Chapter 32

3.1K 292 37
                                    

"A jail nabeelah tayi parking sannan ta nuna musu ID card dinta ta wuce ba tare da sunce mata komai ba,zaune yake jikinsa duk jini anji masa ciwo da duka ya rame yayi duhu kadan....tsugunnawa tayi gabansa cikin tausayi ta zuba mishi ido tana kallo,shima kallon nata yakeyi,,,,idonta na shirin zubar da hawaye tai saurin bude jakarta ta mika mishi bottle din ruwa,da sauri ya mika hannu zai karba sai dai ganin wani babban ciwo a hannun sadik yasa nabeelah saurin janye bottle din ruwan ta mayar saitin bakinsa....murmushi yayi yace thank you sannan ya bude bakinsa ta fara bashi ruwan cike da kulawa da tausayi

"Tissue ta dauko taci gaba da goge mishi jinin da ya bata masa jiki tana hawaye....mamakin nabeelah sosai sadiq yakeyi tambayar daya kasa furtawa a zahiri itace meyasa nabeelah take kuka?meyasa nabeelah ta damu da damuwarsa?itama a nata bangaren tambayar da takeyi kenan....share hawayen da yake zuba a idonta tayi sannan ta tashi ta fita....jiyo sautin ihun sadiq yasa nabeelah saurin juyowa taga yanda akaci gaba da dukansa....da gudu ta fito daga mota ta karasa gurin cikin tsiwa tace heyyy you what are you fucking doing?wannan hukuncin da kukeyi masa dai-dai yake dana wanda yayi kisan kai yake jiran makomarsa kuma dai-dai yake dana yan ta'adda...kunyi haukane?

"Sunkuyar da kansu kasa sukayi sukace sorry maam...umarni ne aka bamu muyi masa haka shiyasa

"Idan sakarai kuma dakikin wanda ya baku umarnin besan me yakeyi ba hakan yana nufin  kuma bakusan aikin kuba

"Da sauri daya daga cikin police officers din ya dago ya kalleta yace point of correction maam sir deen ne ya bamu wannan umarnin you have to....

"Don't you dare tell me what to do,i am on my right way ta karasa maganar tana pointing dinsa da yatsa

"Sunkuyar da kansa kasa yayi yana sake cewa ok maam...ok maam

"Tsaki tai ta shiga mota zuciyarta na bugawa da sauri-sauri ta nufi office dinta

"What?when and how?kuna nufin kwata-kwata ba'aga sadiq dinba?what are you fucking  saying?taya akai har ya gudu baku saniba?deen ne tsaye yake faman yin tambayoyi ba tare da kowa ya bashi amsa ba illa sunkuyar da kawunansu da sukai kasa.....tsaki yayi sannan ya sake cewa look na baku nan da 24 hours a nemo sadiq duk inda ya shiga a duniyar nan

"Ok sir,ok sir gaba daya suka fada sannan suka fita daga office din...buga kansa yayi akan table yace oh my god....saurin dauke kansa yayi jin ya fama ciwon da beelah taji mishi da kwalba yayi sannan ya tashi ya shiga mota ya wuce mansion dinsa duk da gaisuwar da staffs dinsa ke mishi amma ko kallo basu isheshiba

"Cikin fushi yake cire suit din jikinsa ya shiga bathroom ya dade a bathtub yana tunani...wayarsane ya fara ringing a hankali ya goge kumfar hannunsa da tissue din dake gefe sannan ya dauka muryarsa a hade yace hey mom....okay mom kawai ya fada sannan ya kashe wayar

"Tsaki yayi sannan ya dauraye jikinsa ya fito daga bathtub ya wuce bedroom,cool lotion ya shafawa jikinsa ya taje gashinsa da comb sannan yai styling hair dinsa da styling gel...ya dauko ash shirt da white jeansy trouser ya saka ya feshe jikinsa da perfume ya dauki key din range rover ya fita....a gidansu yayi parking ya karasa cikin gidan jikinsa sam babu dadi,zaune ya tarar da mom zaune a palour tayi tagumi jikinta a sanyaye....shima zaman yayi kusa da mom yace mom are you okay?meya faruwa haka?

"Ajiyar zuciya tayi tace dama kiranka nayi na fada maka....dakatawa tai da magana tace deen meya sameka naga bandage a kanka?murmushi yayi ya shafa gurin yace oh mom dama na dan samu home accident but i will be okay soon...ajiyar zuciya ta sakeyi tace batul fa yau kwananta 2 bata ci komaiba sai ruwa kawai da take sha,bata da wani aiki sai kuka yarinya duk tabi ta fita a hayyacinta....nina rasa wannan wacce irin masifa ce take faruwa damu haka?kasan da cewar duk wasu maneman batul da aure yanzu babu kowa tunda abinnan ya faru babu wani namiji da ya sake zuwa gidannan cewar yana sallama da batul da niyyar yana sonta...dazu ma mall muka shiga munje shopping amma baka ga yanda ake nuna batul ba ana zaginta suna cewa ga wannan wacce tayi cikin shegen,batul tana cikin matsananciyar damuwa deen domin doctor yace idan batul taci gaba dasa damuwa a ranta zasu iya rasa ransu ita da abinda ke cikinta

DeenWhere stories live. Discover now