BA SON TA NAKE BA | ✔

By fadeelarh1

326K 25.4K 2.4K

"BA SONTA NAKE BA" Shin dagaske ba sonta yake ba? Shin ita din son shi take?? More

PROLOGUE
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
EPILOGUE

Chapter 33

6.4K 464 32
By fadeelarh1

Abu Umamah reported: The Messenger of Allah, peace and blessings be upon him, said:
"Whoever loves for the sake of Allah, hates for the sake of Allah, gives for the sake of Allah, and withholds for the sake of Allah has perfected the faith."
Source: Sunan Abu Dawud

***************


CUNNINGHAM MARQUEE EVENT CENTRE
ABUJA

Motar Amarya ce ta shigo harabar wurin yayinda 'Yan matanta da kuma abokan ango ke tsaye suna jira...

Ko da Sadiq ya faka motar sai na ga ya dauki wayar shi yayi dialing lambar Farouq.

“Ya Farouq gata nan na dauko ta”

Shiru ya dan yi sannan yace "Okay sir"

Bayan ya kashe wayar ne Hafsat tace “toh babes, ni dai bari in qarasa in dan yi coordinating kafin ki fito, sai mun hadu”

Hafsat tana fita daga motar ne Farouq ya shigo tare da kunna wuta.

"Wooow" na ji ya fada yayinda ya sa mata idanuwa babu qyaftawa..

Tana murmushi tace "what??"

Farouq na ga ya kalli Sadiq wanda ya zuba musu idanuwa ta mirror yana so ya ji me zai ce...

Buga kafadar shi yayi yace “guy, your job is done, I need some privacy please”

Sadiq ya fashe da dariya yace “sorry bro, I wanted to hear your flows ne I swear but I guess I will have to wait till another time... bari in tafi toh”

Bayan ya bude qofar ya fita ne na ga Farouq ya matsa daf da ita yace "Kin ga kyan da kika yi kuwa???"

Murmushi tayi tace "Yaaya kai ma fa kayi kyau sossai"

Hannunta na ga ya kamo yana shafawa... Wani irin mugun sanyi Zara ta ji yayinda zuciyarta take bugawa....

“na taba fadi miki cewa kin fi ko wacce mace kyau a duniyan nan?”

Zaro idanuwa tayi tace "What??"

"Yes Zara, You are very very beautiful... ban taba ganin macen da ta fi ko kyau ba"

Cike da murna da farin ciki tace "Nagode sossai Yaaya... I swear this means alot to me"

Hanunta da yake riqe da shi ne na ga ya kai saitin bakinshi ya sakar Mata kiss sannan yace "Let's go... everyone is waiting"

Zara dai tunda ya sakar Mata kiss a hannu ta kasa motsi... Haka ta bi shi da idanuwa har ya bude qofar shi ya fita....

within few seconds ta ji ya bude qofarta sannan ya miqa Mata hannu yace "let me help you.. come"

Murmushi na ga tayi sannan ta miqa mishi hannu ya taimaka mata ta fito...

Aikuwa Zara tana fitowa na ga Farouq yayi freezing a tsaye...

he was only checking her out by moving his eyes form her head to toe....

Gaba daya hankalinshi ya tafi a kallonta wanda ta kula da hakan... Snapping fingers dinta tayi saitin fuskarshi tace "Yaaya what happened?? na ga kana ta kallona ne... Kayana basuyi kyau ba ne??"

Ajiyar zuciya ya saki sannan ya dan bata rai yace “wai haka zaki shiga?”

Ta kalli jikinta tace “eh Yaaya... ban yi kyau bane?”

Aikuwa nan da nan ta nemi ta fara kuka....

Da sauri yace "Hey dont cry... you shouldn't ruin your make up"

Hannunta ya kamo ya riqe sannan yace “On the contrary, kinyi kyau sossai... what I am trying to say is, shi dinkin haka aka yi shi? aren’t you suppose to cover yourself up with a veil or something?”

Zara wadda ta turo baki tace "Haka yake Yaaya..."

Shiru na ga ta dan yi sannan tace "wait... are you jealous?” yayinda ta kashe mishi ido dqya.

"Nope" ya fada while trying to look unbothered amma ya kasa.

it's written all over him that he is jealous!

Side hug ta bashi tace "Please dont be..."

******************

Qawayen amarya da abokanen ango ne suka jagoranci shigowa hall din.

Bayan sun shigo ne Ango da Amarya ma suka shigo riqe da hannuwan juna.

Sunyi masifar kyau... Sai hotuna ake daukar su yayinda MC yake ta yaba kyan da suka yi tare da wasa su....

"Ya Farouq please ka rage sauri mana"

"wa yace ki sa dogon takalmi? kin cika rigima I swear"

Fashewa tayi da dariya tace “toh Ya Farouq kai ne ai you are tall, idan ban sa takalmi mai tsawo ba za’a yi mun kallon dwarf”

Fashewa yayi dariya shima tare da rage sauri....

Gani nayi ya janyo ta jikinshi tare da bata support... Hakan ya sa ta maqale a jikinshi kamar wata mage yayinda suka cigaba da hira not minding the number of eyes that are on them.

Daddy ya kalli Abba wadanda suke zaune tare da abokanen su yace “ka gan su ko? Kamar ba su bane suke ta bata rai don mun ce zamu hada su”

Abba yana dariya yace “ai wadannan yaran ka qyale su kawai”

Zara dai yau all white ta sa na wani shegen dinki mai masifar kyau da Galiafahad yayi mata, tayi masifar kyau.

Biki dai yayi biki, ana ta shagali. An ci an sha sannan anyi rawa.

A lokacin da MC ya kira Zara ta fito tayi rawa tare da qawayen ta ne Farouq ya hana.

Abu dai kamar wasa MC ya dage akan lallai sai Farouq ya bari ta fito amma ya qi.

Haka kuwa aka dinga yi musu dariya.

“gaskiya idan ba qwaqwarar dalili zaka bamu ba bazamu yarda ba sai amarya ta fito...”

Farouq wanda ran shi ya fara baci da insistence din MC din ne yace “qafarta na ciwo”

Gaba daya hall din aka fashe da dariya yayinda MC ya kalli Zara yace “Amarya wai dagaske qafar ki na ciwo?”

Zara ce na ga ta kalli Farouq looking Sad tace “Ya Farouq please ka bari inyi kadan... ka ga na kamu da na fara shima janye ni kayi..”

“Idan kika sake kika yi rawa you will remain stuck with me forever..”

Cike da mamaki Zara tace "what??"

"Yes, deal is off" ya fada ba tare da ya kalle ta ba.

Da sauri ta kalli MC din tace “dagaske ne, qafana na ciwo”

Reply dinta ya qara ba kowa dariya yayinda suke mamakin ace amarya bazata yi rawa ba ranar bikinta... amaryar ma Zara sarkin son rawa!!

Mamy ce tace “Allah sarki Zara sarkin son rawa, Allah kadai yasan me yace mata that she agreed not to”

Anty ce tace “Could it be saboda kayan da ta sa ne?? na ga ko da suke shigowa he kinda covered her stylishly..."

Granny tana dariya tace “Allah dai ya qara mata” yayinda su Mamy suke ta dariya.

Haka dai ‘yan uwa da abokanen arziki suka dinga cashewa a fagen rawa yayinda Zara ta dinga turo baki tana fushi saboda Farouq ya hana ta.

Farouq dai ya sani cewar ya bata mata rai but what to do??? he doesnt like it when she dance and people look at her.. Again, kayan da ta sanya dukda ya rufe jikinta gaba daya she didnt use veil on it.. how does she expect him to let her dance like that??? 

Gani nayi ya janyo ta jikinshi yace “hey I am sorry please, I have my reasons. Ba haka nan na qi amincewa kiyi rawa ba”

Cikin shagwaba tace “but Ya Farouq even the last time…”

Yace “ssshhhh, I am sorry please princess kinji?”

Yadda ya dinga lallashinta kamar Baby ne ya bata mamaki... So Farouq can be this sweet?? wow!

Gani nayi tayi murmushi tace “its okay, Na haqura”

Bayan an gama dinner din ne Farouq ya janyo Zara ya saka ta a mota sannan ya Kira Hafsat itama ta shiga motar yace ma Sadiq ya kai su gida...

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION
(GIDAN ZARA)

Bayan an dawo daga dinner an sha hira ne kowa friends dinta suka wuce guest section yayinda su Safa suka nufi daya daga cikin dakunan section din Zara..

Zara wadda take a gajiye kuwa sai da Layla Hayat ta lallaba ta tayi wanka cikin turaruka kamar kullum, Bayan ta fito ne ta bata wasu mayyuka ta shafa.

Zara dai at this point in time ta gaji da wannan aiki na Layla... dukda tana qaunar qamshi a rayuwarta, an qure ta.

Bayan sun kimtsa ita da Hafsat ne na ga sun koma kan gado sun kwanta.

“babes wai baki fadi mun ba... did Ya Farouq finally told you he loves you???”

Zara ta zaro idanuwa tace “na shiga uku da ke bestie, wai ku wa yace muku sona yake? why do you guys insist on this??”

Hafsat ta ja tsaki tace “wai ke har ma sai ya fada ne? it's obvious mana... Ga abu kowa yana gani. A dinner dinnan fa both of you were all over eachother, at a point ma kun zama lost a cikin soyayya that you didn't even care about the number of eyes that were on you... c'mon babes”

Zara wadda ta gyara kwanciyarta ce tace “I agree that we were lost but not in love... hira kawai muke yi. You guys need to understand that Ya Farouq ba sona yake yi ba.. he is just acting up ne saboda he has no choice... I dont think he will ever love me because he has a wife kuma ita yake so”

Hafsat ta girgiza kai tace “okay ooo, ke kin ce ba sonshi kike ba, shima kin ce ba sonki yake ba... ku cigaba da denying juna”

Zara tana dariya tace “Hey bestie... I really care about Ya Farouq and I have always wanted him to care about me which he really does but aside that, there is nothing between us, trust me babes”

Hafsat ta harare ta sannan tace “ke qyale ni da shirmen banza, good night” 

Zara wadda take dariya tace "Good night my one and only bestie"

*************

Washegari da daddare ne aka shirya zara don tarbar angonta.

Layla hayat ta kimtsa ta tayi kyau sossai. Zara dai ta sha qamshi har ta gaji.

Farouq tare da abokanen shi ya shigo gidan. Sun ba qawayen amaryan kudi har naira miliyan biyu su raba yayinda suka yi ma su Farouq addu'a tare da yi musu fatan alkahiri.

Abokanen nashi ne suka tafi da qawayenta and they left Hafsat and Mukhtar.

Sadiq kuma shine ya tafi da su Saima gida.

********************

Mukhtar Zaune a babban falon Zara tare da Farouq suna hira.

“abokina finally mun kawo maka love of your life, I don’t even need to tell you to take care of her, Please make her happy”

Farouq wanda yake murmushi ne yace “thank you my friend”

Hafsat ce ta shigo falon ta kalli mijinta tace “shall we???”

“har kunyi sallama? Hope dai baki sa ta kuka ba?”

Hafsat wadda tayi dariya ce tace “ai bata ma san zan tafi ba, I told her I was going to get some water ne”

“kin kyauta, lets go”

Har wurin mota Farouq ya raka su. Bayan yayi musu godiya ne sukayi sallama.

Bayan su Mukhtar sun tafi ne na ga ya tsaya yayi Magana da Chief security na gidan sannan ya wuce cikin gida.

Kai tsaye sashen shi ya wuce don yin wanka.

*****************

Zara tana kwance a kan gadon ta tana ta kallon posts din hotunan su a instagram wadanda ake ta reposting ana commenting.


Wayarta ce tayi ringing...

Mahmood ne!!! 

Kallon wayar na ga tana ta yi har ta gama ringing batayi answering ba.

Few seconds later kuwa sai ga text message dinshi ne ya shigo... tana budewa ta ga saqo kamar haka:

“please cutie just pick up even if its going to be for the last time”

Immediately kuma incoming call dinshi ya shigo and she decided to answer...

A wannan lokacin Farouq ya fito daga sashen shi sanye cikin wandon sweatpant hade da polo T-shirt... he looked handsome as always!

Sashen Zara na ga ya nufa.

Ya qaraso bakin qofar dakinta ne ya ji kamar tana Magana... like she was on a call!!

Tsayawa yayi yana sauraron abinda take fadi.

“you know I love you very much, I didn’t have a choice ne but to agree”

Shiru ya ji ta dan yi sannan tace “please forgive me, kar ka damu ina ji a jikina bazan dade a gidan Ya Farouq ba, shima fa ba sona yake yi ba”

Dariya tayi sannan tace “okay thank you, shiyasa nake qara sonka”

Farouq wanda yake tsaye ne na ga ya runtse idanuwanshi ya bude tare da shafa kanshi da hannuwanshi biyu... Ajiyar zuciya ya saki sannan ya juya ya koma sashen shi rai a bace...

************

Zaune yake a kan gadon dakin shi dafe da kai...

Kalaman Zara ne yake tunowa... kenan even after their wedding she is still assuring the stupid guy cewar zata koma mishi??? kenan dai babu soyayyarshi ko kadan a zuciyar ta sai na yaron?? lallai yana da aiki a gaban shi... He loves her and he will never give up on her, Infact he has to force her into loving him.. she has no choice but to fall in love with him because he is never gonna let her go!

Gani nayi ya gyara pillows dinshi sannan ya kwanta ya rufe idanuwa....

A bangaren Zara dai bayan tayi sallama da Mahmood ne ta miqe ta shiga dressing room dinta ta dauko rigar bacci na wandon three-quarter da t-shirt ta sanya.

Ko da ta fito ji nayi tace "imagine bestie playing me for a fool... wane ruwa ne ta je sha har yanzu bata dawo ba?? I will deal with her tomorrow"

Gani nayi ta wuce wurin Vanity mirror ta kalli fuskarta wadda ta sha kyau har ta gaji.. lip balm na ga ta dauka ta shafa a baki sannan ta ajiye.

Har ta nufi wurin gadonta zata hau ne na ga ta fasa.. Juyawa tayi ta fita daga dakin tana fadin "Ya akayi Ya Farouq bai zo yace mun goodnight ba??"

Tafe take tana bin kowanne lungu na gidan da kallo... she has been in this house since yesterday amma har yanzu akwai wuraren da bata shiga ba a dalilin mugun girma da gidan yake da shi.

Zara dai sossai take son gidan. Kamar yayi shawara da ita lokacin da ake gina gidan don kuwa tsarin gidan gaba daya is to her taste.

Tana shiga sashen Farouq na ga ta zaro idanuwa tare da fadin "wow, this is breathtakingly beautiful”

Tana tafe tana ta kalle-kalle har ta gano dakin shi...

Bude qofar tayi kamar kullum ba tare da knocking ba ko sallama.

Farouq wanda yake kwance a kan gadon shi ya ji shigowarta amma bai motsa ba... he was actually wondering me ta zo yi bayan ta gama hirar soyayya da sakaren yaron nan..

“laaa, Ya Farouq yayi bacci shine bai zo yayi mun goodnight ba??”

Gani nayi ta bi dakin da kallo..

"Hmmm, what a beautiful room this is"

Ji yayi ta qaraso wurin shi ta hau kan gadon sannan ta janyo Duvet ta rufa mishi tana fadin "the room is too cold..."

Gashin kanshi ta dan birkita ahankali tace "Since you decided not to come say goodnight, ni gashi na zo nayi maka... Good night handsome"

Yana jinta ta sauka ta kashe mishi wuta sannan ta fita.

Ba tare da ya bude idanuwan shi ba ya gyara kwanciya tare da fadin "I cant believe this.."

Haka yayi bacci yana shaqar qamshinta da ta bar mishi a dakin wanda yake bala'in so

**************

Toh my people Ya Farouq zaiyi da Zara???

Can he really make her fall in love with him???

Shi kam duka Matan nashi sai ahankali... ba Ruqayyar ba sannan ba Zarar ba... Kowacce da abinda ta sa a gaba🤣

What next???

Kindly show some love please👇👇

One love❤
Fadeelarh1

Continue Reading

You'll Also Like

327K 8.1K 78
တောင်ပေါ်သားနဲ့ မြေပြန့်သူ ဇာတ်လမ်းလေးပါရှင့်
2.6M 251K 40
1920ခုနှစ်လောက်က လူနေမှုပုံစံတွေကို inspireယူပြီး ရေးဖွဲ့ထားတဲ့ Own Creation rebirth fictionလေးပါ။ _________# Starting date_26.6.2020 Ending date_6.1...
187K 18.1K 54
Ta tafka babban kuskure a rayuwarta... Shin zata iya gyara wannan kuskuren ko kuwa??
277K 14.3K 83
🍁ကောင်းခြင်းတည်မြဲ.. 🍁 နိုင်ငံခြားပြန်ကောင်လေး။ ရုပ်ရည်၊ ပညာ၊ စည်းစိမ်ဥစ္စာပြည့်စုံကြွယ်ဝသူမို့ အတော်လေးကြီးကျယ်သည့်လူ။ သူ့ကိုသူလည်း အထင်ကြီးလွန်းပ...