Chapter 36

2.3K 221 5
                                    


"Gudu sukeyi sosai kamar ransu zai fita,horn din ambulance ne yasa beelah saurin kaucewa,ta dade tana gudu taji wata kara a farfajiyar hospital din ta juyo da sauri,tuni har mutane sun zagaye motar da ta buge deen ana ta salati

"A tsorace nabeelah ta karaso gurin jikinta a sanyaye ta kalli deen da yake kwance kamar gawa jini yana zuba daga kafarsa,sosai tai ihu tace na shiga 3 na lalace aunty na kasheshi ko?na shiga 3 na lalace.....

"Accident and emergency aka shigar da deen cikin sauri likitoci suka rufu akansa don ceto rayuwarsa,,,,sai da nabeelah ta dade tukunna ta dawo hayyacinta,kamar gidan zaman makoki haka asibitin ya zama kowa ka kalleshi yayi tagumi yana jiran likitoci su fito su fadi halin da deen yake ciki

"Har 8pm amma shiru ba'a samu wani labari akan deen ba don har lokacin be farfado ba,duk da tsanar da beelah tayiwa deen wannan karon ya bata tausayi ganinshi da tayi kwance cikin jini,anya deen ze rayu kuwa?lallai duniya ta yiwa deen juyin waina ba zato ba tsammani tun kafin aje ko'ina

"Yanda taga dare haka taga rana sam ta kasa bacci sai juyi take yi akan gadon,tsaki tayi tace to waima meye zan damu akan mutumin da koma meye shine ya jawa kansa,watakila ma alhakinane biyoni din da yayi niyyar kasheni yai Allah yasa motar ta bugeshi....tunane tunane taci gaba dayi har akai kiran sallar asubha ta tashi tayi sallah tukunna ta samu bacci ya dauketa

"Data farka bata samu su dad da Aunty a'i a gida ba tasan suna chan gurin deen,tabe baki tayi tace tab gara ma da kuka tafi don wlhy bazan sake komawa asibitin nan ba ko alama

"Kwance take akan gado ta rame tayi baqi ta lalace sai katon cikin da yake jikinta,nafisa ce ta turo dakin ta shigo sanye cikin red jumpsuit ta kalli batul tace hey girl abinda kike a cikin gidan nan fa ya fara isata batul,ke kullum baki da aikin yi sai kwanciya dubi yanda kika yi baqi kika rame sai kace wacce bana baki abinci...yanzu idan akazo aka ganki ai sai a zata bana kula dake ne

"Murmushi batul tayi tace babe kinfi kowa sanin damuwar da nake ciki,ina cikin tashin hankali nafisa.....bacin haukan da yaya deen yakeyi yanzu haka ya sake samun wani accident din ya samu ciwuka sosai a jikinsa taya kike ganin hankalina ze kwanta?

"Ajiyar zuciya nafisa tayi tace duk da haka amma karki manta dai duk sanda mukaje asibiti sai ance jininki ya hau,ga cikin da yake jikinki,,,,ni wlhy batul na raina miki hankali da har kika zauna da ciki kike tunanin wai zaki haifi dan shege...ni nan da kike ganina yawan abortion din da nayi baze lissafuba kuma babu wanda ya sani a gidanmu gashinan kuma kina kallo saura 2 months biki na kowa kallon salihar mace yake yimin,kinga ke kuwa yanzu kin zubarwa kanki mutunci a idon duniya babu wanda ze kalleki da mutunci balle har yace ze aureki....nafisa na gama fadan haka tace malama kinga 6pm yayi zan wuce gida ga abinci nan na ajiye miki ki kula da kanki....see you tomorrow

"Murmushi batul tai tace see you tomorrow nafisa take care

Morocco Dakhla-Oued Ed-Dahab

"Zaune yake a beach yana shan mocktail cikin nishadi yake kallon phone din dake hannunsa yana duba feeds a instagram,a firgice yaci gaba da zooming picture din daya gani na deen,mocktail din dake hannunsa ne ya fadi yace innalillahi wa'inna ilaihir raj'un,,,,madness?how comes?number nabeelah yai saurin kira ya kara wayar a kunnensa

"Gobe zan koma Nigeria beelah,,,sadiq ya fada jikinsa a sanyaye

"Shit!!!kana haukane taya zaka dawo 9ja bacin kasan you are wanted

"Ajiyar zuciya sadiq yai yace beelah bazaki gane irin relationship din dake tsakanina da deen ba,,,i'm regretting akan abinda na aikatawa deen da batul a rayuwa,,,,sam-sam deen beyi deserving abinda nayi mishi ba....nasan dole akwai takaicina da bakin cikin abinda na aikatawa deen a sanadin madness dinsa,beelah bani da kowa a duniya sai deen,,,deen shine mutumin daya mayar dani mutum a duniya,deen shine sanadiyyar samuwar farin cikina.....duk wani abu da iyaye suke yiwa yaransu mahaifin deen yayi min meyasa zan yiwa deen haka?meyasa?ya karasa maganar kamar me shirin yin kuka

"Tsaki beelah tai me sauti tace koma menene mummunan halinsane yaja mishi,kuma Allah ne ya nuna mishi ishara....alhakin matan da yake lalatawane Allah ya fara saka musu,ai deen bega komaiba a rayuwa sadiq

"Ajiyar zuciya sadiq yayi yace nabeelah duk wani abu da deen yakeyi nine nan sanadi

"What?ta fada a cikin mamaki

"Of course BTW(by the way)idan na shigo zan fada miki kowaye deen,zan fada miki irin rayuwar da deen yake yi kafin ya hadu dani....

"Bana bukatar ji don koma menene ba abu bane me kyau,,,,kawai ta fada sannan ta kashe wayar zuciyarta babu alamar nadama

"Tun a daren sadiq ya gama shirya komai nashi ya yanki ticket,12pm sadiq ya sauka a 9ja

"A hankali ya tsuguna ya gaishe da dad din deen,kallonsa yaci gaba dayi cikin mamaki yace get out from my sight,ka fita a idona sadiq,saboda kaga deen ya haukace shine har rashin kunyar taka ta kawo nan ka tsaya a gabana?

"Dad i'm so sorry,wallahi nayi nadamar duk wani abu dana aikata muku a rayuwa,dad yanzu na kawo kainane ku yanke min duk wani hukuncin da kuka ga ya dace dani,amma don Allah don annabi kuyi hakuri dad.....ya karasa maganar kamar zeyi kuka

"Uban me wannan marar kunyar yazo yakeyi anan?ka tashi ka fice daga asibitin nan idan baso kake na hada ka da securities su sanja maka kamanni ba,shege dan iska tsinanne butulu,ai sadiq kai ba dan halak bane wlhy duk abinda deen keyi maka duk yanda deen ya daukeka shine zaka saka mishi da sharri ko?to mun gode yanzu ka kama hanya ka fice daga idona....mom ce tsaye take maganar fuskarta babu alamar dariya

"Dad ne ya kalleta da sauri yace haba hajiya mene kuma haka?ina ganinki mace me hankali da tawakkali ashe ba haka kike ba?ta yaya za'ace yaro yayi lefi yazo kuma yana neman gafara amma kice bazamu yafe ba,irin haka ne yake sa mutane koda sunyi niyyar tuba su koma ga Allah sai su tuna da irin wulakancin da za'ayi musu sai su fasa neman gafarar suci gaba da aikata abinda sukeyi,,,,,kallon sadiq yai dake tsugunne gabansa tace tashi yarona mun yafe maka duniya da lahira

"Kallonsu tai a wulakance tace nidai ban yafe ba sannan tai shigewarta cikin asibitin,,,jikin sadiq sanyaye yace dad ya jikin deen din?

"Sunkuyar da kansa yai kasa yace toh yau dai kwanansa 4 besan inda kansa yake ba amma likita yace insha Allah yau zai farka.....doctor ne ya karaso inda suke ya kalli dad yace ya farfado kuma ya samu lafiya baya tare da ciwon hauka ko kadan

"Sosai murmushi ya bayyana a fuskar dad da sadiq a tare suka ce Alhamdulillah

"Doctor ne ya sake kallonsu yace sedai kuma yayi loosing memory dinsa bazai iya tuna komai ba sannan akwai karaya daya samu a kafarsa zeci gaba da amfani da wheel chair har ya samu lafiya,,,,,,

Don't forget to vote
Thank you  for reading my story
Lot's of love!

DeenWhere stories live. Discover now