Chapter 31

2.8K 250 19
                                    

"Juyi yake sam baccin ya kasa zuwa,tunanin nabeelah yakeyi gaba daya tausayinta ne ya cika mishi zuciya

"Itama nabeelah ta kasa yin baccin sai juyi takeyi tsanar deen ce takeyi mata yawo a zuciyarta,tsaki tayi ta gyara kwanciyarta don ko tunanin deen bataso zuciyarta ta dinga yi ko kadan

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

"Itama nabeelah ta kasa yin baccin sai juyi takeyi tsanar deen ce takeyi mata yawo a zuciyarta,tsaki tayi ta gyara kwanciyarta don ko tunanin deen bataso zuciyarta ta dinga yi ko kadan....

"Tashi tayi ta daura alwala ta fara gabatar da sallar nafila idan tazo sujjud na karshe tana karanta "subhanallah walhamdulillah wala'ilaha ilallah wallahu akbar" sau dari sannan ta mike tayi tahiya ta sake karanta "subhanallah walhamdulillah wala...

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

"Tashi tayi ta daura alwala ta fara gabatar da sallar nafila idan tazo sujjud na karshe tana karanta "subhanallah walhamdulillah wala'ilaha ilallah wallahu akbar" sau dari sannan ta mike tayi tahiya ta sake karanta "subhanallah walhamdulillah wala'ilaha ilallah wallahu akbar" shima kafa dari sai tayi sallama ta daga hannunta ta roki Allah ya yaye mata dukkanin wani damuwarta

Note:Wannan sallar sallah ce sahihiya wacce bata da wani hijabi idan mutum yana da wata bukata a gurin ubangiji toh ya lazimci yinta har tsawon kwana 3 bi'izinillah Allah zai biya mishi duk wata bukatarsa ta alkhairi

"Har sai da tayi sallar asubha tukunna taji bacci yana dibanta ta tashi ta koma kan gado bacci ya dauketa....sai 12pm tukunna ta farka ta shiga bathroom tayi wanka ta dauko tea da chips ta fara ci....maid din gidan ce ta fara knocking door,,,come in ta fada tana karasa hadiye omelette din bakinta

"Okay kawai tace ta mike tsaye ta goge hannunta da tissue ta dauki siririn mayafin abayar dake jikinta ta yafa ta fito palour....kallon aunty A'i tayi cikin shagwaba tace Aunty gani

"Murmushi aunty A'i tai tace kije guess room yanzu kina da baqo

"Bata rai nabeelah tayi tace waye?

"Itama cikin fushi ta kalli nabeelah tace nima bansaniba idan kinje koma waye sai ki ganshi

"Tsaki tayi a ciki-ciki sannan ta nufi guess room zuciyarta na tunanin waye haka yazo nemanta?tura kofa tai ta shiga sannan ta mayar ta rufe ta nufi daya daga cikin cushions din dake dakin zata zauna ba tare data kalli waye yazo gurintaba...kamshin turaren da taji ne ya sata saurin kallon gurin da yake a zaune,,,,deen ta gani zaune cikin white shirt da black trouser wanda sukayi matukar yi masa kyau kamar ba indiye

"Da sauri ta mike ba tare da tace mishi komai ba ta nufi kofa zata fita daga dakin,sedai tuni har deen ya rike mata hannu cikin romantic voice dinsa yace wait....cikin fushi ta daga hannunta ta sauke mishi kyakkyawan mari akan kyakkyawan cheek dinsa ta juya zata fita

"Sake riko hannunta yayi a karo na biyu yace more please....

"Hannu tasa ta sake wankeshi da mari cikin fushi tace i hate you,i hate you ka fita daga harkata na tsani ganinka a duniyar nan deen....wallahi zan kasheka idan kaci gaba da takurawa rayuwata ta karasa maganar hawaye na zubowa daga idonta

"Hannunsa yasa ya tare hawayen da suka zubo daga idonta ya sauka a hannunsa sannan yayi kissing hawayen dake tafin hannunsa yace you hate me and i love you

"Tsaki tai ta tureshi daga bakin kofa ta kai hannunta zata bude kofar.....ya sake rike ta a karo na 3....wannan karon kafarta tasa ta dakeshi da karfi tace karka sake taba min jikina,niba yar iska bace irinka,tsinanne,azzalumi wanda besan halal da haram ba

"Murmushi yayi yasa hannunsa akan gashinsa ya sake matsowa kusa da ita sosai yace i love you beelah

"And i hate you,i hate you asshole....wai kai wanne irin mahaukacine nace maka banasonka,banasonka,banasonka ana dole ne ta karasa maganar cikin tsiwa

"Murmushi yayi yace banason pretending nasan kina sona ki fadamin kawai please

"Over my dead body ai ko na rasa mijin da zan aura bazan taba auren idiot person like you ba

"Sake matsowa yayi ya hade chest dinsu guri daya yace i love you

"Wallahi zan kasheka idan kaci gaba da hada jikin ka da nawa,zubewa tai a kasa a gabansa kamar me neman gafara sannan ta kalleshi tace please na rokeka don girman Allah daya haliccemu baki daya ka fita daga cikin rayuwata,Don Allah don Annabi karka sake hada inuwa dani wallahi na tsaneka deen tsanar da ban taba yiwa kowanne dan adam ba,don Allah ka taimaka ka nisanta kanka dani nima kuma zanyi kokarin nisanta kaina dakai....tsakanina dakai Allah ya isa bazan taba yafe maka ba har abada na tsaneka na tsani ganin fuskarka a duniyar nan.....idan akwai wani buri da nake dashi a duniya bai wuce naga Allah ya la'anceka ba

"Da sauri yasa hannu ya toshe mata baki yace stop it... ya isheki haka,ture hannunsa tayi da sauri cikin kuka tace bazan dena ba tsinanne,Allah ya tsine maka albarka kamar yanda ka wulakanta min rayuwa kaima bi'izinillahi sai  Allah ya tozarta ka rayuwarka bazata taba yin kyau ba....na tsaneka,na tsaneka ka fita daga gidanmu banason ganinka

"Shima zube gwiwoyinsa yayi a gabanta kamar yanda tayi yace please nabeelah kiyi hakuri,nasan nayi kuskure kuma kece mace ta farko dana fara zubewa a gabanta ina neman gafara.....ganin suna iya jiyo numfashin junansu yasa nabeelah saurin mikewa tace ka fita nace...bazan taba yafe maka ba,macuci,mayaudari kawai....ka fita nace ta karasa maga tana nuna masa kofa

"Sake matsowa yayi kusa da ita yace please,cup din glass din dake gefenta ta dauko ta kwadawa deen a kansa cikin kuka taci gaba da fadin ka fita nace tsinanne bazan taba yafe maka ba,wallahi ko hangoka nai cikin wutar jahannama ya rage sena yafe maka ka fito wallahi bazan taba yafe maka ba

"Da sauri ya dora hannunsa akansa,jini ya fara saukowa a goshinsa ya kalleta da jajayen idonsa yace  oucchh beelah kin jimin ciwo fa...kallonsa tai a wulakance tace so what zanfi kowa farin ciki idan ya kasance kasheka nayi ba ciwo kawai naji maka ba....muddin kazamin hannunka marar tsarki be fasa taba jikinaba

"zan tafi ba don na gaji da ganinkiba sai don zuwa a dubamin lafiyata,saboda na dawo naci gaba da rokon yafiyarki da soyayyarki

"Tsaki tai tace bazaka taba samun daya daga cikin suba kuma insha Allah sai kayi mutuwar wulakanci,shege marar tausayi mai lalata rayuwar mutane saboda zalinci da son zuciya.....murmushi yayi kadan ya ajiye mata wayarta akan center table sannan ya fita daga dakin ba tare da yace komai ba

"Dora hannunta tayi a kanta tace oh lord of mercy wannan wacce irin masifa ce haka take bibiyata,tunda na fara dora idona akan deen naketa shiga matsala...tissue ta janyo ta goge jinin deen kadan daya bata mata hannu tukunna ta koma cikin gida

"Wayar tace taci gaba da ringing,tsaki tayi ta dauki wayar ganin number batul ya sata daidaita muryarta tace am sorry batul just give me some minutes yanzu zaki ganni...

Don't forget to vote,share and comments

DeenWhere stories live. Discover now