Chapter 37

3.2K 277 19
                                    

"A tare suka shiga dakin da deen yake kwance yana bacci,,,kallo daya sadiq yayiwa deen yai saurin dauke idonsa ganin yanda deen ya rame,yai baqi,ya lalace kamar ba kyakkyawan handsome guy din daya saniba "Tiger I swear kaine kake sa kaya suyi kyau ba wai kaya bane sukesa kayi kyau ba"tunowa yayi da maganar da yake yawan gayawa deen idan ya fito zai tafi office,,,,amma yau ga deen kwance a gadon asibiti yasa kayan amma ko kyau beyiba....hawayene ya gangaro daga idon sadiq yasa handkerchief ya goge yaci gaba da kallon deen da yake kwance kansa da kafafuwansa duk bandage babu kyan gani

"Komai na nabeelah ya tsaya cak,tunanin deen shine kadai abinda take yi a kullum,,,ji tayi tanason jin menene labarin da sadiq yakeson bata akan irin rayuwar da deen yayi a baya....wayarta ta janyo tai dialling number sadiq ta kirashi tace tanaso gobe yazo ya sameta tanason jin labarin

"A guest room nabeelah da sadiq suka zauna sannan ya kalleta yace beelah deen mutumin kirkine fiye da yanda kike tunani,,yana da nutsuwa da kamun kai da tausayi da rikon addini,,,,asalina dan maidugurine tun bayan fadace fadacen da akai na rasa duk wasu dangina na shiga yawon duniya,,,,tausayi yasa deen ya janyoni jikinsa ya mayar dani kamar dan'uwansa komai tare mukeyi da deen....ganin yanda deen yake kyakkyawan namiji kuma hamshakin me kudi yasa nake mamakin meyasa baya neman mata?meyasa baya shaye-shaye don ina ganin shine babbar wayewa a wannan zamanin....a hankali na fara sakawa deen wannan ra'ayin yarda dani  din da yayi yasa deen tunanin abu me kyau nake koya masa daga nan deen yaci gaba da aikata abubuwa marasa kyau wanda har sun wuce tunanina sai na fara tausayinsa na fara nuna masa cewar ba abu bane me kyau amma a lokacin deen yayi nisa bazai taba denawa ba

"Ya isa haka sadiq,ya isheni haka.....sannan ta mike ta karasa goge hawayen daya wanke mata fuska tace meyasa zaka cuceshi?meyasa ka koya mishi abinda kasan kai koda wasa baza ka iya aikatawaba?yanzu gashinan ai...ga irin rayuwar daka sashi nan ta janyo masa....sadiq ko kadan baka da imani

"I know ya fada shima yana goge hawayen daya gangaro mishi idonsa sannan yace abu daya zanyiwa deen wanda ze sashi farin ciki shine na auri batul bayan ta haihu kuma i promise zan aureta insha Allah

"Kiran wayar nafeesa ne yasa gaba dayansu suka  wuce asibitin da aka fada musu batul tana chan a tsorace,sosai take kuka tana neman yafiyar su....suma su mom da dad riketa sukayi sosai suna tausaya mata daga nan likitoci suka shiga da ita theatre room za'ayi mata Cs bazata iya haihuwa da kanta ba

"Bayan 2 hours likitoci suka fito suna goge gumi da baby a hannun daya daga cikinsu da alamar sunsha wahala.....da sauri mom ta karbi yaron cikin farin ciki tace Alhamdulillah ya Allah,,,shima dad karbar yaron yayi ya kalleshi kamarsu daya da sadiq sedai kuma suna yanayi da deen da yake batul tana kama da deen....fuskar mom a sake tace doctor zamu iya shiga gurin batul din?

"Sunkuyar da kansa yayi kasa yace se dai ayi hakuri batul ta rasu.... Allah ya karbi ranta,ta rigamu gidan gaskiya....innalillahi wa'inna ilaihir raj'un gaba dayansu suka fada a take sadiq ya fadi kasa sumamme

"Babban tashin hankali suka shiga ita kuwa nafeesa zubewa tai kasa kamar mahaukaciya tana ta surutai....da kyar aka matsar da deen daga jikin batul aka shiga don yi mata sutura a kaita gidanta na gaskiya

"Bayan kwana 7 da rasuwar batul aka sawa jaririn suna DEEN,,,,Sannan aka fitar da deen saudi arabia don ya samu yayi cikakkiyar ibada kuma ya samu nutsuwa,,,,saboda har yanzu deen baya iya tuna komai dad kawai yake ganewa sai sadiq din daya tafi yake yin jinyar deen

"Gaba daya rayuwar gidan modibbo ta zama abar tausayi babu wanda yake yin walwala,sosai aka sa malamai suke yiwa deen addu'oi

"Sai da sukayi 3 months tukunna suka dawo still dai deen baya iya tuna komai....zaune suke a parlour suna watching movie mom ta shigo hannunta rike da junior deen ta mikawa sadiq tace kaga yaron nan kullum kamanninsa sake juyewa na batul da deen sukeyi....a firgice deen ya kalli mom sannan ya dafe kansa yace batul,batul,batul kamar me kokarin tuno wani abu.....sake dafe kansa yayi sannan ya kwalla ihu yace innalillahi wa'inna ilaihir raj'un....mom,sadiq meyake faruwa dani?mom a ina nake nan?yaci gaba da kallon dakin yana bin sadiq da jaririn da yake hannunsa da kallo

Boring chappy I know 😭
Poor deen
Don't forget to vote

DeenWhere stories live. Discover now