"Wane wainar ake toyawa bani?.
Hajiya Jumainah da yanzun shigowan ta side din Hajiya Juwairah da jin sunan ta yafi ganinta,siri-riya ce gajera mai fici-ficin ido ,a bushetake ba atab'a cewa gidan kudi take.

"Kide bari takaici  wannan yaron muke  wai ahalul kita binnan yake shigemawa".  

Hajiya Jamila ke wannan maganar.

"Kide bari abin takaici yawane dashi".

Fadan Hajiya Juwairah.

Nan suka zauna aka buga daba,a zage wannan a b'ace wannan,ba Wanda ya tashi yin sallah.

*******
Ana kiran sallah mangari suna danno  motor su cikin haraban gidan ,dai-dai lokacin yara gidan manya da kananu suna alwala don shiga masallacin dake jikin gidan.

Fitowa sukai bayan sunyi parking Jessica  ɗauke da bible dinsu yayinda Juliet rike da key din motor da wayoyin su.

Yaran gidan binsu da kallo sukayi ,Yayyene  su suka gaisar cike da ladabi,wasu sun ansa musu wasu ,wasu ko-ko kallo basu ishe su ba,wucewar su sukai ciki,ɓan garan yara ,duk gasunan a zazzaune wasu na danna waya wasu ko na kallo.

"A'a Auntie's sannu da zuwa".

Jawahir  kanwar Jaheer ke magana cike da murnan ta don tana son su Jessica,sauran ko aike hara-ra suke wurga musu ba yaran ba ba manyan ba kamar sunga kashi.

Murmushi sukai suka amsa kafin suka wuce cikin bedroom dinsu  ,aje  bible dinsu Jessica tayi tafara ƙoƙarin cire kayan ta.

"Kai  dan uwarku,don baku da tarbiya zaku wuce kuna ganin mu ba zaku iya gaida mu ba,tou mu kuke jira mu gaida ku".

Jahdah ce riƙe da ƙugu tana tsaye tana ta jijjiga kamar bishiyar rimi take maganan sai jujjuya ido take.

Juliet da take jikin dressing mirrow tana kwance  gashin ta da taɗaure ta ɗago a kaikaice ta kalle  ta tace,"sorry My Aunt".

Ke dakata niba My ɗinki bane,miye haɗina daku kuna ƴaƴan arna,wa ƴanda basusan komi ba sai zuwa bautan gunki,karki kuma halaƙanta kanku damu ,mu tsarkakkun ƴaƴane,ba kafirai ba".

Ahasale take maganan kamar zata rufe su da duka.

Duk shiru  sukai ,kowa da abinda yake saƙawa.

Tsaki taja tsewwww tare da jan wani ƙwafa ta wuce  tafita fuuuuuuuuu ta buga gambu.

*********
Zazzaune suke akan daining a ɗakin da aka tanada don cin abinci kowa da iyalan sa  falon yake zuwa a yin dinner.

Wurga  ido yake  cikin yaran don sam bai hango ko ɗayan su ba,kallon inda  Jawahir ke zaune yayi ,yace ,"Sister jeki  kiramin ƴan uwanki".

''Suwa zata kira", cewar Abbie da shigowan shikenan dining room ɗin.

"Abbie Sisters Jessica and Julliet".

"Ki ɗiba  kikai musu ,addu'a suke,lokacin adduan sune ai".

Ammie su Jaheer ko sai hara-re-hara-re take.

Ke zauna ba inda zaki cewar Ammie su da ta sa hannu tatturo ɗankwali gaban goshi

Kallonta kawai Abbu yayi ya girgiza kai  yaja kujera ya zauna,don sam bai son ya tanka ma Juwairah.

Jaheer da Jawahir sai kallon juna suke duk sunyi tsuru-tsuru.

Daɗi ko kamar ya kashe Jahda don ta tsani  suna zaune yarannan na kusa,jitake kamar ta kamo su ta shaƙe su.

*ASALIN LABARI*
*SUWAYE WA ƳANNAN JESSICA DA JULLIET A FAMILY ALHAJI JAAFAR ƊANƘASA.?????*

*MIYASA JAHEER BAISON JAHDA?????*


*INDIA*

Cikin asibitin *New Delhi international hospital*   Alhaji Jabeer ne da matarsa Hajiya Jamila  zaune agaban Babban likitan Dr Prakash Rao  babban likitan mata ne Wanda idan mutum yaje wajensa yake ganin tamkar ciwansa yazo 'karshe 

Kallon su yayi cikin kwantar murya yace
"Alhaji kayi hakuri jinkirin haihuwarku  ba  wata lalurarce ajikinku ba nasan duk asibitocin dakukaje hakan suke fad'a muku kuyi hakuri akowanne lokaci zaku iya samun haihuwa tunda kunada wasu yaran"

Jinjina kai Alhajin yayi yace "shikenan Dr mungode sosai "

Mi'ka musu sauran takardun gwaje-gwajen yayi  nan suka sallameshi suka tafi kana ganin fuskokinsu kasan ba haka suka soba har gwanda ma Alhajin akan Hajiya Jamila  tafishi damuwa akan lamarin shi Sam ma baiwani damu akan hakan ba   saboda sunada yara har biyu shibaiga abin damuwaba

Kai tsaye hotel d'in dasuka sauka suka nufa ana saukesu ko tsaya shi batayiba tanufi cikin akan kujera ta cillar da Jakarta da mayafi tafad'a kan gado wasu zafafa hawayen takaichi yana zubo mata

"Bazaiyuba!

Take ta maimata hakan acikin zuciyarta

Yadad'e akanta yana kallonta yana karantar halinda take ciki ahankali yahau saman gadon tareda rungumota ahankali yake shafa bayanta alamar rarrashi

" kiyi hakuri haihuwa lokacine kirungumi yaranki kibasu  kulawa da tarbiya ta yadda kowa zaiyi alfahari dasu, saikiga Allah yabaki alokacin da bakiyi xato ba"

Sake rungumeshi  tayi ita Sam  ba wannan ne tunanintaba yanzu idan ya mutu duk dukiyarsa ya za'ayi da ita  yaranta biu ne kawai  tafiso ace tacika gidan da yara yadda ko nan gaba bazaisamu damar auro wata ba bare tahaifawa yaranta kishiyoyi

Cikin salo na nagartattun maza ya shagaltar da ita harta nunamai babu komai aranta  ahakan suka raya darensu cikeda farinciki

Washegari tun safe sukafara had'a kayansu Dan jirgin shad'ayan safe zasu hau 

Gidan gaba d'aya yarikice da 'kamshi na girki Dana turare kowa kagani cike yake da farinciki na dawowar Uban gidansu yaran gidan kowa kagani cikin farin ciki yake saboda dawowar iyayen nasu.

MORE COMMENTS
MORE TYPING
*LEEMART AND BASAKKWACE*
_0201202i

Sake rungumeshi  tayi ita Sam  ba wannan ne tunanintaba yanzu idan ya mutu duk dukiyarsa ya za'ayi da ita  yaranta biu ne kawai  tafiso ace tacika gidan da yara yadda ko nan gaba bazaisamu damar auro wata ba bare tahaifawa yaranta kishiyoyi

Cikin salo na nagartattun maza ya shagaltar da ita harta nunamai babu komai aranta  ahakan suka raya darensu cikeda farinciki

Washegari tun safe sukafara had'a kayansu Dan jirgin shad'ayan safe zasu hau 

Gidan gaba d'aya yarikice da 'kamshi na girki Dana turare kowa kagani cike yake da farinciki na dawowar Uban gidansu yaran gidan kowa kagani cikin farin ciki yake saboda dawowar iyayen nasu.

MORE COMMENTS
MORE TYPING
*LEEMART AND BASAKKWACE*
_02012021_

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now