Chapter 35

2.7K 253 45
                                    

"Sosai deen yake surutai da buge-buge har sai an mishi allurar bacci ta mahaukata tukunna ake samun saukinsa

After 4 Months

"A hankali take saukowa daga private jet dinsu,sanye cikin black Indonesia abaya da black veil saboda abaya was her favorite outfit,direct gurin black Mercedes-Benz 2018 model ta karasa  ta shiga driver ya fara driving, a babban parking space din gidan motar tayi parking nabeelah ta fito a hankali tayi murmushi tace "home sweet home"

"Wanka ta shiga tayi sannan tai sallar azhar ta karasa dinning area ta ci abinci saboda bata tarar da kowa a gidan ba,sosai nabeelah take jin nishadi don tun wayarta da deen na karshe be sake kirantaba hakan yasa ta tunanin ya hakura ya rabu da itane,,sai bayan la'asar ta farka daga bacci me nauyin daya dauketa tai saurin gabatar da sallar la'asar ta fito main parlour....murmushi tai ganin aunty A'i harta dawo tace Aunty wai ina kikaje ne?instead na dawo inga kuna yimin welcome back sai kuma naga babu kowa?ta karasa maganar cikin shagwaba

"Sorry beti,na manta ban fada miki bane zamuje dubiya?

"Dubiya kuma aunty waye bashi da lafiya?beelah tai tambayar cikin mamaki da tausayi

"Itama aunty A'i saurin kallon beelah tai tace kina nufin bakisan deen bashi da lafiya ba?

"Tsaki nabeelah tai tace toh banda abinki aunty i don't have any business with him taya zan sani?

"Wai nabeelah kina nufin bakisan deen ya haukace ba?

"A firgice nabeelah ta zaro manyan idanuwanta tace hauka aunty?kina nufin deen is mad yet?

"Daga mata kai tayi tace of course tun last 4 months ya haukace an rasa gano meye matsalarsa,sedai yayi ta sambatu yana bige-bige dazu haka har hawaye na zubar wa yaron nan saboda tausayi....bakiji kalaman da yake fadaba na batanci da kansa,kayan shaye-shaye da sauran abubuwa yake ta fada yake cewa ya aikata kinga abin da tausayi don kowa yasan deen yarone me nutsuwa da kamala....nafi tunanin asiri akayi masa don gaskiya deen mutum ne mai nutsuwa da hankali ga addini wallahi nabeelah ba don tuntuni kinqi deen ba inason kasancewarki mata a gurinsa.....

"Ni din?wlhy aunty bana sonsa ko kadan nabeelah ta fadi maganar ranta a hade

"Nabeelah ke yarinyace karama har yanzu baki san namijin da yafi dacewa dake ba amma deen shine mijin da yafi dacewa dake tun a lokacin baya.....mom stop it please nabeelah ta fada kamar me shirin yin kuka sannan ta juya ta koma daki ta kulle gabanta na faduwa

"Hauka?what's wrong with him?what happened to him kuma?murmushi tayi har dimple dinta ya lotsa kadan sannan ta daga hannunta sama tace Alhamdulillah Allah nagode maka daka karbi addu'ata da sauri haka,,Allah nagode maka daka fara nunawa wannan la'anannen bawan naka ishara tun a duniya....fashewa tai da wani rikitaccen kuka wanda ita kanta bata san dalilin yin hakan ba a daren ranar sam nabeelah bata rintsaba ta rasa menene yake damunta

"Doctor but kana ganin deen ze samu lafiya kuwa?dad din deen ne tsaye yake yiwa doctor tambaya cike da damuwa

"Yes sir muna tunanin haka sedai har yanzu mun kasa gano which type of madness he's suffering with,akwai kalamai da yake yawan fada cewar yana shaye-shaye sannan yana lalata yaran mutane kana ganin bazamu dauki wannan maganar serious ba????saukar mari ce ta dakatar da doctor daga maganar da yakeyi a fusace dad ya kalleshi bayan ya sauke masa mari a fuskarsa yace point of correction,you have to mind your tongue doctor mu nan da kake gani ba mutanen banza bane,deen ba irin yaran da kake tunani bane idan duk duniya bata yarda da deen ba mu iyayensa mun yarda dashi,,,,,,inaso kasan cewar deen ko hayakin abinci bayaso ya shaqa balle har ya dauki cigarette yace ze sha,deen baya harka da kayan shaye-shaye sannan deen yarone mai kamun kai,addini,nutsuwa da kunya hakan yasa ko hada ido da macce be fiye yiba balle har yayi lalata da mata don haka duk wasu kalamai da zaka ga sun fito daga bakin deen a asibitin nan to kasan cewar yanayin hakane ba a hayyacinsaba yana yin hakane cikin haukan da yake fama dashi

"Sorry sir,i am sorry sir doctor ya fada sannan ya kalli wrist watch din dake hannunsa yace lokacin bashi magani yayi.....

"Knocking door dinda ake tayine ya tashi beelah daga bacci sannan ta bude taga aunty A'i tsaye sanye cikin sky blue din shadda,sunkuyar da kanta tai kasa tace ina kwana aunty....lafiya lau sleeping head maza jeki shirya dad dinki yana jiranmu

"Cikin mamaki beelah tace ina zamuje kuma?

"Dubiya mana ai kullum sai munje duba deen asibiti

"Turo baki beelah tai tace ni gaskiya baza niba

"Cikin rashin fahimta aunty a'i tace meyasa?

"Aunty kaina ke ciwo wlhy i'm having a little headache

"Murmushi tai tace kinsan dai halin dad dinki sarai bayason disappointing don haka maza kiyi sauri ki shirya kisha paracetamol,banda abin nabeelah ma keda zakije asibiti ai kema sai a baki treatment....ta karasa maganar tana dariya

"Okay kawai nabeelah tace tukunna ta shiga bathroom,bayan ta fito batayi wani heavy makeup ba ta dauko straight gown na lace red colour dinkin ya zauna a jikinta sosai ta fesa perfume ta daura dankwalin kayan sannan ta dora veil din a shoulder dinta ta fito...

"A mota ta tarar dasu dad suna jiranta,dad neya kalleta yace lazy big head sai yanzu?

"Murmushi tai tace nooo dad nidai ka dena cemin lazy big head,,,,i am not lazy fah....yanda tai maganar gaba daya sukayi dariya har suka karasa hospital din suna hira,,,,a kofar asibitin dad din deen da dad din beela suka hadu daga nan beelah da aunty a'i suka karasa cikin dakin da deen yake gaban nabeelah na dukan uku-uku

"Cikin sallama suka tura kofa suka shiga,mutum 4 ne a dakin zaune tare da deen sai securities da suke tsaron deen....da sauri deen ya bude idonsa ya saukesu akan nabeelah,,,,sosai deen ya rame yayi baqi gashin kansa duk ya sanja daga yanda yake da.....a zahiri nabeelah ta furta kalmar innalillahi wa inna ilaihir raj'un duniya budurwar wawa,duniya babu komai cikinta sai tarin jarabawa,,,,yanzu deen ne haka cikin wannan halin?ina gayun deen?ina kudinsa?ina kyan nashi da yake taqama?ina farin jinin sa?ihun da deen yayine ya firgita kowa dake cikin dakin lokaci daya ya karya gadon da yake kai ya mike yana wani gurnani ya nufo gurin nabeelah

"Da gudu ta fita daga dakin shima ya ture duk securities din dake kokarin rikeshi yabi bayan nabeelah da gudu....

Don't forget to vote,share and comment
Thank you for reading my story
Lots of love!

DeenWhere stories live. Discover now