Chapter 46

2.4K 249 22
                                    

"Karasowa yayi da sauri har yana cin tuntube ya karasa gabanta yayi murmushi yace hey beelah yau kece gidan namu?

"Murmushi tayi tace wlhy sadiq nice nazo bikine ayi komai dani ta karasa maganar tana kallon peacocks din da suke tafiya

"Kallonta yayi cikin tsokana yace eh tunda kin qimu ai sai ki daure kizo mana biki ai

"Dariya tayi ta dan ciji lips dinta kadan sannan ta mika masa paper dake hannunta tace dama yanzu naganta a kasa da alama yardar da ita akayi,karba yayi ya bude yace oops ai wannan angon sarkin rawar kai har yana jefar da takardar test dinsu,,,,sannan ya karbi takardar ya juya zai karasa cikin gidan

"Kamar an mintsineta tai saurin kiran sunansa da sauri,juyowa sadiq yayi a firgice yace what?

"Murmushi tayi kadan alamar wasa tace bani takardar nan tunda nina tsinceta niya kamata na bayar da ita,dariya sadiq yayi sannan ya jefa mata takardar yace dama kamar kinsan ko dakinsa banason shiga saboda wannan mara kunyar amaryar tashi kishi takeyi da kowa ba macen ba namijin

"Wani takaicine ya taso mata ta dan daure tace kaga lefintane ai dole ta nuna kishi akan abinda takeso musamman gurin irinku masu hana ruwa gudu

"A tare sukayi dariya yace wlhy seriously beelah kinyi missing har kika bari deen zai auri wata yarinyar

"Harararsa tayi cikin wasa tace eh naji din nidai banaso akai kasuwa,sun dan jima suna wasa da sadiq kafin su karasa cikin gidan,a palour ta tsaya ta gaishe da duk matan da suke xaune mafi yawancinsu bata sansuba....aunty a'i ce ta karbi jakarta ta kai mata wani room da aka kayatashi da kaya masu kyau pink colour....sannan ta kalleta tace mata taje bedroom din mom din deen ta gaisheta kafin ta zauna

"Knocking tayi kadan aka umarceta da ta shiga dakin,tura kofa tai ta shiga zaune take akan gado inda wata mata me dan jiki ke zaune akan resting chair din dake kusa da gadon suna hira da alama shirye-shiryen bikin sukeyi,tsugunawa tai kasa fuskarta dauke da murmushi ta gaishesu,,,,,,kallo daya mom tai wa nabeelah ta galla mata harara sannan ta dauke idonta daga kallonta,sai hajiya saratu ce ta amsa gaisuwar tana sake kallon nabeelah tana yaba kyau da irin baiwar da Allah yayi mata

"Mom ce ta kalli nabeelah a wulakance tace toh ba mun gaisaba seki tashi ki wuce iya ta gaisheda assha......da sauri beelah ta fice daga dakin dama tasan za'a rina tasan halin mom tunda ta nuna kiyayyar deen kiri-kiri babu abinda ze hana mom nuna mata kiyayya

"Tana fita hajiya saratu ta kalli mom deen tace haba hajiya ya zaki dinga hantarar kyakkyawar yarinya irin wannan?irin wannan ai lallabasu ake ayi connection marriage da ya'yan governor's da president kema seki samu naki rabon ciki

"Murmushi mom din deen tai tace hajiya wannan fa da kike gani ba wata bace illa yarinyar da tace batason deen bata kaunarsa,hajiya a gaban idona ta kalli deen yarona dana haifa da cikina take furtamin cewar bata sonshi bata kaunarsa,,,,deen yasha wahala akan yarinyar nan hatta rayuwarsa ta kusa salwanta akanta da kyar Allah ya taimakemu ya cireta daga zuciyarsa ya dauki kaddarar auren zulaikha,,,,meyasa bazan hantaretaba wallahi hajiya na tsani yarinyar nan ko kallonta bana sonyi sai dole kinsan yar gidan aminin alhajice kuma gaskiya iyayenta mutanene masu kirki da halacci ita kadaice batayo halinsuba,,,shigowar aunty a'i ce ta sasu saurin chanja hira

"Akan hadaddem gadon ta fada duk da karamine amma ya birgeta sosai,window din dake kusa da gadonta ta bude don ta gaji da kwanciyar tanaso ta dinga hango waje kasancewar a upstairs dakin yake......sake bude ido tai tana kallon sports field din data hango deen sanye cikin jersey red colour sunyi matukar yi masa kyau tsaye yana table tennis game,,,,,murmushi tayi tana mamakin yanda ya dage yana table tennis shi kadai ba tare da abokin yi ba,cigaba tai da murmushi tana sake yaba kyau da sura irinta deen

"I wish we were together ta fada a hankali tana sake gyara tsayuwarta,zulaikha ta hango sanye itama da nata jersey din da alama tare suke playing table tennis din,cigaba sukayi da wasan cikin kwarewa a soyayya,saurin rufe labulen tayi ta koma kan gado ta kwanta jikinta a sanyaye zuciyarta na quna,,,,,,seda suka kwashe sama da 2 hours a sports field din kafin su bar gurin

"Bude jakarta tai ta dauko paper din ta ajiye akan mirror sannan ta shiga bathroom ta watsa ruwa ta fito,doguwar riga na atamta royal blue colour ta saka kayan sunyi matukar karbar jikinta duk da beelah ba wata me jiki bace amma tana da figure me daukar hankali,ji tayi tanaso tai kwalliya sosai a fuskarta haka yasa ta dauki lokaci me tsaho tana make-up duk da ba wani heavy makeup takeyiba amma ta dauki tsahon lokaci tana yin light make up....simple dauri tayi a kanta ta feshe jikinta da perfumes zafafa goma lol sannan ta yafa siririn mayafi a shoulder dinta ta nufi apartment din deen bugun zuciyarta na karuwa lokaci zuwa lokaci

"Knocking door tayi seda tayi 40 seconds tukunna yace come in,tura kofar tai ta shiga.....towel ne daure a waist dinsa yana taje kansa da alama yanzu ya fito daga wanka,,,,juyowa yayi ya zuba mata ido yana kallo kamar wanda yake kallon wani abin mamakin......seda suka dauki kusan 3 minutes suna kallon junansu kafin ya karaso inda take tsaye yace what?

"Sai a lokacin ta sake ganin hotness din deen sosai,da sauri ta fara ja da baya ta mika mishi takardar hannunta na rawa,takardar ya hade da hannunta ya rike sosai har seda tayi qara kadan ouchh,kallonta ya sake yi cikin wani kalar salon nashi yace daga yanzu idan kinyi tsintuwa ki dinga kaiwa immediately musamman important things like this ya fada yana nuna mata takardar.....be jira ta sake cewa komaiba ya juya yaci gaba da taje gashinsa

"Juyawa tai a fusace zata bar dakin da sauri yace heyy Mrs P.A (personal assistant),juyowa tai jikinta a sanyaye,,,,,can you help me with some coffee?

"Go to hell,ta fada ranta matukar bace ta juya zata fita daga dakin....sedai tana taba kofar taga yayi locking dinsa da remote din hannunsa,,,,,

"Tray ne a hannun zulaikha cike da fruits  ta tura kofar dakin taji a rufe murmushi tayi don tasan watakil baccine ya daukeshi ta koma dakinta ta ciro mukullin dake jakarta na dakin deen tukunna ta fara kokarin bude kofar dakin tace hey baby

Don't forget to check my new story MU'AMALAT

DeenWhere stories live. Discover now