Chapter 49

3.2K 344 127
                                    

"Motocin daukar amaryane fiye da ashirin jere ana jiran fitowar amarya da kawayenta da yan'uwanta,inda deen ke controlling mutanen gurin don ya shiga busy matuka tare da kewar amininsa ya Allah meyasa ban bari seda Sadiq ya samu sauki akayi auren nan ba shine abinda deen ke maimaitawa a zuciyarsa

"Agogon hannunsa ya kalla it was already 7pm,mamaki yaci gaba dayi menene dalilin fitar mom unguwa tun da safe ace har yanzu ta kasa dawowa kuma wayarta a kashe,ya salam i think something wrong is happening to mom,,,Alhaji modibbo ne ya karaso inda deen yake tsaye da sauri yana tambayarsa ko yasan inda mom ta fita tun safe an kasa samun wayarta sannan duk wanda ya tambaya se yace besan inda takeba hatta gidajen yan'uwa wanda yake tunanin zataje duk bai sametaba

"Aunty A'i ce ta karaso gurin da Alhaji modibbo ke tsaye tare da deen da gudu cikin kuka tace na shiga 3 na lalace ni a'i wallahi an sace nabeelah,babu inda ban duba ba bata cikin gidan nan,sannan wayarta yana ta ringing ba'a dagawa,a tsorace gaba dayansu suka juyo suka kalleta cikin tsoro musamman deen da yayi mutuwar tsaye zuciyarsa na bugawa da sauri,meyake faruwane haka?mom ta bata,nabeelah ta bata sannan an sace masa wayarsa kuma duk a lokaci daya,wayar dad ya karba ya kira police yayi musu reporting halin da ake ciki na batan nabeelah da mom

"Sosai aunty a'i ke kuka a compound din gidan kamar wata karamar yarinya ana lallabata,me gadi ne ya karaso fuskarsa dauke da matsananciyar damuwa yace wai wacce nabeelar ake nema kuma?

"A zafafe deen ya kalleshi yace what a fucking darkest hell are you saying?har nabeelah guda nawa ne a gidan?sunkuyar da kansa yayi cikin ladabi yace ranka ya dade ai indai wannan yarinyar fara siririya marar jiki wacce naji ana kiranta da nabeelah to lallai dazun nan suka fita da wannan amaryar taka amma banga dawowarsu tareba se naga kun dawo tare da amaryar taka ita kadai kawai

"Kana nufin nabeelah sun fita tare da zulaikha ne?deen ya fada a takaice

"Saurin daga kansa yai yace kwarai kuwa

"Karya kake tsinanne,matsiyaci dan talakawa wanda yazo a talauci ze kare a talauci shege talakan megadi,idan kana yin sharri kana xama lafiya toh baka isa kayiwa zulaikha ba,banda sharri da makirci yaushe zulaikha ta fita da wata nabeelah sai kace wata sa'arta?hajiya saratu ta karasa magana tana haki kamar wacce take a filin yaqi

"Alhaji modibbo ne ya watsa mata wani kallo mai dauke da tambayoyi da yawa sannan ya sunkuyar da kansa kasa yana dana sanin zamanta sirikarsa tun ba'aje ko inaba ta fara nuna halinta na dabbobi inaga kuma yarinyar tata,kallon daya daga cikin cousins din zulaikha da sukazo bikin yayi yace kira min zulaikha din

"Sake kallonsa hajiya saratu tayi tace haba Alhaji wai ya ma za'ayi ka dinga yarda da zancen kananen mutane kuma talakawa,shifa wannan tsohon talakan neman na abinci yakeyi baka tunanin yayi hakane don kawai ya dorawa zulaikha lefin daba nata ba don kawai ya samu kudin siyan masara da dawa a kauye akaiwa tsofaffi,,,,,a fusace megadi ya kalli hajiya saratu yace ke dakikiya marar ilimi kalleni da kyau koda bani da wadatar arziki amma inada wadatar imani a zuciyata ke kika damu da tarin dukiya shiyasa har kike ganin kamar zaki iya fitar da kudi ki siyi duniyar gaba daya,da talaka da me kudi duk dayane a gurin ubangiji sannan inaso kisan  cewa yawancin attajirai talakawane a baya sannan yawancin talakawan yanzu toh attajiran masu kudine a baya,,,ban damu da kudiba amma na damu da mutuncina da imanina don haka baki isa ki zauna kina cimin mutunci a bainar jama'aba don haka ki kama kanki ba zamanki nakeyi a gidan nanba

"Alhaji kanajin abinda yake cemin ko kanajin abinda me gadin gidanka yake gayaminko toh wallahi zanyi tijara a gurinnan zanyi cin mutunci a gidannan,da sauri alhaji modibbo ya rike baki cikin mamaki yace ayi hakuri hajiya,megadi ne ya kalleshi yace alhaji ka bar bata hakuri inta fasa yin tijarar uwarda ta haifeta shegiyace ko batasan cewa na fita tijaraba harni za'a nunawa tijara gardin kauye mamaki lol

"Karasowar zulaikha ne ya dakatar da sa'insar da ake tsakanin megadi da hajiya saratu,gabanta ke tsananin faduwa wanda har ta kasa boyewa ta tsuguna gaban alhaji modibbo tace gani,kallonta yai yace zulaikha ance dazu kun fita da nabeelah kuma ba'aga dawowarku ba tare sai ke kadai

"Mikewa tai tsaye jikinta na rawa tace injiwa?waye yace na fita da nabeelah?ni ban fita da wata nabeelah ba,ta karasa maganar muryarta na rawa

"Ahaf nina fada ai,wai ma banda toshewar basira taya xa'ace zulaikha ta fita da wata yarinya se kace wata sa'arta,yarinyar da ba ajintaba,figaggiyar yarinya tana tafiya kamar iska zata hureta meya hadata da zulaikha wacce ko a shekaru ta fita,hajiya saratu ta karasa maganar tana hararar megadi

"Motar yan sanda ce ta karaso gidan tai parking mutum 2 daga cikin yan sandan suka fito suka tsaya gaban Alhaji modibbo cikin ladabi sukace ranka ya dade

"Cikin rikicewa Alhaji modibbo yace ya anyi nasarar gano inda suke?

"No sir,ita dai yarinyar anyi nasara don halin yanzu munyi tracing number wayarta kuma har yanzu wayar a kunne take mun gano location din da wayar take a badawa layout ne no 148,itama kuma hajiyar muna da tabbacin inda aka saceta bazeyi nesa da nan ba,,,da sauri deen ya dago ya kalli zulaikha da gumi ya fara wanke mata jiki.....if i can remember badawa layout dazu achan naje na dauki zulaikha shine abinda deen ke fada a zuciyarsa yanzu maganar me gadi tana da nasaba kenan

"Alhaji modibbo ne ya kalli jerin mutanen dake tsaye yace kowa ya koma ciki sannan kowa ya kwantar da hankalinsa insha Allah komai zezo da sauki,sannan zancen kai amarya yana nan sedai dalilin halin da muka shiga za'a wakilta mata 3 ne kawai su kai zulaikha gidan angonta deen

"Daki suka shiga suka kulle kansu gabansu na mummunan faduwa zulaikha ta kalli hajiya saratu tace momy na shiga 3,kinga me gadi ze buden aiki ko?na shiga 3 mom yanzu idan akayi tracing gidan sojeeyy aka ga gawar nabeelah ya zanyi tunda dazu deen achan ya daukoni,,,,wallahi momy na shiga 3....murmushi hajiya saratu tayi tace haba zulaikha ko kin manta wacece hajiya saratu nice nan mace me kamar maza yar gidan shedan kuma abokiyar dujjal,babu abinda ze faru shima me gadin nayi miki alkawarin bazeyi kwana 2 ba zebar duniya....subhanallah

"Waya ta dauka ta fara laluben number sojeeyy don duk da maganar da hajiya saratu ta fada mata sam hankalinta be kwantaba,bugu daya tayi ya daga wayar cikin muryarsa ta bosawa yace hajjaju makkatu ki bamu kudi mu baki dadi hahaha ya karasa maganar yana dariya,ajiyar zuciya tai tace sojeeyy asirina yana gab da tonuwa don har yan sanda sun gano inda nabeelah take ka gaggauta fita da gawarta kafin suzo su tarar da kai ka jawo min masifa

"Sake bushewa yayi da dariya yace haba aimu bama tsoron kwalawa wallahi ba wani shege,aini yanzu har na daureta a buhu ma kawai zan dauko motane in sata inje babban teku in jefar da ita (mamaki my heart a buhu lol)

"Yawwa sojeeyy please ka taimaka ina cikin tashin hankali don Allah ka taimaka kafin asirina ya tonu,angama hajiya ya karasa maganar yana busa cigarette sannan ya ajiye wayar,saurin daga hannunsa yayi surrender  ganin yan sanda da bindiga sunyi arresting dinsa,suka fara dukansa kamar ransu ze fita,yallabai tana motsi kamarfa bata mutuba muyi sauri a kira ambulance a kaita asibiti

"Haba inspector kana kallon yanda take kwance jini kacha-kacha a jikin gawa kace wai tana da rai,wallahi naga tayi motsi yallabai daya daga cikin yan sanda ya fada a takaice......

"Wayar hannunta ce ta zame ta fadi kasa ganin deen tsaye a bakin kofa yana sauraron duk abinda take cewa da sojeeyy

DeenWhere stories live. Discover now