Binta kawai sukeyi da kallo  Jadidah da take da kimanin  shekara takwas tace,"Abie wacece wannan munyi sabuwar y'ar aikine Abie?.

Kallon'ta yayi tare da watsa Mata mugun kallo kafin yace,"karki dameni d surutu".

Yayinda Jawahir da Jahdah Wanda kansu guda suka kafe Jenifer da ido.

"Kama hannun su Abie yayi yace mushiga ciki ko".

Yana magana Yana kallon su.

Gyada kansu sukai amma idon su day hankalin su na wajan Jenifer.

Gaba yai suka bishi a baya inda Jadida ke bin Jenifer da harara ta kasan ido harsuka shiga babban falon su  yace ma Jenifer ta zauna.


Dai-dai lokacin Hajiya Jamilah ta fito anci kwalliya an caskare kyau ga saurin Nan na gado ture kaga tsiya tana washe hakora tace,"sannu da zuwa Alhaji ", sai Idonta karaf a kan Jennifer.

Baki ta bude gaban'ta na tsanan ta fadi don tunda tai tozali da yarinyar nan gaban'ta ya Fadi,butar uba ta fada a zuciyar ta  kafin ta kuma cewa Alhaji wannan mai kayan arnan fa,bade sabuwar Y'ar aiki mukayi ba?,Ina ka samota?.


Kallon'ta yayi ya girgiza kai ya fada bedroom dinsa.

Wani kallo ta watsa ma  Jenifer kafin taja dogon tsa'ki mtsww ta juya tabi bayan mijinta.

Jenifer ko zama tayi tai tsuru-tsuru yayinda Jahadah da jawahir suka zuba Mata na mujiya sai wani kallon'ta sukeyi kamar sun saku t v yayinda  jadida  ta wuce  game room dinsu taje taci gaba da buga game.

Hajiya kaka ce ta sauko daga sama Jenifer tana ganinta ta zube 'kasa tana gaidata tace "Good evening marh" murmushi hajiya kaka tasakar Mata ta daga Mata han'nu alamar sannunta itama sunkuyar da kan'ta 'kasa Jennifer tayi sauke glass din ido hajiya kaka tayi sannan tace mata "what is your name" ?

"My name is Jennifer Daniel"

Wow nice name "which state are you from"?

"Am From Adamawa state am living in DEMSA local government"

"Okay" inji cewar hajiya kaka a takaice cewa Jennifer tayi "follow me"

"Okay marh" inji cewar Jennifer da mamakin hajiya mama yakamata yanda taga tana turanci bama gargada aciki balai kuskure biyar bayan hajiya kaka Jennifer tayi suka haura sama wani d'aki taga hajiya kaka ta nuna Mata tace tashiga aciki akwai komai acikinsa ta nuna Mata toilet da komai godiya har 'kasa Jennifer ta duka tanayiwa hajiya kaka godiya sosai hajiya kaka taji dadin yanda taga Jennifer na Bata girma tayi soboda hajiya kaka akwai son girma murmushi tayi Mata tace "kada ki damu anzama daya kishiga toilet Yanzu kiyi wanka kishirya sai akawo maki abinchi". Tana Gama fadar hakan Bata jira meh Jennifer zatace ba ta juya tayi ficewar ta.

Biyar d'akin da kallo Jennifer tayi lungu da sako maida dubanta tayi ga makeken gadon d'akin Masha Allah ba acewa komai murmushi tayi tayi tako biyu ta Isa wajen gadon ajiye jakar hannun'ta tayi ta zauna akan ga'do tana Kara 'karewa dakin kallo.

Turo kofar akayi tayi saurin saisaita nutsuwarta masu aikin gidanne suka shigo dauke da kuloli kala_kala suna ajewa agabanta gaidata sukayi a tunaninsu batajin hausa sai sukaji tace "nagode sosai"

Mamaki ne yakamasu dukansu murmushi sukayi Mata suka juya sukaja kofar dakin suka tafi saukowa tayi ta Fara bude abinchi da aka kawo Mata kala Kala rufewa tayi Takoma inda take ta zauna


********
"Alhaji kamin bayani wancan yarinya wacece,wallahi in yar aiki ce baniso ka kaima Hajiya Mama".

Atsai tsaye take maganan ba taushi balle tausasawa take wa miji magana.

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now