Chapter 45

2.4K 228 29
                                    

"Sai daya iddar da sallar asuba tukunna ya kwanta,janyo wayarsa yayi yaga 3 missed calls din nabeelah damn stupidity!!!ya fada sannan yai tsaki ya jefar da wayar ya kwanta bacci me nauyi ya daukeshi,,,7am alarm din agogon dake bedside drawer dinshi ya tasheshi,bude idonsa yayi kadan ya shafa gashin kansa sannan ya dauki towel ya wuce bathroom yayi refreshing jikinsa,,,jikin closet ya tsaya ya dauki suit dinsa dake sakale a hanger sannan ya wuce jikin babban dressing mirror dake cike da perfumes da sauran skin care da mayukan gyaran kai,be jimaba ya fito palour ya tarar da mom da little junior suna breakfast,tsugunawa yayi ya gaisheta tukunna ya dauki junior yace ewwooo junior me is getting heavy mom yaron nan kiba yakeyi fah,sosai mom tai dariya ganin yana shirin fita beyi mata maganar zulaikha ba yasa ta kiran sunansa da sauri,,,juyowa yayi yace yes mom
"Ina ganin kafin ka dawo daga office fa za'a kai kudin aurenka gidansu zulaikha sannan munyi magana da dad dinka yace asa 1 week kawai bikin shima zeyi kokarin dawowa daga Morocco din kafin 5 days

"Murmushi yayi yace no problem mom,ayi duk abinda ya dace kawai,sannan ya kalli wrist watch din dake hannunsa yace shit i'm late

"Sai 10am ta bude idonta ta saukesu kan agogon dake manne jikin bangon dakin,a firgice ta mike ta shiga bathroom tai wanka ta shirya cikin doguwar riga sky blue,aunty lami ce ta shigo dakin tace nabeelah har kin tashi kenan?"Daga kanta tai tace au...

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

"Sai 10am ta bude idonta ta saukesu kan agogon dake manne jikin bangon dakin,a firgice ta mike ta shiga bathroom tai wanka ta shirya cikin doguwar riga sky blue,aunty lami ce ta shigo dakin tace nabeelah har kin tashi kenan?
"Daga kanta tai tace aunty ina kwana?

"Lafiya lau dama tashinki nazo yi kuma na tarar ma har kin tashi ina zakije haka?

"Am am dama zanje gidansu fatima ne ta karasa maganar cikin i'ina

"Haba nabeelah gidan kawa kuma da sassafe haka,ai sai iyayenta su zarge kima ace ba mutuniyar arziki bace,ki bari sai azhar ko la'asar sai kije

"Da sauri ta sake kallonta tace aunty dama inaso na fara zuwa office dinmu xan karbi wasu papers daga nan sena wuce chan

"Yauwa,yanzu naji zance toh yanxu dai kije kiyi breakfast tukunna sai ki tafi kinsan yau mutuniyar taki nayi miki

"Zaro ido beelah tai tace aunty badai har kinyi wainar shinkafa ba da safen nan kafin na tashi?

"Murmushi tai tace kwarai kuwa an gaya muku mu irinkune matan zamani marasa son aikin wahala

"Duk da ba wani yunwa beelah keji ba amma taci wainar shinkafar da miyar taushen da yasha biscuit bone (tantakwashi) da kunun farar shinkafar da yasha fresh milk

"Parking tai ta fito daga cikin motarta sannan ta zubawa 5th floor din da deen yake ido,murmushi tayi memories dinsu ke dawo mata,sosai take jin dadin kallon office din nashi tana cigaba da tuno tsahon rayuwar da sukayi spending da deen,,,,mr arrogant ta fada cikin dashashiyar muryarta sannan tayi murmushi ta danna elevator dinda zai kaita 5th floor

"A bakin office din ta tarar da P.A dinsa suka gaisa sannan ta tura kanta ta shiga office din zuciyarta na bugawa da sauri,zaune ta tarar dashi yana aiki a system dinsa kunnensa daya dauke da Bluetooth yana yin waya,,saurin dago kansa yayi yaci gaba da kallon beelah ganin bata da niyyar dauke idonta itama akansa ya sashi maida hankalinsa kan system dinsa,seda ya gama wayar tukunna ya cire Bluetooth din daga kunnensa ya kalleta a fusace yace how dare you!!!what the hell are you doing in my office?

"Shiru tayi tana kallonsa tana wasa da fingers dinta kamar karamar yarinya,sake kallonta yayi yace heeeeyyy deaf,am talking to you....mikewa yayi ya karaso inda take tsaye ya zagayo da kansa dai-dai saitin kunnenta wanda take shaqar hadaddan perfume din jikinsa yace mrs deaf are you looking for a job?

"Saurin girgiza kanta tayi alamar a'a

"Komawa yai kan kujera ya zauna sannan yace then get the hell out of my office,i don't want to listen anything....i said get outttttt

"Turo kofar da akayi ce ta dakatar dashi daga magana a tare suka kalli me shigowa,zulaikha ce sanye cikin straight gown red colour na material wanda ya matse mata jiki sosai shape dinta ya fito....kallo daya beelah tai wa zulaikha ta tabbatar da cewa lallai wannan itace yarinyar da fatima ke mata bayanin deen ze aura

"Tana ganin beelah ta daure fuska a fusace ta kalli deen tace who is she?

"Oh yeah she's my sister beelah ya fada yana murmushi

"Awwnnn so beautiful zulaikha ta fada a takaice

"Kallon mamaki beelah tayiwa deen,har yaushe ya hadu da zulaikha da zeyi mata karyar cewa ita kanwarshice don kawai kar ranta ya baci?yanzu deen yana son zulaikha kenan shima?tabota da zulaikha tai ya sata ajiyar zuciya da sauri ta kalleta

"Hannu zulaikha ta mikawa beelah tace nice to meet you sister beelah,itama tai saurin mika mata hannu tace thank you

"Ranta a bace take driving gaba daya haushin kanta takeyi meyasa take kasa fadawa deen abinda ya kawota ne?wayarta ce ta fara ringing ta daga ganin sunan aunty a'i

"Hey aunty ina wuni,ya nake jinki cikin hayaniya nabeelah ta tambaya a takaice

"Wlhy muna gidan Alhaji modibbo kinsan yau ansa ranar auren deen sati 1 aka saka,yanzu haka muna gidan anata shirye shiryen bikin hatta family din amaryar suma duk suna gidan alhaji modibbo don haka kema ya zama dole gobe ki taho idan an gama biki seki koma kada iyalan modibbo suyi tunanin akwai wani abu a zuciyarmu bayan hanasu aurenki da mukayi

"Innalillahi wa inna ilaihir raj'uun ta fada a zuciyarta,tai saurin yin parking ta tsaya ganin sitiyarin motar na shirin kwace mata,amma aunt,,,,,jin an kashe wayar ya sata jefar da wayar gefe tace ohh shitttttt aunty bazaki taba fuskantar mutum ba kedai kullum kamar mama sabil!!!

"Sai da jirin ya dena dibarta tukunna ta karasa gida,a palour ta tarar da aunty lami tana cin dambun gargajiya,tare suka zauna sukaci anan aunty lami take fada mata cewar aunty a'i ta kira waya tace gobe ta koma gidan alhaji modibbo da zama har se an gama bikin deen tukunna

"Karfe 11am nabeelah ta gama hada kayanta tayi sallama da aunty lami sannan ta kudurcewa ranta cewar cikin sati dayan da zatayi gidan modibbo ya zama dole ta dakatar da auren deen da zulaikha ta hanyar fada masa gaskiyar lamari,sedai ta yaya?anya deen da yan'uwansa zasu fahimceta koda kuwa ta fada musu cutar da take faruwa da zulaikha?so fucking noo bazasu taba yarda daniba ta fada tana girgiza kanta

"11:30am tai parking din motarta gidansu deen,fitowa tai ta tsaya tana nazari da tunani akan tsarin gidan,gaskiya an kashe kudi a cikin gidannan komai na gidan na daban ne,,,,,ferrari din deen ce tai parking kusa da motarta sannan suka fito da zulaikha hannunta dauke da ledoji fuskarsu dauke da murmushi da alama shopping sukaje,,,,kallo daya deen yayiwa beelah ya dauke idonsa itama zulaikha wannan karon kallon banza tayiwa beelah suka wuce

"Seda suka wuce tukunna ta karasa rufe motarta zata wuce tai tuntube da paper a kasa da alama deen ne ya jefar da takardar be kulaba,a hankali ta tsuguna ta dauki takardar ta bude,takardar test ne na H.I.V da genotype,da sauri ta kalli gurin result din sedai abin mamaki dukaninsu negative har zulaikha bata dauke da wata cuta,tabbas fatima ba karya take yimin ba sedai idan zulaikha ce ta hada baki da wani doctor din don a yaudari deen ta fada a zuciyarta

"Hango sadiq tai da little junior ya dawo daga sports field da sauri ta daga mishi hannu

TanTanTan fire on the mountain run,run,run,run
Ga deen,ga sadiq,ga beelah,ga zulaikha duk gida daya what are you thinking guys😂

DONT FORGET TO CHECK MY NEW STORY MU'AMALAT

DeenWhere stories live. Discover now