BA SON TA NAKE BA | ✔

By fadeelarh1

326K 25.5K 2.4K

"BA SONTA NAKE BA" Shin dagaske ba sonta yake ba? Shin ita din son shi take?? More

PROLOGUE
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
EPILOGUE

Chapter 38

6.3K 510 53
By fadeelarh1

Al-Hasan ibn Ali reported: The Messenger of Allah, peace and blessings be upon him, said:
"Leave what makes you doubt for what does not make you doubt. Verily, truth brings peace of mind and falsehood sows doubt"
Source: Sunan al-Tirmidhī

************

FAROUQ AL-HUSSAIN RESIDENCE
(GIDAN ZARA)

Kwance take a kan gadonta tana ta kuka.

A rayuwar Zara babu abinda ta tsana irin fushin Farouq.. Mugun tashin hankali take shiga.

Tabbas tayi nadamar abinda tayi domin kuwa ta gane cewa babban kuskure tayi. A matsayinta na matar aure bai kamata ta fita ganin wani ba tare da mijinta ya sani ba.. toh amma ai ba zuwa zata yi ta ga Mahmood don tana son shi ba har yanzu, she was only going to end everything between them. she wanted to explain this to Farouq but he refused to listen to her! why would he when tayi mishi laifi???

"Zara you are a fool, shouldn't you have just ended things with him on phone??? yanzu ga abinda na janyo ma kaina" ta fada cikin kuka.

Gaba daya ta rasa yadda akayi tunaninta ya gushe da har tayi wannan wautar... haka ta cigaba da zagin kanta tana kuka.

Tana nan kwance tana ta kuka ne cikinta ya fara yi mata ciwo... tun tana ta jurewa har dai abu ya fara fin qarfinta...

Haka ta dinga juye-juye a kan gado.

Zara dai ta sani sarai al’adarta ce ta zo..

Ni kuwa nace wrong timing!!

Da qyar ta lallaba ta shiga bathroom tayi wanka sannan ta kimtsa kanta.

Drawers din dakinta ta shiga budewa tana neman maganinta amma babu. Daga baya ne ta tuna cewa ya qare and she forgot to get it.

Jiki a sanyaye ta koma can gefe bisa tiles din dakin hoping zata ji sanyi...

Zara dai haka ta cigaba da juyi a qasa. Aikuwa bata taba jin zafin da take ji yau ba.. its definately because she is worried akan fushin da Farouq yayi da ita.

Wuraren qarfe daya na dare ne da ta kasa jurewa ta miqe jiki a sanyaye ta fita don neman taimako a wurin Farouq.

A daddafe ta qaraso dakin shi ta bude qofar sannan ta shiga.

Kwance yake a kan gadon shi, idanuwan shi a rufe amma ba bacci yake yi ba. Ya ji shigowarta  amma bai motsa ba balle ya bude idanuwan shi.

Zara wadda tayi zaton yana bacci kuwa sai ta kasa tayar da shi.

Gani nayi ta kwanta a qasa yayinda ta cigaba da juyi.

Farouq dai yana jinta amma yayi watsi da ita... Sossai ta bata mishi rai a yau. Just when he thought things will get better between them... why does she have to invite the guy to his house??? atleast ai ko bata girmama shi ba yakamata ta girmama matsayinta na matar aure. Is she this crazy????

Zara dai ta kasa jurewa at this point don haka ne ta tashi ta nufi gefen gadon shi tace “Ya Farouq”

No response!

Fashewa tayi da kuka ta dan taba shi tare da fadin “Ya Farouq please help me, cikina”

Jin tana kuka ne ya dan bude idanuwan shi yace “meye?”

Cikin kuka tace “cikina ke ciwo kuma na duba magani na ya qare, please help me” 

Shiru ya dan yi sannan yace “come here”

A rude tace “na’am”

Daga nan kuwa shiru yayi bai sake yi mata Magana ba.

Ganin yayi watsi da al'amarinta ne na ga ta saki ajiyar zuciya yayinda ta matsa ta hau gadon. Gaba daya jikinta rawa yake yi because she was confused about what he asked her to do.. how is 'coming to him' going to solve her problem???

Hannuwan shi yasa ya janyo ta ya manna ta a jikin shi... Hakan sai da ya sa gaban ta ya fadi yayinda jikinta ke rawa kamar mazari.

what is he doing???

Zara wadda ta kasa controlling kanta ce tayi saurin janyewa daga gareshi tare da matsawa a bit far from him... She was seriously shaking.

Qara janyota yayi jikinshi yace “idan bazaki natsu ba tashi ki bani wuri”

Aikuwa nan da nan ta natsu yayinda hawaye ke ta bin fuskarta.

Bata ankara ba ta ji ya zura hannuwan shi a ta cikin rigarta ya fara massaging cikinta zuwa lower abdomen dinta gently... Runtse idanuwa tayi a dalilin wani mugun shock da ta ji.

Ji nayi ta saki numfashi yayinda wani sanyi ya fara ratsa ta... Nan da nan ta ji sauqi ya fara samuwa a gareta!

Mai karatu ko minti goma sha biyar ba'a yi ba bacci ya kwashe Zara... there is no doubt ta samu relief sossai.

Shima kuwa Farouq bai san lokacin da baccin ya kwashe shi ba.

Cikin dare ne Zara ta farka... abinda ya faru ta tuno!

Da sauri ta juyo tana fuskantar Farouq wanda yake bacci.

Gani nayi tana ta kallon shi yayinda take murmushi.

Kiss tayi mishi a kumatu tare da fadin “thank you big brother... your hands did a wonderful magic”

Ba tare da tunanin komai ba kuma sai na ga ta manne a jikinshi ta rufe idanuwanta.

***********

Da asuba ana Kiran Sallah ne Farouq ya bude idanuwan shi. Zara ce maqale a jikin shi kamar mage yayinda take ta baccin ta.

Girgiza kai yayi sannan ya zare jikin shi daga nata a hankali ya sauka ya gyara mata Duvet da suka rufa da shi sannan ya wuce bathroom dinshi.

Alwala yayi ya fito sannan ya wuce masallaci.

Ko da ya dawo daga masallaci Gym dinshi ya wuce ya dan yi working out har zuwa qarfe bakwai sannan ya koma dakinshi don yin wanka.

Har a wannan lokacin kuwa Zara bacci take yi sossai (kar ku manta she didnt really get enough sleep through the night)

Bayan Farouq ya fito ya gama shirin shi ne ya fita abinshi domin kuwa dama akwai surgery din da zai yi da safen nan.

Zara dai bata farka ba sai wuraren qarfe goma na safe. Juyawa tayi ta ga babu Farouq, da sauri ta tashi zaune tare da murza idanuwanta.

Agogo ta kalla ta ga qarfe goma da minti goma. Gani nayi ta zaro idanuwa tace "what??!!"

Da sauri ta sauka daga kan gadon tare da yaye Duvet tana kallon spot din da ta kwanta.

Ji nayi tace “spotless... thank God”

Dakinta ta wuce don yin wanka.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

CALEDONIAN SUITES
MAITAMA ABUJA

Kwance suke a bisa gadon daya daga cikin dakunan Hotel din kamar kullum.

Musty ne yace “wai ina Farouq dinki ne, yaushe yakamata in je mu gaisa kamar yadda ya buqata?”

Ruqaya ce ta tashi zaune cikin bacin rai tace “what? Ai wallahi bazaka je ba, ka kuwa san zai iya gano wani abu a duk lokacin da kuka hadu? He is very smart fa”

Fashewa yayi da dariya yace “toh ma banda rigima irin nashi yanzu da ya qara aure ai ya kamata ya baki space kema”

Hararar shi tayi tace “ni na fadi maka ina son space?”

Yana ta kwasar dariya yace “gashi nan kuwa kin samu har kin waiwaye ni”

Ruqayya ta girgiza kai ba tare da tace komai ba.

Janyo ta yayi yace “I really love you Ruky, wani lokacin ma ji nake yi kamar in kauda Farouq din naki don in same ki all to myself”

Da sauri ta ture shi tace “don’t try anything with Farouq, I am warning you”

“sorry love, I won’t as long as zamu cigaba da haduwa”

Daga nan ne ya canza hirar.

“wai dagaske kike yi Junior ba yaro na bane?”

Ruqayya dai wannan karon sauka tayi daga kan gadon zata shiga bathroom tace “ai kuma sai kayi”

Daga nan ta shige yayinda Musty yake ta dariya.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION
(GIDAN ZARA)

Zara ce kwance a kan gadon dakinta cikin Duvet yayinda take tunanin special hanyar da zata bi don ba Farouq haquri.

A yanzu dai zuciyar Zara gaba daya ta karkata zuwa ga yayan nata.. Tabbas tun tana qarama take bala'in son shi, he has always been an important person in her life... Up until yesterday before they kissed, she has always seen him as that big brother whom she cares about so much. But after the kiss, komai ya canza... Farouq ya canza ma kanshi matsayi a cikin zuciyarta. Wani abu take ji a game da shi wanda ko rabin shi bata ji ba game da Mahmood din da take ikirarin tana so. the truth is she doesnt want to leave this house, she doesn't want to leave Farouq.. She wants to be stuck with him for life..

A yanzu mamaki take yi na yadda ta dage akan bata so ta aure shi lokacin da iyayen su suka dauko zancen... Kenan da sun biye Mata haka zatayi losing being with a great guy like him???

This surely means one thing, she has fallen in love with him...

"have I??" na ji ta tambayi kanta.

Wayar ta ce tayi ringing.

Hafsat ce!

Da sauri tayi answering tace “bestie dama yanzu nake shirin kiran ki, I really need to talk to someone”

“aikuwa nima wani labari nake so in baki da dumi dumi but it can wait, how far”

Ajiyar zuciya Zara saki tace “I think I have fallen deeply in love with him bestie”

Cikin rashin fahimta Hafsat tace “ban gane ba babes, who are you talking about??”

“Ya Farouq, I just realised I can’t live without him”

Hafsat ta ja tsaki sannan tace “say something I don’t know babes, ai ba wanda bai san wannan ba..”

“you don’t understand bestie, there is something you dont know”

“then tell me”

Daga nan fa Zara ta bata labarin plan din da suka yi na rabuwa da juna bayan wata daya da yin auren su.

Hafsat kuwa me zata yi banda dariya.

Cikin dariya ne tace “toh wai ke dama a tunanin ki Ya Farouq dagaske yake zai rabu da ke?”

“ai ba sona yake ba…”

Hafsat ta katse ta tare da fadin “Hajiya, Ya Farouq loves you a lot, dama kin natsu kin bude mishi zuciyarki, kin dai san kina da competition ko?”

(Ni kuwa nace ah toh.. remind her dai Hafsat)

Ajiyar zuciya Zara ta saki sannan tace “I am not sure about that bestie amma ko ma menene ni ina son shi kuma bazan bari mu rabu ba... Yanzu the problem is nayi mishi laifi jiya kuma yayi fushi da ni...”

"huh bestie, wallahi ba kya jin magana. Me kika yi mishi this time??”

Anan ta bata labarin abinda ya faru lokacin da Mahmood ya zo....

Hafsat tace “gaskiya babes kinyi mistake, what were you thinking da har zakiyi inviting dinshi???"

"Wallahi bestie i just wanted to end things ne with him shiyasa na...."

"Well dama a dalilin Mahmood din na kira ki, even if you didn't plan on ending things yesterday you will do it after this"

"Babe tell me... what happened???"

"not 'what happened?' but 'what did he do?'..... ki shiga Instagram ki ga labarin da yake ta circulating regarding him. Just get back to me idan kin gama kallo”

Zara kuwa bata tsaya jiran komai ba ta kashe wayar tare da tashi zaune ta shiga Instagram and few minutes later sai na ga ta zaro idanuwa tare da fadin “Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un, na shiga uku. Dama haka Mahmood yake?? Allah ya isa tsakani na da shi”

Ni kuwa da na leqa wayar sai na hango Hoton Mahmood tare da wasu karuwan ‘yan mata a hotel yayinda ake sanarwar daya ta mutu saboda mugayen qwayoyi da suka yi mata yawa wanda a yanzu haka an kama Mahmood tare da sauran ‘yan matan ana tuhumar su.

Da sauri Zara tayi dialing tace “bestie wallahi na gani, dama haka Mahmood yake ban sani ba?”

Hafsat tana dariya tace “Jiya da daddare aka kama su, ai dama na fadi miki tun farko bana son Mahmood, wallahi tun ranar da na fara ganin shi ban yarda da shi ba”

A lokacin da take magana da qawarta a waya ne Farouq ya shigo gidan. Kai tsaye dakin Zara ya nufa to check on her. the truth is bazai iya zama ba for long yana fushi da ita... he loves her so much that he can never stay mad at her no matter the kind of laifi da zata yi mishi.

Zara ta riga tayi mishi mugun kamun da yake tunanin ko wanne irin laifi tayi mishi zai iya yafe mata.

Yana daf da shiga ne ya jiyo muryarta tana fadin “wallahi bestie kwata kwata ko ganin shi bana son yi, a yanzu haka na tsani kaina wallahi. Bana son shi ko alama, I hate him with every fibre of my being....”

(Oh my... oh my... Not again)

Gani nayi Farouq ya dafe qirjin shi tare da runtse idanuwan shi, komawa yayi da baya cikin tashin hankali yayinda kalaman Zara suke ta amsa kowa a qwalwar shi.

A rude ya qaraso falon shi ya zauna a kan kujera dafe da kanshi.

Idanuwanshi ne suka yi jajawur yayinda na ji yana fadin “does she hate me this much? Subhanalillah, me nayi ma yarinyar nan haka ne da zata fadi irin wadannan kalaman?”

Zuciyar shi ce take ta radadi yayinda jikinshi yayi sanyi gaba daya.

He was seated there confusedly for over two hours without knowing what to do... All possible solutions to his problem popped up in his head but he didn't even know which one to take.

Gani nayi ya ja numfashi sannan ya ciro wayar shi daga aljihun shi yayi dialling lambar Dr. Schurle.

“Hello colleaque, I have decided to join the team, I will be in Germany the soonest Insha Allah”

Bayan sun gama magana ne na ga ya kashe wayar sannan ya miqe ya nufi dakinshi ya hada akwatin shi sannan ya fita daga gidan.

toh fa... what a solution he picked!

**********

Zara dai ta dade tana hira da qawarta a waya da.. Mahmood kuwa ya sha zagi yayinda Hafsat ta dinga kwasar dariya.

Bayan sunyi sallama ta sauka daga kan gadon ta shiga dressing room dinta... Tana shirin shiga wanka ne na ji tace "Zan ba Ya Farouq haquri sannan in fadi mishi cewar ina sonshi... zan kuma roqe shi akan ko baya sona yayi haquri ya zauna da ni because I swear I cant live without him"

hahahahahaha...

After a while!

Bayan ta fito daga wanka ta kimtsa kanta ne ta ji wayarta tayi qara alamar an turo mata text message.

Ko da ta duba sunnan Farouq ta gani, tana murmushi ta bude saqon da sauri ta ga rubutu kamar haka:

"I am on my way to Germany right now, I have an emergency case to attend to. Take care."

"what???" ta fada da qarfi yayinda ta zaro idanuwa.

Gani nayi ta saki wayar tare da dafe qirjinta wanda yake bugawa babu sassauci.

Hawaye ne na ga sun fara wanke mata fuska yayinda take fadin “Inna lillahi wa'inna ilaihir raji'un... yau na shiga uku, ya tafi ya barni”

Gani nayi ta zame qasa sannan ta fashe da kuka sossai.

Kamar wadda aka yi ma shocking sai gani nayi ta zabura tare da janyo wayarta. Lambar shi tayi dailing amma switched off, haka ta dinga kira bata samu. Jefar da wayar tayi ta cigaba da kuka.

"Ya Farouq why would you leave me now?? Na shiga uku ya zanyi??"

(Ni kuwa ina daga gefe nayi tagumi..🤔)

**********

Zara dai daren yau baccin kirki bata yi ba. Ta sani sarai Farouq ya tafi yana jin haushin ta, a duniya babu abinda yake tayar mata da hankali irin fushin Farouq... she really wanted to apologise and tell him how she feels about him but she cant because he is unreachable!

Aikuwa kafin gari ya waye ta fita hayyacinta. Nan da nan wani zazzabi mai zafi ya rufe ta.

**********

Oh my God, why does Farouq have to always appear at the wrong time??😡

Well, thank God mun rabu da Mahmood... Yeeeeey💃 (one down.. one to go 👉 madam Ruks)

Toh fa, Wane hali Zara zata shiga? Ga Farouq yayi nisa... Shin zai dawo ko kuwa??? Germany is far oo🤔

What will happen next??

Kindly change the colour of the star below👇 and lets hope our Romeo comes back to his Juliet🤣

One love❤
Fadeelarh1

Continue Reading

You'll Also Like

485K 41.1K 33
ရိုးရိုးအချစ်ဇာတ်လမ်းလေးတစ်ပုဒ်ပါပဲ
127K 15.2K 32
[Zawgyi+Unicode] ငါဟာ မင္းသမီးတစ္ပါး... တိတိက်က်ေျပာရရင္ ငါဟာ အရူးမင္းသမီး... ေရႊနန္းေတာ္ႀကီးထဲမွာ ေမြးဖြားလာတယ္ဆိုေပမယ့္ ငါ့ရုပ္ငါ့ရည္ဟာ သာမန္ရြက္ၾ...
317K 15.3K 84
🍁ကောင်းခြင်းတည်မြဲ.. 🍁 နိုင်ငံခြားပြန်ကောင်လေး။ ရုပ်ရည်၊ ပညာ၊ စည်းစိမ်ဥစ္စာပြည့်စုံကြွယ်ဝသူမို့ အတော်လေးကြီးကျယ်သည့်လူ။ သူ့ကိုသူလည်း အထင်ကြီးလွန်းပ...
187K 18.1K 54
Ta tafka babban kuskure a rayuwarta... Shin zata iya gyara wannan kuskuren ko kuwa??