chapter 1

112 10 2
                                    

_typing🖌️_


     *🏝️Z°•W°•F🏝️*


    *🏘️A GIDANMU SUKE🏘️*

MALLAKAN:- *LEEMART PINKY AND MRS BASAKKWACE*


SADUKAR WA:- *WANNAN LABARIN DAGA FARKON SHI HAR KARSHEN SHI SADAUKAR WANE GA IYAYEN MU, PLEASE IN KI/KA KARANTA KAI MUSU ADDU'A,YA ALLAH KA KARA MUSU TSAWON RAI MAI ANFANI WAND ZAMU FARANTA MUSU,SUMA SU FARANTA MANA*

ALHAMDULILAH! ALHAMDULILAH!! ALHAMDULILAH!!!
_ALLAH MUN GODE MAKA DA KABAMU ARAN KWANA DA ARON RAYUWA,KA BAMU LAFIYA,DA ZAMAN LAFIYA ,YA ALLAH KABAMU IKON ISAR DA SAKON DA MUKE TAFE DASHI CIKE DA ANGARAR MU,AMEEN YA ALLAH_

*PAGE 1&2*


*DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJIN KAI*

"Kai da komowa takeyi a tsakiyan tangamemen falonnsu,da ya sha kayan alatu,faɗan  tsaruwan shi  ma ɓata lokacine,kai da kawowa takeyi,tana yi tana cizon yatsa,kallon wani ɓangare tayi tace," *JADIDA*,ki kalleni da kyau daga sama har ƙasana mai na rasa da  *JAHEER*  bai sona,dan Allah wani haline nake dashi wanda bai da kyau da har Jaheer ke ƙyamana,ya tsanani?,why Jaheer don't love me why?.

Cikin sanyi murya,kamar zata fashe da kuka take maganan.

*KALLONA NAKAI GA WANNAN YARINYAR MAI MAGANA,GASKIYA MASHAALLAH,SAI DAI ACE MAƘI GANI YA KAUDA IDON SHI*

Budurwace ƴar kimanin shekara ashirin da biyu da uku,doguwa mai matsaikaicin tsayi,farace tasss son kowa ƙin wanda ya rasa,tana da dogon fuska,mai ɗauke da manyan idanuwa,tana  dogon hanci har baka,ga bakinta ɗan ƙuttt,tana da yalwan gashin gira dana ido,tana da manyan boos daga ƙasa kuma tana da ɗan ƙaramin ƙugu,yayin da daga ƙasan ta tawani buɗe ,tana sanye da riga da siket ya fidda shape ɗinta dai-dai jikinta,kamar a jikin ta aka ɗinka kayan,ga gashin kanta da ya sauka har kafaɗa.

Miƙewa ɗayan tayi ta tako,ta dafa ƙafaɗar ta kallo ɗaya zakai musu kaga tsan-tsan kamarsu da tayi yawa,cikin tausas-san murya tace," *JAHDA*,baki rasa komi ba,kowane ɗan adam tara yake bai cika goma ba,kusan ke ince kin cika cicif,kin haɗa komi,Wanda ko y'a mace  ta ganki sai tace masha Allah balle na miji,kinsan shi so wani abune da bai sauka inda ya dace Jaheer ba sonki ne kawai,abayayi ba badon kina aikata wani mugun haliba ko mugun ɗabi'a ba,ƙila bakya cikin matan da ya dace ya sone Jahdah".


"Jadidah ina mugun son Jaheer,ina kishin shi,ina tsan-tsan son shi da konima ban san ya akai na fara son shiba,ki duba duk faɗin gidannan da ƴammatan gidanan Yayah Jaheer  wa ƴannan arnan ƴaƴan yahudawa masu warin ƙashi in kinga dariyan shi tou su ya gani,bai min dariya komi namai sai ya gwasale ni,mi zanyi ya fara sona,mai zanyi ya kulani,ya subuhanallah,ya rab sa'iduni".


Cikin shashsheƙar kuka take maganan.

**********
"Juliet ki sauri ki shirya mu shiga coci,kar lokaci ya ƙure mana".

Wata doguwar yarinya fara kyakyawa son kowa ƙin wanda yarasa,kyawun ta kawai da ka kalla sai kayi tasbihi ga ubangijinka.

"Ok Jesica,ina duba dogon wondo nane orange ban ganshi ba".

"Kisa kowani kaya kawai kizo muje".

Cikin mintuna  ƙanƙani ta gama shiryawa ta ɗauko musu bible ɗin su ,suka jera,suka fito.

Ɗayan sanye take da helf gown dai-dai guywa,sanyi da dogon wandonta aciki Wanda ya matse Mata jikinta sosai tayi packing ɗin dogon gashin ta  dake reto har gadon baya.

Saɓanin ɗaya da tasa t-shirt fara  da  wando ja,iri ɗaya gyaran gashin su  da sukayi.

Tsan-tsan kamar su ya bayyana,ɗaya tafi ɗayane ɗan tsawo kaɗai ya ban-banta su.

 A GIDANMU SUKE Labari ne akan Soyayyar arniya da Kuma musulmi Where stories live. Discover now