Chapter 48

2.7K 377 77
                                    

"Mom da zulaikha din aka daura masa aure?sadiq ya karasa maganar da kyar

"Eh mana,dawa kake tunani da?ai kasan dai deen zulaikha ze aura,,,mom tai maganar fuskarta cike da damuwa,da kyar ya mike zaune ya kalli mom yace mom zulaikha tana dauke da cutar H.I.V...ayi gaggawar fadawa deen kada ya kuskura ya kusanceta

"A firgice mom ta kalli sadiq tace me kake fadane haka?ko ka fara haukacewa ne?

"Mom ina nan cikin hayyacina,wlhy da gaske nake mom bamu da wani sauran lokaci me tsawo sanarwa deen shine abu mafi mahimmanci fiye da surutun nan

"Karya kakeyi sadiq,karya kakeyi sadiq wallahi bazan taba yarda da maganarkaba wannan wani sabon salon harkar yaudarar takace,,taya akai kasan zulaikha nada H.I.V?menene shedarka kuma ina kasan zulaikha?tambayoyi barkatai mom ke watsowa sadiq ba tare data samu koda amsa guda daya ba
"Sai da sadiq ya dauki lokaci me tsawo yana yiwa mom bayani kafin ta yarda dashi,ashe wannan shine dalilin da yasa hajiya saratu take ta gaggawar a daura auren deen da zulaikha cikin lokaci kankani?meyasa hajiya saratu zata min haka?ya zama dole yanzu,yanzun nan a warware auren deen da zulaikha

"Hannu tasa zata tura kofar ta shiga don tun dazu an fada mata mom tana asibiti wajen sadiq,sedai jin kalaman da mom take yasata saurin dauke hannunta daga jikin kofar ta zaro ido tace what?za'a warware auren deen da zulaikha meyasa?da gudu hajiya saratu ta koma mota ta fara driving cikin gaggawa tai parking ta fito direct dakin zulaikha ta fara bubbugawa....ita da sauran kawayen amaryane a dakin sunata shewa,,,,kallon zulaikha tai cikin rashin kuzari tace zonan zulaikha,hannunta taja suka shiga wani dakin suka kulle sannan ta kalli zulaikha cikin gaggawa tace meyake faruwane zulaikha?yanzun nan naje zan duba sadiq a asibiti naji mom din deen tana cewa ya zama dole a warware aurenki da deen yau dinnan?sannan naji sadiq shine yake fada mata maganganun amma bana iya jiyo maganarsa saboda a hankali muryar tasa take fita

"What?innalillahi momy asirina zai tonu....momy sadiq ne ya tona min asiri kenan?taya akayi ya sani momy?cikin rashin fahimta ta kalli zulaikha tace asirin me kuma?sai a lokacin zulaikha ta tuna da hatta mahaifiyarta batasan tana dauke da cutar H.I.V ba,saurin gyara lafazinta tayi sannan ta kalli hajiya saratu tace mom inajin akwai sharrin da sadiq ke kullamin a gurin mom....ya zama dole na dauki mataki

"Sharri kuma zulaikha?sharrin me?ta tambayeta a rikice,mikewa tsaye tai ta kalli hajiya saratu tace momy bamu da sauran wani lokaci me tsaho nasan yanzu duk inda mom take tana hanya don bata wannan taron zatazo tace an fasa wannan bikin,don haka yanzu zansa a dauketa baza a saketaba har sena tare a gidan mijina,shi kuma sadiq zansa doctor yaci gaba da dura masa allurar bacci daga nan zuwa sati daya,zanyi amfani da wannan damar na sace wayar deen don kada suyi wani communicating da mom ko sadiq din ....kinga momy idan nai haka za'ayi komai cikin nasara

"Cikin mamaki da farin ciki hajiya saratu ke kallon yarinyar tata cike da soyayya,ajiyar zuciya tai tace ina alfahari dake zulaikha tun kina karama kike da zuciya me tsananin zafi da kaifi,,maza kije ki aiwatar da aikinki ina miki kyakkyawan zaton nasara domin ni kaina jinina ze iya hawa idan yata bata samu shiga cikin family alhaji modibbo ba amma fa kibi a hankali,,,karki damu mom indai ni zulaikha ce ina da yaran da zasu yimin dukkanin wannan ayyukan
"Sai data fara Kiran doctor me kula da sadiq suka gama magana zata tura mishi 3 million idan har ya aikata abinda takeson yayi mata,sannan ta tura yaran da zasu tare mom a hanyarta ta dawowa gida su dauketa su gudu da ita,,,,,text ne ya shigo wayarta da sauri ta duba deen ne ya turo text din yana fada mata koda zata nemeshi wayarsa ba charge yana sport field yana yin charge a mota

"A kan mota zulaikha ta hadu da deen hannunsa dauke da little junior,murmushi tai duk da faduwar da gabanta keyi,hey baby tace a takaice shima ya mayar mata da wani killer smile yace hey princess,turo baki tai kamar zatayi kuka tace baby wai meyasa wutar gidan nan ya dauke gaba daya?nifa wayana babu charge kuma inaso nayi magana da aunty yana sun taho suna hanya daga meduguri kuma wayana ya dauke gaba daya.....shitt ya fada sannan ya kalleta yace wlhy princess i don't know what's happening,dazu wutan ya dauke gaba daya kuma an tayar da gen shima still wutar bezoba ance gaba daya wiring din gidan ne ya samu matsala but wannan ba wani matsala bane ki shiga mota kisa charge seki kira aunty yana din....murmushi zulaikha tai don tasan kwanan zancen saboda itace tasa akai disconnecting wutar gidan gaba daya saboda deen ya fito mota yasa charge ta samu damar dauke mishi waya

"Tana shiga motar ta dauke wayar tashi ta saka a jakarta sannan ta dan bata lokaci kadan ta fito

"Direct asibiti ya wuce gurin sadiq sedai abin mamaki babu kowa gurin sadiq yana kwance shi kadai,tausayin sadiq neya kamashi a fusace ya kalli doctor yace doctor wai menene yake damun sadiq ne har yanzu ya kasa farfadowa?
"Gyara tsayuwarsa yayi sannan yace we are sorry sir,,kasan yana suffering pains ne jikinsa kuma ya shiga comma ne,dama na fada muku ze dauki lokaci me tsawo kafin ya farfado infact ze iya kaiwa 1 week nan gaba a haka,,,shut up doctor what a fucking nonsense are you telling me?dazu munyi magana da mom tace min sadiq ya farfado amma meyasa kuma zakace mun tunda aka kawoshi a haka yake be farfadoba?gaban doctor neya fadi a zuciyarsa yace karfa zulaikha ta jawo masa matsala garin son kudi ya rasa aikinsa,,,,cikin i'ina yace sorry sir eh tabbas dazu ya farfado amma be wuce 2 minutes ba ya sake komawa yanda yake

"Shiru deen yai bece komaiba ya fara laluben fito da waya don Kiran mom amma be gantaba,mota ya koma yaci gaba da dubawa amma sam ya kasa ganinta,,,,gida ya koma ganin har 4pm yayi tsaki yai yace mom yawonki yayi yawa yauma da ake bikin danki guda 1 amma kin kasa zama a gida ohh shitt!!!

"Hajiya saratu ce taci gaba da aiwatar da duk wata harkar bikin duk wanda ya tambayeta ina mom din deen setace ta fita amma zata dawo anjima,,tuni hajiya saratu ta sake cika gida da masu daukar amarya ana jira karfe 6 yayi akai amarya zulaikha gidan angonta deen......

"Da sauri zulaikha ta mike hannunta rike da wayar deen tana duba saqo tace what?nabeelah dama kece kike kokarin budemin asirina dana rufe?beelah dama ke kika sanarwa sadiq ina dauke da cutar H.I.V....hawayene ya gangaro daga idon zulaikha ta goge sannan tai murmushi tace beelah kinyi gangancin kutsa kanki shiga cikin rayuwata ya zama dole nai gaggawar kawar dake daga duniyar gaba daya domin idan kina nan bazaki taba barina na zauna da dan'uwankiba

"Knocking door din dakin ta fara yi a hankali,da kyar ta mike daga kwanciyar duk da zazzabin dake damunta ta bude kofar ta kalli zulaikha cikin ladabi tace sannu aunty,murmushi zulaikha ta mayar mata tace yawwa nabeelah dama nazo ki rakani gidan wata aunty dinane please zan karbo lafaya din da zanyi amfani da ita anjima karki damu yanzun nan zamuje mu dawo banason ina yawo ni kadaine ta karasa maganar tana kallonta,,,murmushi nabeelah tai tace ok aunty bari na tambayo aunty a'i sai mu tafi

"Saurin kallin beelah zulaikha tayi tace haba sister don kawai zamuje yanzu mu dawo se kin fadawa aunty a'i....aiseta zata ma wani nisa zamuyi kinga yi sauri ki dauko mayafinki mu tafi,okay kawai beelah tace ta dauko mayafinta duk da tsananin ciwon da kanta keyi

"Bakin wani katafaren duplex sukayi parking suka shiga,a tsorace beelah ke bin zulaikha ganin girman gidan sedai shiru babu alamar mutane a cikinsa.....a babban parlour suka zauna basu wuce 2 minutes zaune ba wani saurayi ya fito hannunsa dauke da wuqa,cikin aljihunsa kuma bindigogine guda 2....a razane beelah ta mike ta fara fadin innalillahi wa'inna ilaihir raj'un

"Murmushi zulaikha tayi sannan itama ta mike zaune ta kalli saurayin tace sojeeeyy wannan itace yarinyar inaso kayi mata kisan wulakanci,kisan da ko taje lahira bazata manta da azabarsaba,,,,,nabeelah kinyi gaggawar shiga rayuwata ni zulaikha,ba'a gangancin raba zulaikha da duk wani abunda takeso amma ke kinyiwa kanki gadar zaren yin haka

"Tuni hawaye suka wankewa nabeelah fuska ta zube a kasa tana basu hakuri,,,a fusace zulaikha ta kalli sojeeyy tace what are you waiting for?wuqar dake hannunsa ya cakawa nabeelah tai wata razananniyar kara sannan yasa kafarsa ya taka cikin nata,,,,,bushewa yai da dariya yace hajiya na cika aiki yanzun nan zata sheqa lahira zuwa dare zan kaita babban teku in jefar

"Murmushi tai ta cilla mishi rapper na dollars tace good job sojeeyy ni zan koma kasan yau ake bikina dukkan jama'ar gidan idonsu na kaina,bata sake cewa komaiba ta juya ta fita zuciyarta fes babu alamar regret...

"Gabantane ya fadi har tana cin tuntube ganin motar deen a bayan motarta,shi kuma ya harde hannunsa a jikin motarta yana jiranta,,,,,cikin karfin hali ta karasa kusa dashi muryarta na sarkewa tace babyyy

"What are you doing here?ya fada cike da mamaki

"Oh oh baby ina ganin mu bar wajen nan,dama motata ce ta samu matsala toh cikin gidan nan akwai wani me gyaran mota shine na shiga na kirashi kuma ban sameshi bama,sai a lokacin deen ya dan samu nutsuwa kadan yace amma meyasa zaki shiga guri ke kadai ba tare da abokin tafiyaba karki manta yanzu fa ke matar aurece

"Murmushi tai tace i'm so sorry baby i won't try it again,a tare suka shiga motar deen suka fara tafiya gaban zulaikha naci gaba da faduwa,gefen mayafinta ya kalla cikin mamaki yace blood?Princess meya hada jikinki da jini?

Voting da comments dinku sam-sam baya gamsardani,wallahi tallahi zan dena rubutun nan i am upset😈😈

DeenWhere stories live. Discover now