faɗan Albanian Jamal ataƙaice mijin Hajiya Jumainah.

Falon ƙara ɗaukan shiru yayi,kowa yana son yaji mai za'a yanke.

Shiru Abbu yayi na ɗan wani lokaci kamai mai nazarin wani abu kafin yaci gaba da faɗin,"mun yanke hukun haɗa Juliet ƴar gidan Yaya Jabeer aure da ɗan wajena Jaheer".

Falon take ya ɗauke farinciki saɓanin Jahda da Jadida da Hajiya Jamila da Hajiya Jumainah.

"Shima Jahoor yafito fa tashi,haka Jahda da Jadidah duk ba wanda ya rasa masoyi acikin ku duk kufito da naku da Jawahir".

Faɗan Alhaji Jalal mijjn Hajiya Jasmin.

Abie ne yai gyaran murya yafara magana kamar haka"burin kowani mahaifi akan ƴaƴan shi bayan ya haife su ya tarbiyantar dasu ya ilimintar da su babu kuma abinda zai ƙara mai yamasa babban gata sai ya aurar da su,aure sunan manzo ɗan Amina".

Hajiya Mama gyaɗa kai kawai takeyi tana gamsuwa da maganan ƴaƴanta.

Yayin da matan su ko kowa shiru yayi saɓanin bakin Hajiya Jamila bakinta rawa kawai yake yai magana.

"Jahoor muna sauraran ka ,wa ka tsayar ƴar gidan wanene?.

Alhaji Jalal ke maganan  ,lokaci ɗaya kowa kallon shi ya koma gare shi saɓanin Jawahir da  tayi ƙasa da kanta gabanta na bugawa kar Jahoor ya kira sunan wata ba ita ba,duk da tana s tabbacin soyayyan da suke ma juna ɗari bisa ɗari.

Gyara zaman shi yayi yaɗan ƙara shan kunu kamar ba zaiyi magana ba,can kuma yace,Abba ba kowa bace fa Jawahir ce itace zan aura muna soyayya".

MashaAllahu iyayen suka rinƙa faɗa Hajiya Juwairah ko farin ciki bakinta yaƙi rufuwa,haka Hajiya Mama da duk masoyan Jawahir.

Jawahir ƙasa tayi da kai ta tura cikin cinyoyinta sabida kunya.

Hajjiya Jamila ko miƙewa tayi ta lailayo ashar ta watsa da saida kowa yayi mamakin ashar ɗin da tayi.

"Ni za'a munafinta ,ni zaa raina ma hankali,ai Jahdah da Jaheer soyayya sukeyi ,amma dayake abin na munafinci da munafukai ne dole  a haɗa shi da arniya mai warin najasa,sannan wallahi ban yafe ba inde Jahoor zai aura Jawahir sai na ɗaga masa nono ya kasa amfana a duniya".

Cikin ɗaga murya take maganan.

Duk da ran Hajiya Juwairah batason Juliet ko kaɗan amma yanzun tana ɗanji gwamma Juliet da Jahda,don yanzun Jahda bata ganin mutuncinta ko kaɗan ,kuma zata rama cin mutunci da cin fuskan da Hajiya Jamila tayi mata bazatayi magana ba.

"Ke Jamila kishiga hankalinki mu ba tsofaffin banza bane,sannan inde muna numfashi gaba ɗayan mu anan sai anyi auranan san kai kawai don ke sakarya ce ,tou saide Jahadah ta mutu in mutuwa zatayi amma ba fashir auran Jahir da Juliet".

A tsawace Abie ke magana cike da tsan-tsan ɓacin rai.

Wani mugun ƙara Jahda ta sake ta faɗi ƙasa wanwar a sume.

Kanta Jadida da Jawhir da Juliet sukai suna girgizata goran ruwan da aka kawo ma Juhura Juliet t ɗauka ta zuba mata amma ko motsi aka ƙaro ruwa ko motsi.

Jahir ko yana kallo ,ƙyamarta yake yasa bazai iya taɓata ba.

Jahoor miƙewa yayi yafice don baison ko hayaniya wannan ma da yashiga kanshi har yafara bugawa.

Hajiya Jasmin ne tace,"akaita asbiti".

Abie miƙewa yayi yace," ke Juhura miƙe mu shige ta mutu mana".

Gaba yayi batare da ya jira mai zaa ce ba ,bin bayanshi Juhura tayi.

Ɗaukanta akayi akafitar da ita hankalin Hajiya Jamila ya tashi ihu kawai take kurmawa  tana faɗin ankashe mata ƴa an huta.

*******
A&E aka shiga da ita kowa da yazo asbitin  hankalin shi a tashe.

Take likitoci da  nurse suka rufe akanta.

Shuɗewan awa ɗaya  kafin aka ceto rayuwar ta.

Bayan Dr yafito ya umurce Alhaji Jalal da ya biyo shi.

*********
Bayan sun shiga office Dr ya mai bayanin  abinda ke damunta, firgici ne yaja mata dogon suma ,akiyaye gaya mata abinda bashi bane ciwon zuciya na gafda kamata mai tsananin ,rubuce-rubucen magunguna yayi tare da sallama in ta tashi.

Har zai miƙa masa takaddan da ya rubuta sai ya ɗan tsaya

Gyara  murya ya ƙara yi yace,"Alhaji ina mijinta?.

Murmushi Alhaji  Jalal yayi yace Dr bata da miji yanzun muke niyan aurar dasu".

Shiru Dr yayi yana kallon Alhaji Jalal.

Kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace,"a gaskiya Alhaji ƴarku tana ɗauke da cikin sati biyar".

A wani razane Alhaji Jalal ya miƙe take zufa ta fara karyo mai cikin rawan murya yace," Dr gasssskkeee ko wasa,ka gwada daidai kuwa".

"Nasan aikina zan ma ƙarya ne,ka kwantar da hankalin ka,kuje ku tuhumeta inda ta samo shi amma tabbas ƴarku na da juna biyu".

Cikin kwanciyar hankali cike da ƙwarewa  akan aiki yake maganan.

Hasbunallahu wa niimal wakil,innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai Alhaji Jalal ke maimaitawa.

Godiya yai ma Dr ya  fita jiki a sanyaye.

Hajiya Jasmin da ta hangoshi yanayin yanda yafito ta taho da sauri tana faɗin," lafiya Alhaji?.

"Jasmin ina lafiyaJasmin ,Jahdah ta ɓata wayonta Jahda ashe har maza takebi cikine da ita".

Cike da tashin hankali yake maganan.

Ciki Amie ta faɗa da ƙarasowar takenan inda suke tsaye.

Ciki faɗan Jawahir a tsorace tana zaro idanu.

Kowa cike da mamaki yake maganan.

Da gudu Hajiya Jamila ta juya ta nufi ɗakin da Jahda ke kwance.

Idonta biyu don bacci mai nauyi ya kasa ɗaukanta amon muryan Abie ke dawo mata a ƙwaƙwalwa kawai.

Awani sukwane Amie ta cakumota tace..........!

*MRSBASAKKWACEPINKY*

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now