BA SON TA NAKE BA | ✔

By fadeelarh1

331K 25.7K 2.4K

"BA SONTA NAKE BA" Shin dagaske ba sonta yake ba? Shin ita din son shi take?? More

PROLOGUE
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
EPILOGUE

Chapter 36

6.7K 482 58
By fadeelarh1

Zaid ibn Aslam reported: Umar ibn Al-Khattab, may Allah be pleased with him, said:
"Let not your love be infatuation and let not your hatred be destruction"

It was said, “How is this?” Umar said:
"When you love someone, you become infatuated like a child. When you hate someone, you love destruction for your companion"

Source: Al-Adab Al-Mufrad

**************

FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION
(GIDAN ZARA)

Tsaye take a bathroom din shi tana ta wankewa.

Zara dai tayi more than one hour tana abu daya. Ni da nake kallonta har na gaji, at a point ma I started praying for her kar ta zame ta fadi domin kuwa yadda take yin aikin da gani zaka fahimci lallai ba ta saba yin shi ba.

Farouq ne ya shigo dakinshi rataye da towel a wuyan shi.

Daga Gym ya fito.

Wandon three quarter ne kawai a jikin shi...

Kai tsaye bathroom din ya wuce don yin wanka.

Yana daf da shiga ne ya ji motsi and he paused a bit yayinda yake wondering who is inside.

The one possible person would be Zara amma kuma he is sure ba ita bace... what will she be doing in his bathroom??? he could remember lokacin da ya fito zai shiga Gym din ya leqa dakinta ya ganta kwance tana bacci.

Dukda yayi almost 2 hours a gym din, he is 100% certain ba ita bace domin a yadda ya san Zara da son bacci, lokacin tashin ta bai yi ba!

He needs to find out who is inside... he thought!

Yana bude qofar na ga ya zaro idanuwa yayinda ta juyo a tsorace tare da sakin bowl din da ke hannunta... Gaba daya ruwan da ke cikin bowl din ya zube a qasa.

Sanye take cikin kayan bacci na wandon three quarter da wata ‘yar qaramar T-shirt. Ta kama gashin ta a tsakiyar kanta... she looked beautiful dukda bata dade da tashi daga bacci ba!

Zara dai tunda ta juyo ta ga Farouq tsaye babu riga a jikinshi ne ta rude. Jikinta sai rawa yake yayinda ta kasa magana....

A bangaren shi kuwa ya cika da mamaki sossai on seeing her... me take yi???

Tsautsayi ya sa idanuwan Zara suka sauka akan six pack abs dinshi yayinda zuciyarta ta buga da qarfin gaske... 

It's not the first time da take ganin abs din Farouq..

On previous occasions, she sees it from afar... She has never seen it this close. Idanuwanta ta rufe da sauri tare da fadin “n-nn-na shiga Uku, Ya Farouq..”

Tana qoqarin daga qafarta zata gudu ta bar bathroom din ruwan da ta zubar ya zamar da ita...

Aikuwa ihun da tayi ne ya sa na toshe kunnuwa na yayinda na ga Farouq ya fashe da dariya..

like seriously???

Zara zaune dirshan a qasa tana kuka ce take kallon shi cike da mamaki.

“Ya Farouq dariya kake yi mun???"

Da sauri ya matse tare da girgiza kan shi alamar 'No'

Gani nayi tana yunqurin tashi amma ta kasa and Farouq was still standing there admiring how cute she looked while crying...

"Please Ya Farouq ka zo ka taimake ni, na karye....”

Jin statement dinta ne na ga hankalinshi ya tashi matuqa... Kenan its serious sabanin what he thought!

Da sauri ya qarasa wurinta ya duqa tare da daukarta yana fadin "hey sorry.. is it that serious???"

Tana maqale da shi cikin shagwaba tana kuka tace "very serious Yaaya.."

"Mu je asibiti.."

"No" ta fada da sauri yayinda ta cigaba da fadin "bai kai a je asibiti ba Yaaya.."

Farouq wanda yayi murmushi ya gane cewar it's not serious... from the way she slipped he could swear zata iya tashi lafiya but with Zara being Zara, he already knows what to expect!

Ko da ya fito riqe da ita gani nayi ya nufi gadon shi ya kwantar da ita ahankali yayinda ya zauna a gefenta yace “toh wai ya haka? what were you doing in my bathroom???"

"I was cleaning it"

"and you slipped and fell just like that???”

Hararar shi tayi tace “ba kai bane ka tsorata ni?”

“Ni kuma Baby Angel?? am I a ghost that you will get scared like that???”

"toh wa yace ka shigo bathroom din???"

Cike da mamaki Farouq yace "ban gane ba... the last time I checked, this is my room ai..." gani nayi ya sauka daga kan gadon sannan yace "...let's leave this for now, bari in dauko first aid kit"

Zara tana kallon shi ya koma bathroom din...

A lokacin da ya fito gani nayi ta qura mishi idanuwa... she was actually staring at his abs. A lokacin da ya qaraso daf da ita kuwa sai na ga ta kauda kai da sauri yayinda zuciyarta take ta bugawa...

Tana jin shi ya zauna a kan gadon sannan yace “ina ke miki ciwo?”

Butt dinta ta nuna mishi...

“gyara toh in shafa miki” ya fada kai tsaye.

"what??" ta fada a firgice yayinda ta tashi zaune with her eyes wide open tana kallon shi.

Confusedly yace “what? did I say something wrong?”

“Yes you did... ta ya zaka shafa mun magani a...." bata qarasa ba kuma tace "....hey, you are not suppose to see, ni ka bar shi ma ya daina ciwo”

Farouq dai fashewa yayi da dariya sannan yace “toh shikenan my Baby Angel.. tunda baki so in shafa miki...”

Gani nayi ya ajiye balm din a gefe yayinda yace "Na San bai daina yi miki ciwo ba so please try and apply it... Ni bari in je inyi wanka”

Zara dai daga mishi kai tayi ba tare da tace komai ba, haka bata kalle shi ba.

Bayan ya shiga bathroom dinshi kuwa ta shafa balm din sannan ta koma ta kwanta...

*******************

Zara tana nan kwance a kan gadon Farouq ne ya fito daga wanka.

Tana kallon shi ya nufi gaban Vanity mirror dinshi ya gama duk wani abinda zai yi sannan ya wuce dressing room dinshi.

After a while ya fito sanye cikin qananan kaya... Wandon Cinnox baqi da long sleeve shirt.

Gaban Vanity mirror ya koma ya feshe kanshi da turaruka sannan ya dawo wurin Zara wadda ta sa mishi idanuwa babu ko qyaftawa..

"Baby Angel irin wannan kallon da kike yi mun fa ban gane ba..."

Turo baki tayi ba tare da tace komai ba... toh me zata ce mishi bayan ita kanta bata gane irin kallon da take yi mishi ba!!

Hayewa yayi kan gadon ya kwanta a gefenta yace “ya ciwon? ya daina zafi???”

"eh, ya rage zafi..."

"toh Allah ya baki lafiya... I am sorry it's all my fault. Please forgive me"

Murmushi tayi sannan tace "it's okay Yaaya"

Gani nayi ya qara matsawa daf da ita yayinda yake shaqar qamshinta... Lumshe idanuwa yayi yace “I love your smell”

Itama lumshe idanuwan ta tayi a dalilin nashi qamshin da take shaqa... Qamshin da take masifar so!

"Yaaya ban yi wanka ba kake fadin haka..."

"sssshhhh, bazaki gane ba" ya fada tare da sakar mata kiss a kumatu sannan ya tashi zaune yana kallon ta.

Farouq dai a yanzu ya kula Zara tayi laushi gaba daya.. its definately because of the kiss he just gave her.

“zan je asibiti, are you going to be okay?”

Turo baki tayi sannan tace “yes, amma dai kar ka dade yaaya"

"I will try... You need something???"

"Yes please... take me to my room"

"Okay my Baby Angel" ya fada sannan ya dauke ta cak kamar 'yar baby.

******************

Bayan Farouq ya kwantar da ita a kan gadon dakinta ne ya rufe ta da Duvet sannan ya zauna a gefen ta yace “forget about cleaning my side, I will do it myself henceforth kinji?”

“but Ya Farouq kasan fa Mamy ta…”

Kumatun ta ya ja sannan yace “kar ki damu ni nace I will do it myself”

Murmushi tayi tace “thank you big brother”

“zan turo miki one of your maids to watch over you before I return, is it okay??” ya tambayeta yayinda ya sauka daga kan gadon.

“don’t worry Ya Farouq, Hafsat tace mun zata zo anjima”

“okay, as soon as I am done zan dawo, call me if you need anything”

"Okay Yaaya... take care"

"You too My Baby Angel"

Haka ta bi shi da idanuwa har ya fita.

Lumshe idanuwa tayi tare da sakin ajiyar zuciya...

Gani nayi ta bude idanuwa ta saki murmushi. Babu shakka she enjoyed everything that just happened. Aside zamewar da tayi, duk abinda ya faru tsakanin ta da Farouq was superb.

Babban burinta a rayuwa shine ta zama very close to him, she wants to be his favorite person, she wants him to care for her... that too, UNCONDITIONALLY. She is seeing alot of it and she is super happy.

Gani nayi ta janyo pillow ta rungume and in no time, bacci ya dauke ta.

************

After a while!

“toh gimbiya, tashi.. baccin ya isa haka”

Ahankali Zara ta bude idanuwanta ta ga Hafsat tsaye tana kallon ta.

Murmushi tayi tace “babes how far, ke da kika ce sai da rana zaki zo? zauna mana”

Hafsat wadda ta danna mata harara ta haye kan gadon tace "ka ji munafinci, you are asking me bayan kin hada baki da Ya Farouq akan lallai sweetlove ya amince in zo inyi jinyar ki?”

Zara ta tashi zaune cike da mamaki tace “laaa, yanzu Ya Farouq sai da..”

“shut up jor, me ke damun ki? Yace wai kin samu minor accident, ya akayi? ina ciwon?”

“uhmm... dama na zame ne a bathroom dinshi kuma ma duk laifin shi ne but i think i am okay”

Hafsat ta girgiza kai tace “Allah ya shirye ki bestie”

Zara ta fashe da dariya yayinda ta sauka daga kan gadon tace “bari inyi wanka in zo”

“je ki zo in baki wani albishir”

“Dagaske??? please tell me” Zara ta fada yayinda ta dawo ta zauna.

Come on, tashi ki je kiyi wanka. idan kin fito zan fadi miki... I'm here right??"

"Okay fine"

********************

Kamar kullum sai da ta dade a bathroom din sannan ta fito.

“mutum ka shiga wanka kayi awowi kamar zaka canza fata”

Zara tana dariya tace “bazaki gane bane bestie”

Bayan Zara ta gama shirinta ne ta dawo kan gadon tace “ina jin ki qawata, tell me”

"albishirinki"

"Goro"

"Fari ko baqi"

"Fari sol bestie... please tell me"

“kin kusa zama Aunty, I am pregnant”

"what???" Zara tayi ihu tare da rungume qawarta tace “wow, I am so happy for you, wallahi I cant wait to see my baby. Allah ya sani ina bala’in son yara”

Hafsat tana dariya tace “toh ai sai ki dage ki haifo kema since you have a husband abi???”

Turo baki tayi tace “ba dai anan gidan ba”

Cike da mamaki Hafsat tace “ban gane ba”

“uhm, manta da zancen bestie”

“in tayi tsami zamu ji”

************

Farouq bai dawo gidan ba sai wuraren qarfe tara na dare. Ko da ya shiga ya tarar da Zara kwance a kan kujera a falon qasa tana kallon tashar Zee TV.

Hankalinta yayi nisa a kallon da bata ji shigowar shi ba.

“hello My Baby Angel”

Da sauri ta juyo ta gan shi tsaye yana murmushi...

Cike da murna ta miqe ta nufi wurinshi da gudu ta rungume shi da qarfin gaske...

"whoa..." ya fada yayinda yayi wrapping hannuwanshi around her.

“Ya Farouq where have you been??? ka bar ni ina ta missing dinka” ta fada cikin shagwaba yayinda take ta squeezing dinshi a cikin hug din.

Farouq yana murmushi yace “sorry dear, wani emergency ne, besides ki daina missing dina dayawa...”

Da sauri tayi breaking hug din tana kallonshi confusedly.

“ban gane ba Ya Farouq”

Hannunta ya janyo suka zauna a kan kujera yayinda ta maqale a jikin shi kamar mage.

“kin san gobe zan koma gidan Ruqayya, na raba muku kwana bibbiyu..”

Tun kafin ya rufe baki ta miqe a rude yayinda zuciyarta take ta bugawa...

"hey....." ya fada looking worried and confused.

"Na Shiga uku ni Zara..."

Daga nan sai ta wuce da gudu ta bar falon yayinda Farouq ya tashi tsaye yana fadin "hey wait..."

(toh fa🙄)

Gani nayi ya shafa kai da hannuwanshi sannan yace “I didn’t see this coming”

************

Zara tana kwance a kan gadonta ne ya shigo dakin. it's been more than thirty minutes since she ran off.

Farouq dai a lokacin da ta bar falon, dakinshi ya wuce yayi wanka ya shirya and now he is here to pacify her dukda ya san it will be difficult..

Ko da ya qaraso wurin gadonta gani nayi ya tsaya cak looking super worried.

Kuka take yi... Now this will be more difficult than he thought!

Ajiyar zuciya ya saki sannan ya haye kan gadon ya matsa daf da ita ya share mata hawaye yace “hey beautiful, what is it?”

“I don’t want you to go”

“are you falling in love with me already?”

"wh-wha-what??? No, I mean.. I...."

Farouq ne ya fashe da dariya yayinda yace "hey calm down and tell me, meyasa baki so in tafi?"

“Nima ban sani ba Yaaya.. kawai bana so ka tafi”

"Come here.."

Da sauri ta matsa tare da kwantar da kanta a bisa kafadarshi.

Hannunta ya kamo yana murzawa ahankali yace "Kiyi haquri my Baby Angel... I have to go, I must go. that’s how it’s gonna be”

"But Yaa..."

"Sssshhhh..."

Daga nan sai ya miqar da ita suka tashi zaune yayinda yace “what’s for dinner? I am hungry”

Gani nayi ta turo baki ba tare da tace mishi komai ba.

"My Baby Angel please..."

Bai rufe bakinshi ba ya ga ta matsa nesa da shi ta kwanta ta cigaba da kuka...

Hankalinshi yayi mugun tashi ganin tana kuka... shi da kanshi ya sa ta kuka. He knows what her problem is but he cant solve it for her!

Dukda masifar sonta da yake yi bazai taba biye mata ba akan wannan.. ya sani sarai idan ya fara lallashinta, narkar mishi da zuciya zata yi...

Adalci tsakanin ta da Ruqayya is his top priority at the moment don haka he has to stand firm and not let her melt his heart.. 

Gani nayi ya matsa yayi mata kiss a kumatu sannan yace "I am sorry"

Tana jin shi ya sauka daga kan gadon ya fita.

***********

Washegari da sassafe Zara ta hada breakfast ta koma dakinta ta kwanta.

Farouq ne ya shigo dakin ya tarar da ita a cikin Duvet... she wasn't sleeping but she looked super worried.

“Good morning my Baby Angel”

Zara wadda ta kalle shi ce ta turo baki sannan tace "good morning"

Yana murmushi ya qaraso wurinta yace "Na ga kin shirya breakfast kuma kin dawo daki... Oya sauka mu je mu ci... nayi latti"

Ba tare da ya jira ta ba na ga ya duqa ya yaye Duvet din da ta rufa da shi sannan ya dauke cak kamar Baby.

Gaba daya jikin Zara ya mutu, she couldn't even do anything... haka ta maqale a jikin shi tana shaqar qamshin turaren shi mai dadi har suka isa dinning room din.

Gently ya zaunar da ita a kan kujera sannan ya zuba musu abincin and as usual he settled down to start feeding her first.

Da farko qin karba tayi amma ganin ya canza mata fuska ne ta bude baki.

Sai da ta qoshi kamar kullum sannan ya fara ci.

“Allah ya sani cewa I am going to miss your delicious delicacies”

“toh kayi zaman ka kawai anan mana" ta fada hoping he will agree..

Murmushi yayi yayinda ya cigaba da cin abincin shi.

A taqaice dai haka Zara ta gama kumbure-kumburen ta, tana ji tana gani Farouq ya tafi ya barta wanda ba zai dawo ba sai bayan kwana biyu.

(An fara shifting kenan🤣... an koma home and away🤣)

☆☆☆☆☆☆☆☆

FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION
(GIDAN RUQAYYA)

Wuraren qarfe goma na dare ne Farouq ya shiga gidan, He just returned from the hospital.

Dakin shi ya wuce direct yayi wanka sannan ya fito ya nufi dakin ta.

Kwance take a kan gadonta tana magana da Musty a waya.

Tayi nisa a hirar da bata ji shigowar Farouq ba.

“kasan fa nayi missing dinka sossai” can kuma tayi shiru sai tace “okay, I will try” murmushi tayi tace “Junior is fine, I love you too... Bye”

Bayan ta kashe ne ta jiyo muryarshi kamar daga sama...

"who was that???"

A firgice ta tashi tsaye tana kallonshi... gaba daya ta rude. jikinta sai rawa yake yi yayinda kanta yayi nauyi. Ji take yi kamar tayi tsuntsuwa ta gudu...

“who was that?” ya qara tambayarta yayinda ya fara approaching dinta.

Gani nayi tana ta hadiye miyau yayinda take qoqarin yin magana amma ta kasa... she looked like a thief that was caught red-handed.

“give me the phone”

A razane tace “Uhmm uhmm Honey... Cou-cou-cousin dina ne fa”

"I said give me the phone"

Hannunta na rawa ta miqa mishi...

Farouq ya karba sannan ya shiga call log dinta yayi dialing last contact- Musty!

Gani nayi ya sa wayar on speakerphone yayinda ya sa mata idanuwa yana jira Musty yayi picking..

Mai karatu ni da nake kallon fuskar Farouq I was suprised because babu alamun bacin rai ko fushi a tattare da shi... he looked calm and unbothered.

“hey love, did you forgot to tell me something?” suka jiyo muryar Musty.

Da sauri Ruqayya tace “ehm, dama Honey ne zaku gaisa, kasan fa har yanzu baku taba haduwa ba... you are on speakerphone”

Tayi saurin yin magana ne just to alert Musty kar ya kwafsa...

Musty wanda ya dan yi shiru ne yace "oooh, Allah sarki my In-law har yanzu dai bamu hadu ba, the last time da na zo baka nan”

Farouq wanda yake kallon Ruqayya ne yace “Eyyah, and I really would love to meet you don na ga alama wifey tana ji da kai”

Dariya Musty yayi yace “ai she is my favorite, I love her sooo very much”

“easy bro, its my wifey we are talking about”

“My sincere apology” Musty ya fada yana dariya.

Farouq yayi murmushi yace “Apology accepted. we need to set up a time to meet, what do you say?”

“ba damuwa, zanyi tafiya gobe idan na dawo, we will insha Allah. Please take care of my sister”

“she is in good hands... trust me”

Ruqayya dai tana nan tsaye tana sauraron su... Gaba daya hankalinta a tashe yake, duk sanyin da ke dakin bai hana ta yin zufa ba... Addu'a kawai take yi kar Musty ya kwafsa... ta sani sarai dan iska ne kuma zai iya fadin wata Magana da zata iya zame mata matsala.

Jin suna sallama ne na ga ta saki ajiyar zuciya...

Bayan Farouq ya kashe ne ya miqa mata wayar sannan yace “your cousin seems nice, I really want to meet him, please idan ya dawo do let me know”

A sanyaye tace “toh Honey”

"why are you sweating?? are you alright???" ya tambayeta tare da matsawa ya dafa goshinta sannan ya shafa wuyan ta just to feel her temperature.

"I am fine Honey..."

hmmmmmm!

***********

A yanzu dai abubuwa sun birkice ma Zara.

Sati uku kenan da yin auren su wanda yayi daidai da saura sati daya Farouq ya sake ta a yadda suka yi plan dinsu.

A kullum Farouq qara shiga ranta yake yi, gaba daya yanzu tunaninta duk na Farouq ne.

A duk lokacin da zai koma gidan Ruqayya ji take yi kamar ta mutu. Gaba daya bata jin dadin rayuwarta sai ya dawo gidanta.

toh fa!!!

************

Aha my people...

Da alama dai Farouq ya fara samun nasara akan Zara! Dama dai yayi alqawari akan lallai sai ya sa ta So shi cikin wata daya... Shin dagaske ta fara Son shi ne????

Hajiya Ruqayya dai al'amarin nata ba'a cewa komai... da alama tana gab da asirin ta ya tonu. Shin zata bari Farouq ya hadu da Musty kamar yadda ya buqata ko kuwa???

Kindly show some love!!
Vote,
And most importantly Comment.

One love❤
Fadeelarh1

Continue Reading

You'll Also Like

563K 15.2K 20
"ဘယ်သူကမှ သူရဲကောင်းအဖြစ်မွေးဖွားလာတာမဟုတ်ဘူး သူရဲကောင်းတစ်ယောက်၊ ခေါင်းဆောင်ကောင်းတစ်ယောက်ဖြစ်ဖို့ဆိုတာ ပင်ကိုယ်အရည်အသွေးနဲ့ ကိုယ်တိုင်လုပ်ယူထားတဲ...
1.7M 123K 67
ဤဇာတ်လမ်းပါ အကြောင်းအရာသည် စာရေးသူ၏ စိတ်ကူးယဉ် သက်သက်သာ ဖြစ်၍ မည်သည့်အဖွဲ့အစည်း၊ လူပုဂ္ဂိုလ်ကိုမှ ထိခိုက်စော်ကားလိုခြင်းမရှိပါ။ #Boylove#Romance#Maf...
716K 63K 77
It is a story about two sisters that are like the two sides of a coin, totally different yet part of each other. It is a story about loneliness, sadn...
16.5K 1.4K 63
Rai dai kirkirarren labari ne na rubuta domin fadakarwa, ilmantarwa da nishadantarwa. Duk wanda yaji wani abu me kamanceceniya da rayuwarsa arashi ne...