Sakin ajiyar zuciya yayi bayan yagama nazarin garin .

Alhaji Jabeer ne yace "kai masha Allah yanayin garinnan ya matu'kar burgeni wallahi mukulle motar mushiga ciki mutambayi Wanda take gyaran mota sai a gyara mana"

Alhaji ne yace "kwarai kuwa nima yanayin garin yamin sosai saidai daga dukkan alamu musulman cikinsu basuda yawa"

Ganin suna 'bata lokaci sosai yasa suka fara takawa haraukafara shigowa cikin mutane bayara ba manya wajen kallonsu saboda kayan jikinsu ma kawai inka kalla kasan kud'i sun zauna musu.

Wani kirista sukagani da alama shima wajen bautar zaije tsaida shi sukayi
Alhaji yace "d'an uwa muna tambaya ne munzo wucewa motarmu ta lalace shine muke tambayar inda zamu samu me gyara kuma wanne gari ne nan?.

Washe wawakeken bakinsa yayi yace " nan sunansa DEMSA kuma duk masu gyaran basanan saidai ku'karasa gaba saiku tambaya akwai wani tsoho chan zai iyasa yaransa su duba muku".

Godiya sukayimai san'nan suka bashi kudi suka wuce.

Saida suka shiga sosai san'nan sukaga wani  dattijo ri'ke da fartanya saidai kana ganinsa kaga Wanda ba musulmiba kayanshi sunyi du'kun d'ukun da alama daga gona yake saidai mayunwacine Dan da'kyar yake tafiya.

Kamar yadda sukayiwa wancen shima haka sukayimai saidai shi sund'an sunkuya kafin sugaidashi .

Cikin girmama sukace " Baba Dan Allah inazamusamu me gyara doguwar tafiyace agabanmu motarmu ta lalace".

Murmushi yayi sannan yafara tafiya yace "kubiyoni".

Binshi suka farayi har suka isa wani gida da aka gewayeshi da zana sai bukkoki dayawa da alama gidan gandu ne.

Wani bukka yashiga dasu Wanda aka shinfid'a tabarmar kaba akai
Cikeda gajiya suka zauna suna sakin ajiyar zuciya
Zama shima yayi a gefensu yace " a Ina kuka ajiye motar zansa yarona yad'auko ingyara muku bazan iya zuwa bakin kwalta ba".

Gayamasa inda motar take sukayi san'nan yatashi yafita Saida yad'an dad'e kafin yadawo nan suka fara d'an fira harma yake cemusu mutanen gidan suntafi church shiyasa sukaji gidan shiru.

Alamu tafiya sukaji wata yarinya ce tashigo budurwace kyakykywa da ita kai bakace ba musulma bace yarinyar tanada kyau sosai ga diri .

Tunda tashigo idanuwansa na kanta harta aje ruwan da takawo tagaidasu Alhaji Jabeer sam baimaji gaisuwarba hankalinsa na kanta Saida Alhaji Ibrahim ya  zungureshi san'nan ya d'auke idanunsa akanta cikeda kunya .

Gaishe su tayi a ladafce kafin ta juya ta bar wajan ta nufi cikin gida'n su.


Sanye take da riga da zani na atamfa Mai kalan pink da ratsin  blue  kanta daure da dankwali ko gashin ta ba a hangowa shigace shigar mutunci a jikinta,fara ce sol kalan fatan ta kalan irin na larabawan Morocco ne,tana da matsananci tsayi,bata kiba amma tana da manyan mazaune da manyan hips,fuskarta doguwa ne mai dauke da dogon hanci da dan karamin baki,tana da manyan ido da zara-zara gashin ido kamar tai k'ari,gashin giranta a circike.

Kallo daya zakai mata zakaga tana da yanayin musulmai,daga fuskanta har shiganta

Dariya dattijon yayi yace "yarinyatace sunanta Jennifer ita kad'aice anan batayi aureba a yammatan garin nan badan itaba baza kusameniba saboda bazan iya tafiya nabarta ba ita kad'ai,dagani sai ita sai mahaifiyarta a nan".

Cikeda mamaki Alhaji Jabeer yace "to meyasa ita bazatajeba?.

Sunkuyar da kanshi yayi kafin yad'ago yace " saboda Fasto ya haramta mata zuwa ko ina a wannan 'kauyen  saidai idan  taje Noma nan ma'kotanmu itakuma bataso shiyasa ta hakura".

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now