Chapter 33

2.6K 242 22
                                    

"Kansa ne yaci gaba da sarawa a hankali ya zame ya zauna akan daya daga cikin cushions din gumi yaci gaba da zubo mishi,cigaba yayi da kiran number batul sedai amsa daya ake bashi wayar is switch off....Oh my godness wai meyake faruwa danine komai ya zama worst a gareni?shine tambayoyin da yaci gaba dayi a zuciyarsa,,,,itama mom zubewa tai a kasa tana cigaba da hawaye inda dad ke tsaye yana sake karanta paper da batul ta ajiye musu sannan ya dago ya kallesu yace karna sake ganin kowanne cikinku ya shiga damuwa indai akan batul ne..tunda ta zabi barin gida toh ina ganin ta ciremu daga cikin wasu important people's dinda ta sanine a rayuwarta don haka muma yana da kyau muyi saurin cireta daga zuciyarmu

"A firgice mom ta dago ta kalleshi tace but Alhaji kana ganin wannan maganar daka fada babu wani gyara a ciki?taya zamu haifi yarinya da cikinmu ace kuma mu manta da ita?kafin ta karasa maganar har dad dinsu deen ya fita daga dakin...fashewa tai da kuka

"Shima deen key din motarsa ya dauka jin zuciyarsa nayi masa wani zafi kamar zata fito,ya dade a mota kafin ya karasa gida...bar dinsa ya wuce direct ya fara shan whiskey kamar yanda ya saba idan ransa ya baci idan yanason yin bacci amma har 2am deen bai samu barciba sai tunaninda yake ta karuwa a zuciyarsa....tunanin nabeelah shine mafi worst da yafi yi don wannan karon yana jin idan har nabeelah taqi amincewa ta aureshi zai iya rasa rayuwarsane

"8am ya sauko daga kan bed dinsa,bathroom ya shiga yayi refreshing kansa tukunna ya shiga kitchen....idonsa ne ya sauka akan wani babban banner din da aka liqa kusa da electric cooker an rubuta MEN AT WORK...murmushi yayi don sadiq ne yayi art din kuma ya saka banner din a kitchen sosai yaji yana missing din sadiq don deen sam be iya girki ba sadiq shine yake shiga kitchen yayi musu girki idan basu da ra'ayin yin order din abinci nearest restaurants....freezer ya nufa don shi ya rasa me zeyi ma...wani paper dinne manne jikin fridge din ansa DON'T OPEN..I SAID DON'T OPEN....besan sanda ya bushe da dariya ba har yana tafa hannu cikin dariya yace you are worst sadiq....da sauri ya hade ransa kamar an aiko mishi da mutuwa ya juya ya fita daga kitchen din ransa a matukar bace

"A fridge din parlour ya samu fresh milk da chocolate cake yaci duk da deen ba meson zaqi bane sosai...be jima da gama breakfast ba ya fito ya shiga range rover ash colour driver yaja shi suka tafi....a office din nabeelah sukayi parking deen ya fito jikinsa a sanyaye ya karasa office dun nata,wannan karon beyi knocking ba kawai ya shiga ciki

"Zaune take cikin black dubai abaya tayi rolling kanta da black veil din kayan tana having breakfast,da sauri ta dago kanta ganin deen ya shigo ko sallama babu,shiru tayi batace komai ba ta maida hankalinta gurin files din da take dubawa zuciyarta na bugawa sosai....hannu yasa ya rufe file din da take dubawa yace hi,banza tayi mishi batace komai ba ta sakar masa takardar ta dauki wayarta ta fara duba messages,,,hannu yasa ya kare wayar daga hannunta yace i said hi....sallama ceta dace gurin nan ba hey ba ta fada a fusace

"Assalamu Alaikum ya fada jikinsa a sanyaye,ba tare data kalle shiba tace amin....lumshe idonsa yayi yace amma ina tunanin nace amincin Allah ya tabbata a gareki bai kamata kice min amin kawai ba yana da kyau ki amsa da Amin wa'alaikumusalam nima ki neman min aminci a gurin Allah kamar yanda na neman miki....tsaki tayi sannan ta dauki wayarta ta dauki handbag dinta ta nufi hanyar waje

"Shan gabanta yayi yace where are you going?

"That is not your business ta fada a takaice

"But i wanna know

"Hannu tasa ta tureshi sedai kafin ta karasa tureshi yayi joining hands dinsa yai hugging dinta very tightly....don't leave me please beelah you are my everything,you are my love...my life....please babe don't leave me,,,,da karfi tasa hannu ta tureshi tace don't you dare hug me again ta karasa maganar breath dinta yana fita very hardly sannan ta juya ta bude kofa zata fita

"Hannunta ya riki yace please beelah we need to talk,duka 2 takai mishi a chest dinsa kamar wata karamar yarinya tace i said don't you dare touch me again idiot,wai kai wanne irin maye ne....stop touching my body nace bana sonka,bana sonka ka rabu dani mana

"Ouchhhh so sweet ya karasa maganar idonsa a rufe hannunsa nakan chest dinsa data ke dukansa,,,,murmushi yayi yace i really enjoyed it

"Yanda kake enjoying  haka zakayi enjoying hell tsinanne kawai ta karasa maganar cikin tsiwa,hannu yasa ya murda lock a jikin kofar sannan ya kalleta yace meyasa bakyasona beelah?

"Saboda na tsaneka ta fada ba tare da wani tsoro ba

"Meyasa kika tsaneni?

"Saboda kai tsinanne ne,la'ananne,mazinaci,maha'inci,macuci kuma mahaukaci wanda tsinuwar Allah take bibiyarsa,wallahi na tsaneka bazan taba sonka ba shiyasa nakeso kayi saurin fita daga rayuwata

"Ajiyar zuciya yayi jikinsa a sanyaye yace idan kuma.....be karasa maganaba wayar beelah ta fara qara hango sunan wanda ke jikin wayar yasa deen saurin daukan wayar da sauri duk da kokawar da nabeelah keyi seta kwace wayar amma deen yayi answering call din....hannunsa ne dauki rawa ya kalli beelah a firgice

Boom Alert:Zan sake yin wani update din tonight just manage this....

Don't forget to vote,share and comment

DeenWhere stories live. Discover now