Chapter 29

3K 248 43
                                    

"Mom ce ta shigo dakin ta tarar da batul zaune ta zuba tagumi,jikin mom sanyaye ta zauna ta dafa kafadar batul  tace batul

"Juyowa tai ta kalli mom cikin rashin walwala tace mom

"Ya kamata ki kwantar da hankalinki saboda deen ya tsaya akan maganar sannan ya debo lawyers wayanda zasu jajirce akan ganin an bi mana hakkinmu gaskiya munyi dana sanin yarda da sadiq ashe makashinka yana tare dakai kuma wlhy sadiq se yayi dana sanin yi miki fyade sai ya gwammace tsakanin kida da karatu sadiq ya gama rayuwar farin ciki don zai karasa rayuwarsa ne a prison ...mom ta karasa maganar tana tsaki

"Jin an ambaci sadiq zai karasa rayuwa a prison yasa batul rusa kuka

"A tsorace mom ta kalleta tace kiyi hakuri ki dena kuka insha Allah sai ya tabbata a wulakance,tana gama fadan haka ta fita daga dakin

"Tafiya yake kamar wani mara lafiya gaba daya duniyar zafi takeyi masa,elevator yai pressing ya karasa office,guri ya samu ya zauna ya dora hannunsa a kansa tunani barkatai yakeyi tare da zazzafar tsanar sadiq

"Good morning sir how can i help you?P.A din deen ce tsaye take ta faman yin magana amma sam bema jita ba,sake gyara tsayuwarta tayi ta danyi knocking table din kadan tace how can i help you sir?

"A firgice ya dago ya kalleta da zafafan idanunsa yace get out

"Jikinta ne ya dauki rawa kamar me shirin kuka tace am sorry sir

"Will you get out or i should take you out?ya karasa maganar yana nuna mata door

"Da sauri ta fice waje har tana cin tuntube da covered hill shoe din dake kafarta tana sake fadin am sorry sir

"Tsaki yayi ya zauna yana huci kamar wanda yayi dambe,sai a lokacin ya lura da takardar dake ajiye akan table dinsa,takardar court ce nabeelah ta kawowa deen yayi signing

"Whatt????ya fada yana sake duba takardar gaba daya,murmushi yayi ya jefar da paper din yace nabeelah you are mad bansan meyasa kike gangancin shiga rayuwataba kuma hakan babban kuskurene ko a tsarin constitution  (hahaha but a section nawa please)

"Kamar an mintsineshi ya mike har yaje bakin kofa ya koma ya dauki paper din da nabeelah ta kawo masa ya fita,parking space ya wuce ya dauki motarsa duk kuwa da gaisuwar da staffs dinsa keyi masa amma ko kallo basu isheshiba,a office din nabeelah yai parking paper din rike a hannunsa ya karasa....kafarsa yasa ya tura kofar sedai a rufe take tsaki yai ya fara knocking a fusace...Secretary din nabeelah ne ya bude kofar ganin deen ya sashi zubewa kasa yana fadin afternoon sir....thank you deen yace kamar wanda bayason yin magana,a tsorace nabeelah ta dago jin maganar deen a cikin office dinta tsoro sosai ya bayyana a fuskarta

"Taku 6 deen yayi ya karasa kan table din nabeelah,sosai bugun zuciyarta ya qaru,hannunta 2 ya rike da karfi sannan ya mikar da ita tsaye kamar wata karamar yarinya,hannu tasa ta tureshi tace don't you dare touch me with your filthy hands....how dare you....sake riketa yai sosai ya matse hannun har sai da tayi siririyar kara kadan tace stop it....i will not ya fada fuskarsa babu alamar wasa,shiru ne ya ratsa tsakaninsu kadan sannan deen ya saketa ya ajiye takardar akan table dinta yace take it,i will never ever sign on this fucking sheet
Murmushi tayi ta dauki paper din sannan ta kalleshi tace dama ba signing dinka nafi bukataba inaso idon azzzalumi kuma macuci wanda ya damu da damuwarsa shi kadai ba tare da ya tausayawa kowaba yasan cewar duniya cike take da masu daukan fansa kamar yanda kake kokarin bi wa batul hakkinta haka nabeelah take kokarin bi wa kanta hakki,sannan inaso kasan cewar batul itace ta kai kanta har mansion dinka kuma ta bukaci sadiq yayi amfani da ita a matsayinta na shashashar mazinaciyar mace.....ooouchhhh saukar mari taji a fuskarta wanda har sai da taga hasken wuta

"Mind your tongue nabeelah,i said mind your tongue nabeelah karki sake kiran batul prostitute ya fada a zafafe yana huci

"I will not domin kai kanka na dade ina kiranka mazinaci wanda Allah yake fushi da dukanin masu irin halayenka,nayi danasanin saninka a rayuwata banza macuci azzalumi kamar yanda ka lalata min rayuwata insha Allah ka rabu da ganin farin ciki a rayuwarka....hannu yasa ya matse bakinta yaci gaba da kallonta sannan yace a yaushe na lalata miki rayuwarki?kina nufin nayi raping dinkine?well idan har nayi raping dinki meya hanaki sanarwa iyayenki su dauki mataki a kaina?murmushi yayi yace hakan yana nufin ni banyi raping dinki ba kece kikazo har inda nake don haka karki sake gangancin cewa nayi raping dinki kuma ki gaggauta fita daga cikin case din sadiq don deen baya aiki da qananun lawyer's....you are too young babe....young lawyer ya karasa maganar yana murmushi

"Da karfi ta ture hannunsa daga bakinta tace anya kuwa kana tsoron Allah?anya kuwa kana da zuciya a cikin kirjinka?anya kuwa zaka gama da duniya lafiya?meyasa baka da tausayi?meyasa kakeson kanka dayawa?meyasa kake mantawa da lahirarka?meyasa kake daukan dukanin wata gaskiya a zuwan karya?meyasa karya ta zama abinci da ruwan sha a cikin rayuwarka?ka lalata yammata wanda bazasu lissafu ba kuma ka zauna lafiya amma kai akan an lalata kanwarka shine har kake rantsuwar cewar bazai bar prison ba?bakasan muma kannen wasu bane?meyasa rayuwarka kawai ka sani baka damu da rayuwar kowa ba?ta karasa maganar cikin kuka

"Ajiyar zuciya yayi yace how can i answer all this kind of stupid questions?

"Why are you answering my questions with a question?ta fada a zafafe

"Coz you are very stupid ya karasa maganar yana kallonta up and down sannan ya fita daga office din

"Zubewa tai a kasa ta fashe da kuka a hankali tana fadin i hate you,i hate you ka shigo rayuwata ka hanani jindadi ka takurawa rayuwata....insha Allah se ka wulakanta deen,sai ka zamo abin gudu a gurin kowa,sosai take kuka take sumbatu

After 2 months
"What???doctor what are you saying?batul is pregnant?innalillahi wa inna ilaihir raj'un deen ya karasa maganar yana zama akan chair,doctor ne ya mikawa batul paper din test sannan ya fita daga gidan ya basu guri

"Sosai gumi yake zuba a jikin deen,mom da batul tsaye kamar wayanda aka turowa da sakon mutuwa....zagaye deen yaci gaba dayi a palour din kamar wani soldier sannan ya kalli batul dake tsaye kusa dashi yace this will never happen wallahi bazamu taba accepting wannan cikin a gidan nan ba,we will never accept a criminal child in this family

"Mom ce ta kalleshi tace then what do you want us to do?

"Abort the baby,we will abort this child mom

"A firgice mom ta kalleshi tace do you know what you are saying?it's a baby we are talking about fa deen

"So what?i don't care,and if you didn't agree to abort the baby then i will still do what i think it's right for me,it will just bring shame to our family besides i know she don't like it too

"Dad ne ya karasa saukowa daga upstairs yace deen you are wrong,you are thinking wrong.....abinda yake cikinta da kai duk dayane meyasa kake shirin aikata kisan kai?dukkaninku Allah ne ya hallicceku sannan zancen jin kunya kuma idan munce bamason jin kunya a duniya ranar lahira kuma fa?me zamuce da ubangiji?kana tunanin dabarace mu bata lahirarmu wajen  gyara duniyarmu?

"Sunkuyar da kansa yayi kasa yace toh amma dad idan har batul ta haihu da sunan cikin shege wa kake tunanin zai aureta?yanzu rayuwar batul zata zamo irin rayuwar sauran yaran talakawa da muke gani a bakin titi jibge babu mazajen aure ana kiransu karuwaine cikin shege sukayi?haba dad....haba dad

"Murmushi dad yayi yace haka Allah ya kawo mana tamu kaddarar kuma ya zama dole mu karbeta....idan kana zancen sauran yaran talakawa suma duk wasunsu hakan ce ta faru dasu wasu da son ransu wasu kuma bada son ransuba kuma sakayyarsu tana gurin Allah S.W.T shine zai zaka musu domin akwai azaba mai tsanani ga duk wanda ya lalata rayuwar mace domin mata suna fuskantar kalubale sosai a rayuwarsu

"Amma meyasa dukanin matan da nake lalatawa babu wacce ta dauki ciki?meyasa nabeelah da nayi amfani da ita tsawon watanni amma bata samu cikiba?sai batul?......deen yaci gaba da magana a zuciyarsa

A/NFire on the mountain run run run run hahahaI am backAlhamdulillah Allah ya bani lafiya,sannan another surprise shine zaku dinga samun update kullum insha Allah

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

A/N
Fire on the mountain run run run run hahaha
I am back
Alhamdulillah Allah ya bani lafiya,sannan another surprise shine zaku dinga samun update kullum insha Allah

DeenWhere stories live. Discover now