Dai-dai lokacin su Hajiya Jamila suka shigo gidan a motor Hajiya Jumaina dama suka fita.

"Keee ina zaki ".

Faɗan Hajiya Jamila dake ƙoƙarin buɗe ƙofar motor ta sakko ƙafa ɗaya waje.

"Sannu da zuwa Ammie".

"Tambayanki nake?.

"Yaya zankai ma abinci".

"Abinci dama ke kike kai mai koko anbaki kin barbaɗa mai ne a mallake min ɗaa".

Cike da tuhuma take mata magana.

*MATSALAN MAI BIN BOKA KENAN GANI YAKE KOWA MA ZUWA YAKE🤦‍♀️*

Arazane ta ɗago ta kalle Ammie don da kanta na ƙasa ne cike da mamakin maganan ta ,sai kuma ta waske tace,"shiyace in kawo mai".

"Jeki kai mai ki maza ki fito kuma".

Gyaɗa kai tayi ta wuce ba tare da ta kuma magana ba don tana gafda gayama Hajiya Jamila magana ,don taga matan nan yanzun kanta da mahaifiyarta tsanan ta ke juyowa.

"Kisa ido ga ɗanki sosai  don wallahi sam yanzun ban yarda da Juwairiya ba".

Faɗan Hajiya Jumainah.

"Ina zan tsaya kallon ruwa kwaɗo yamin ƙafa,saide ko ayi bani gishiri in baka manda,tana kallo ɗanta ke wulaƙanta min ƴa bata taɓa magana ba ai,saini da nake sakarya in bar ƴarta da ɗana,ai gwamma ya mutu ba aure".

"Kinyi tunani ko mai kyau na rigaki a zuci kin rigani a baki,Allah ya huta gajiyar mu".

"Wani gajiya,zanjira maciyi amanan nan ne ya dawo in mai ruwan rashin mutunci".

"Aiko karki raga masa ko kaɗan ,kimai mummunan rashin mutunci wanda zaiji dama wancan takwarkwasassan tsohuwar bata haife shiba".

Dariya sukai tare da tafa hannu suka sake shewa,kafin kowa tai hanyar ɓangaranta.

*********
Yanaji an buɗo ƙofar shi  ta ƙasan ido yake hangenta tare da ƙara lumshe idanuwan sa kamar mai bacci.

Murmushi tayi da yake ƙaramata tsantsan kyau ta nufi inda canter table ɗin tsakiyan falon ta aje ta jawo cater table ɗin kusa da inda yake.

Zama tayi ta gefen ƙafafun shi ta zuba masa manyan idon ta.

Shima ta ƙasan ido yake kallon ta yana tasbihi ga ubangiji da ya azurta shi da samun masoyiya kamar Jawahir.

Kai hannun ta tayi a hankali ta shafo gefen sajenta sa cikin kwantacciyar murya tace,"kayi haƙuri Hubby nasan kana jina ba bacci kakeyi ba,dan Allah ka tashi kaci abinci kaji".

Cikin shagwaɓaɓɓiyar murya take maganan kamar zata fashe da kuka.

Dariya ta bashi ya ƙyalƙyale da dariyan da baisan sanda ta ƙwace masa ba.

Dariya itama ta saka  yanda taga yana dariya ba ƙaramin abu ke sa shi dariya irin haka ba yafiyin murmushi.

Sai da yayi mai isarsa kafin ya tsagaita da dariyan.

Hararan wasa ta galla mai irin na masoya .

Maraice fuska yayi kamar ɗan yaro lokaci ɗaya yace,"kindena sona ko Honey tunda zaki iya barin mijinki da yunwa kusan one hour ,wai mai kika tsaya yine?.

Ya ƙarashe maganan da sigar tambaya.

Karyar da kai tayi tace,"tuba nike my husband".

Tana maganan tana ɗan murɗa kunnan ta.

"Bazanyi haƙuri ba sai kin tauna abincin nan kin rinƙa bani a baki har in ƙoshi".

Zaro manyan idanuwan ta tayi kamar zasu faɗo ƙasa.

Wani rikitaccen kashe mata ido yayi yana murmushi ƙaɗan.

"Ko bazaki iya bane?,yai mata tambayan a taƙaice.

Murmushi tayi tace,"mi zai hana inhar hakan zai saka jin daɗi".

"Yauwa matana mai sani farin ciki".

Ƙasa tayi da kanta tana murmushi kafin ta ɗau plate ta fara zuba abincin.

******
"Ke Jahda wuce side ɗin Jahoor kiga wannan shegiya annamimiyar yarinyar ta fito ko ta tsaya masa karuwan ci".

"Wacece kuma haka?,wallahi Ammie kindawo kenan da shegen masifar ki".

Jahda dake kwance kan doguwar kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana chart.

"Ƙundun ubanki ,nice masifaffar?.

Tai maganan tana watsa mata daƙuwa da  hannu bibbiyu.

"Shin wai Ammie wa kike nufi?.

"Ƴar gidan Juwairiya mana".

Uhmmmm ta faɗa tana tashi tana  buga ƙafa a ƙasa  tace,"ohhhhhh shitttttt Ammie kincika rigima ,mai wannan mai fuskan aljanun zai mata,yanda yake da faɗin rai kamar fir'auna ,ƙila abu yasata".

"Ke sakarya ce haka kike gani,ni jeki duba min".

"Wallahi Ammie saide kije da kanki ko kikira Aunty Jadida,ohhhh nama manta sunfita da saurayinta,nibazan ma jeba kijamin ɗan banzan duka,gwamma ke uwarshi kike saide yai mazurai".

Cike da  rashin kunya take maganan.

Shikenan ya isa uwata don naga gaba-gaba duka zaki hauni dashi.

"Allah yamin tsari da dukan ki,kiji da abunda ke gaban ki kina kallon na wani,inma soyayya suke ai aure halak ne,nasan ko mata sun ƙare bazai yi soyayya da Jawahir ba yarinya sai tsawo kamar igiyan shanya".

"Naji uwata tashi kisa akawo min abinci inkin gama zagina duk a gajiye nake".

*******
Jahoor ko da Jawahir suna can suna cin soyayyar su cikin jin daɗi da kwanciyar hankali  Jawahir ke cida shi kamar zata maidashi ciki.

*********
Ƙarfe bakwai da ƴan mintoci jerin gwanon motoci suka fara shigowa cikin haraban gidan marigayi Alhaji Ja'afar ɗan ƙasa.

Guɗa kawai ake sakewa,motoci ko ta ina ba masaka tsinke.

Hajiya Mama da murnan ta ta sake wani danƙareren guɗa da taji shigowar amaryan ɗanta.

Yayinda Jasmin jiki na ɓari ta fito,haka Hajiya Juwairiya ita da Jawahir.

Hajiya Mama ma kasa zama tayi ashigo da amaryan ɓangaranta ta miƙe ta fito.

Kusan a tare suka fito da su Jesica da Juliet,yaran gida kafffff da ƴan aiki sun fito.

Hajiya Jumaina ko tana ta window tana leƙe don sai taga fitowar Hajiya Jamila zata fito.

Sanda Hajiya Jamila taji guɗa take cikin ta ya murɗa ƙululululuuuuu da gudu ta miƙe ta faɗa ban ɗaki,saida ta kasayar kafin tafito jikinta har rawa yake ta nufi ɓangaran ƴan aiki  ta ɗauko ƙatoton taɓarya tayo haraban gidan.

Dai-dai lokacin da Hajiya Mama ta buɗe motor ta kamo hannun amarya dake dunƙule  cikin hijjab tana kuka   tana kwance jikin gwaggonta saide sukaji saukan abu.

*MRSBASAKKWCEPINKY*

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now