Chapter 51

3.6K 367 54
                                    

"Wayarta ta kara a kunnenta ta kira kawarta wacce suke harkar malamai da bokaye tare hajiya hindu tace tanason ganinta yanzun nan zasu fita tare,ba'a wani dauki lokaci ba hajiya hindu ta karaso suka wuce gurin boka me ruguzau,zaune suka tarar dashi ya juya baya yana wasa da wuta cikin muryarsa me ban tsoro yake fadin ruguzun ruguzun se munyi ruguzau muke samu nasara,ruguzun ruguzun se munyi ruguzau muke samun nasara hahahahaa,,,sai daya dauki kusan 5 minutes yana ihu tukunna ya juyo ya kallesu da fuskarsa marar kyan gani da yayi mata paint da wasu irin kaloli yace nasan meke tafe daku,kuma kun kawo kukanku inda za'a share muku hawayenku.....kinaso a cire soyayyar nabeelah daga zuciyar yaronki deeni sedai kin makaro domin da soyayyar nabeelah aka halicci zuciyar deeni raba zuciyar deeni da soyayyar nabeelah dai-dai yake da daukan bindiga ayi masa kisan wulakanci da zarar na cire soyayyar nabeelah a zuciyarsa baze sake kwana 1 ba zai bar duniya,,,,a tsorace mom ta kalli hajiya hindu dake tsugunne tace na shiga 3 kinajin me yake cewa kuwa?murmushi hajiya hindu tai tace ki kwantar da hankalinki sannan ta kalli boka me ruguzau tace boka bamu da kowa se kai kuma dakai muka dogara ya kamata ace ka taimaka mana muna cikin damuwa,bushewa yai da wata mahaukaciyar dariya sannan ya dakata kadan yace toh zan temakeku zan tura aljani basamude ya danneta bazata sake tashi daga inda takeba har se ranar mutuwarta sannan zamu tura mata aljani dan kurma ya shiga jikinta daga ranar bazata sake magana ba zata zama summun bukumun,toh tanan ne yaron zega meyasa ze auri wacce take nakasasshiya,,,,a tare mom da hajiya suka tafa sukayi shewa suka zubewa boka kudade suka tafi zuciyarsu fes

"Ganin har 11am nabeelah bata fito tayi breakfast ba yasa aunty a'i karasawa apartment dinta,ganin halinda take cikine ya sata kwalla kara cikin tsananin rikicewa ta sanar da dad dinta aka kaita asibiti,sosai likitoci suka ci gaba da bincike akan cutar nabeelah amma har tsahon 1 week kwance take bata iya tashi ko kadan kuma bata iya yin magana,daga karshe aka bawa aunty a'i shawarar a koma yi mata maganin gargajiya ko za'a dace

"Zaune ya tarar da dad yana karanta newspaper yayi murmushi ya gaisheshi,cikin farin ciki deen ya kalli dad yace dad dama inaso muyi wata magana me mahimmaci,gyara zamansa yayi yace ina jinka deen fadamin ko menene

"Dama dad inaso in fada maka cewar zan auri nabeelah a haka,deen ya fada yana sunkuyar da kansa kasa

"Sosai Alhaji modibbo yayi mamakin jin kalmar deen sedai a zahiri be nuna masa mamakinsa a fili ba sai sake hade fuskarsa da yayi yace kana nufin zaka auri nabeelah duk da halin nakasun da Allah ya dora mata?

"Daga kansa yayi yace eh haka nake nufi dad

"Baze yiwuba,wlhy bazai yiwuba kuma ba'a cikin gidan nan ba,wai deen ka fara shan giyane ko kuma ka fara haukane da hankalinka da komai kace zaka auri yarinyar data nakasa kullum rayuwarta a kwance bata magana,inaso ka gane cewar akwai banbanci tsakanin mutum cikakke da kuma wanda ba cikakkeba,baka tunanin wannan abin kunyane a cikin zuri'ar nan ace yaron mu tilo ya auri mace nakasasshiya?toh wlhy baze yiwuba jinina bazai taba auren nakasasshiya ba,mom ta karasa magana tana rike kugu

"A tare deen da Alhaji modibbo suka kalli mom sedai babu wanda ya bude baki yace mata komai sai kallon banza da Alhaji modibbo yayi mata sannan ya kalli deen yace ka amince zaka auri nabeelah a halin data tsinci kanta?

"Da sauri deen ya daga kansa yace eh dad ina son nabeelah

"Kuma ka amince zaka rike amanarta domin duk wata kulawarta zai koma hannunka,alhaji modibbo ya karasa maganar yana nanatawa

"Daga kansa yai yace insha Allah dad

"Masha Allah,yanzu ma daga nan zan wuce gidansu nabeelar domin ba karamin jihadi zakayiba deen auren mace nakasasshiya a wannan zamanin abune mai matukar wahala

"Mom ce ta zube a kasa gumi ya fara zubo mata tana sake nanata kalmar bazai yiwuba,ta kira number hajiya hindu suka wuce gurin boka me ruguzau.......zubewa tai gabansa tana zubar da hawaye tace boka don Allah ka taimaka min,,,,a fusace ya kalleta yace dakata,nace ki dakata min nan gurin ba'a kiran sunan Allah nan gurin shedanune saboda haka duk sanda kika kira sunan Allah aljanunmu da shedanunmu suna guduwa ne subar gurin kuma mu aikinmu baya yiwuwa seda shedanu domin dasu muka dogara,,yana gama fadar haka ya bushe da wata mahaukaciyar dariya.....subhanallah wa'iyazubillah Allah kai mana tsari daga aikata haramun Allah ka rabamu da kaucewa hanyarka,Allah ka doramu akan hanyarka madaidaiciya....Allah kasa mu mutu muna aikata alkhairi tare da kalmar shahada a bakinmu amin..

"Ajiyar zuciya mom tai cikin tsoro tace ka gafarceni aljani kurungu ya taimakeka boka nayi kuskure amma wannan aikin da kaimin nema yake ya dawo kaina domin deen ya amince zai auri nabeelah a halin da take ciki yanzu,,,,bushewa yai da wata dariyar sannan ya hade fuskarsa kadan kamar mahaukaci yace yanzu me kikeso ayi?gyara daurin dankwalinta tai tace inaso kada ya kuskura ya aureta,,,,wata kwarya ya janyo da take cike da ruwa ya fara dube-dube cikinta sannan yace bazai yiwuba....sam sam bazai yiwuba munyi kuskure babba

"A tsorace mom ta kalleshi tace kuskure kuma boka?daga mata kai yayi yace kuskure babba ma kuwa domin ya zama dole deen ya auri nabeelah bamu isa mun canja masa ra'ayiba,,,a tsorace ta sake kallonsa tace kana nufin dole seya aureta kenan?kwarai kuwa seya aureta boka ya fadi maganar a takaice,,,gyara zamanta tai ta fara fiffita da gefen mayafinta tace boka yanzu tunda kace seya aureta kawai nina hakura da nakasar da akasa mata kawai a mayar da ita yanda take lafiyayya daga nan seya aureta din amma ni yanzu wannan abin kunyane a gareni aga yarona ya auri matar da kullum take a kwance

"Dariya ya kwashe da ita yace kin makaro,nace kin makaro mu ba'a mayar mana da aikinmu baya idan mukai aiki anyishi kenan,dora hannunta tai a kanta tace boka yanzu babu wani taimako da zakamun?shiru yayi kadan yace akwai taimako daya da zanyi miki shine zamu kasheta mu rabata da duniyar amma se kin cika sharadin dazan lissafo miki yanzu ba tare da kin kauce ko guda daya ba don idan aka samu matsala toh duk abinda kikayi kan yaronki zai koma

"Gyara zama tai cikin farin ciki tace fadamin boka duk abinda ake bukata zanyi indai wannan shegiyar yarinyar zata bar duniya don abin kunyane ace yaron dana haifa da cikina ya auri marar lafiya.....toh inaso ki kawomin ruwan hawayen deen da mahaifinsa nan da hour 4 dashi zamuyi anfani mu kasheta,a firgice mom ta kalli boka tace haba boka hawaye kuma ni yanzu ina zan samo hawayen deen dana alhaji dukkaninsu jaruman mazane babu yanda za'ayi in samu hawayensu

"Bata rai yayi yace toh wannan shine sharadin dana gina miki ya zama dole ki kawo,gabantane ya fadi cikin tsoro tace ina ganin kawai nina hakura da abinnan zan barshi ya aureta din kawai ta karasa magana jikinta sanyaye

"Dariya yayi sosai har yana dafe cikinsa sannan yace bakin alkalami ya riga ya bushe ai tuntuni na fada miki indai baki cika sharadin dana lissafa mikiba toh lallai yaronki deen zamu turawa mutuwar wulakanci,ya kara bushewa da wata dariya

Vote,share and comment

DeenWhere stories live. Discover now