BA SON TA NAKE BA | ✔

By fadeelarh1

331K 25.7K 2.4K

"BA SONTA NAKE BA" Shin dagaske ba sonta yake ba? Shin ita din son shi take?? More

PROLOGUE
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
EPILOGUE

Chapter 11

6K 461 27
By fadeelarh1

Jabir also reported that the Messenger of Allah, (PBUH), said, "No Muslim plants something without what is eaten from it being sadaqa for him. Even what is stolen from it is sadaqa for him. And no one visits it without that being sadaqa for him." (Muslim)

**********

KHALIL MANSION
MAITAMA ABUJA

Hafsat ce zaune a kan gadon dakinta tana magana da Galiafahad a waya. Galiafahad dai wani shahararren fashion designer ne wanda ake ji da shi a qasar Dubai. they are actually discussing about her wedding dress wanda zai dinka mata..

Bayan ta gama wayar ne ta kalli Zara wadda take latse-latsen wayarta tana murmushi.

"Babes wai ban tambaye ki ba, me kike shirya mana ne na Birthday? Kin dai san ba haka nan zaki bar mu ba ko?"

"labarin da muke yi kenan da Sweetie, yace zai yi organizing party, I don't know whether to agree or not"

Hafsat ta bata rai tace "idan dai Mahmood zai hada party toh bazan je ba"

Zara ta ajiye wayarta a gefe ta kalli Hafsat tace "haba bestie, wai meyasa ba kya son Sweetie ne? the other day ma fa sai da ya tambaye ni"

"babes ni fa ba wai shine bana so ba, I don't like him with you ne... baku dace ba gaskiya"

Zara ta fashe da dariya tace "ke ai kin dace da Ya Muky"

"yi haquri qawa ta"

************

Wuraren qarfe takwas na dare ne Zara ta bar gidan su Hafsat.. A kan hanyar ta ne ta biya Frozenscoop don siyan Ice cream.

Ko da ta shiga ta siya ta fito tana shirin yin reverse ne wani mai mota ya shigo wurin da gudu, dayake waya yake bai kula da motar Zara ba sai ya gabza mata da qarfin tsiya.

Ihu Zara tayi a dalilin kan ta da ya bugu da steering yayinda qafarta ta taka birki.

Nan da nan mutanen da suke harabar wurin da wadanda suke ciki duk suka fito suka taru yayinda ake ta yi ma mutumin fada tare da bashi rashin gaskiya.

Zara dai ko fitowa daga motar ta kasa yi... Dafe kanta tayi yayinda jikinta yake ta rawa.. babu shakka she is still in shock!

Mutumin da ya buga mata ne ya qwanqwasa mata gilas din motar ta don ya bata haquri domin kuwa barnar da yayi mata yasan bazai iya biya ba.

Its actually an expensive Mercedes Benz! One you can hardly find around in town!

Zara wadda ta sauke gilas din tana kallon mutumin har ya gama magana bata san me yace ba..

Gani nayi ta daga mishi hannu sannan ta ja gilas din motar..

Mutanen da suka taru sun so ta fito su ga yanayinta amma ko alama bata bi ta kansu ba.

Hannunta na rawa ta janyo wayarta tayi dialling lambar shi... Wayar tana daf da tsinkewa ne yayi picking

"Hello, Ya Farouq don Allah ka zo"

A lokacin ya baro asibiti kenan yana kan hanyar zuwa gida.

Cike da masifa yace "are you mad? In zo ina?"

Fashewa tayi da kuka tace "yi haquri yaaya, I had an accident yanzun nan, ina frozenscoops. I am confused and i dont know what to do, I just... I am...."

Hankalin shi a tashe yace "subhanalillah, hey are you okay?"

"I dont know, please ka zo"

Daga nan ta kashe wayar ta kifa kanta wanda yake yi mata bala'in ciwo a kan steering...

Minutes later ne Farouq ya shigo harabar wurin.. Motar Zara ya hango da mutane a tsaye.

Da sauri ta faka motar shi a gefen nata yayinda ya fito..

Ko da ya kalli Bumper din motar da yadda tayi kaca-kaca yayi mamaki.. it looked very bad!

Hankali a tashe ya qarasa ya qwanqwasa mata gilas.

Zara wadda ta dago kai ta gan shi ce ta bude da sauri ta fito ta rungume shi very tight tana rusa kuka.

And for the first time, Farouq bai yi attempting ture ta ba infact gani nayi yayi hugging dinta shima.

"its okay, I am here" ya fada tare da bubbuga bayanta alamar lallashi.

Breaking hug din yayi ya dafa kafadunta yace "are you hurt?? ina ne yake yi miki ciwo??"

"My head...."

"Come" ya fada yayinda ya ja ta zuwa motar shi ya bude ta shiga ta zauna sannan ya rufe.

Dawowa yayi wurin motarta zai dauki kayanta yayinda yake tambayar mutanen wurin abinda ya faru.. Nan da nan kuwa suka yi mishi bayani tare da jajanta mishi.

the most important thing is that she looks okay, babu injuries sustained, kawai ta dan bugu ne sai shock da take ciki don haka he instantly let go wanda yayi causing accident din yayinda yake ta yi mishi godiya tare da qara bashi haquri.

Ko da ya kwashe hand bag dinta da ice cream din da ta siya ya sanar da security din wurin cewar zai aiko a zo a dauki motar Zara gobe da safe.

♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤

AL-HUSSAIN MANSION
MAITAMA ABUJA

Mamy tana zaune a falonta ta ga Zara ta shigo dafe da kai tana kuka yayinda Farouq yake biye da ita riqe da hand bag dinta da ledar ice cream.

Hankalinta a tashe ta miqe tsaye tace "Princess ya na gan ki haka? me ya faru??"

Zara ta nufi wurin Mamy ta rungume ta yayinda Mamy ta kalli Farouq tace "lafiya? what happened to her???"

"She had an accident ne Mamy amma dai da sauqi"

Mamy ta dafa goshin Zara wanda yayi zafi sossai tace "subhanalillah, ga kanta yayi zafi sossai. Meyasa baka kai ta asibiti ba? You have to do something"

"yi haquri Mamy.. first, let's take her to her room"

*******************

after a while!!

Kwance take a kan gadon ta tana bacci.

Mamy ce zaune a gefen ta yayinda Farouq yake tsaye yana kallon ta.

Mamy ta dago kai ta kalle shi tace "hope she will be fine?"

"Insha Allah Mamy, maganin da ta sha will do the magic"

Stool ya janyo ya zauna sannan yace "daga yau kada Zara ta sake fita da mota da daddare"

"abinda na gama tunani kenan, don't worry about that, I will take care of it"

*******************

Washegari da safe Zara tana kwance a kan gadonta ne Hafsat ta shigo.

Da sauri ta nufi wurinta tace "bestie how are you feeling"

"I am feeling much better, baki je school bane yau?"

"wane school bayan bestie dina ba lafiya, Allah dai ya tsare gaba"

Kafin Zara tayi Magana ne aka qwanqwaso qofar.

Farouq ne ya shigo.

"Ya Farouq ina kwana" Hafsat ta gaishe shi.

"lafiya lau Hafsat, ya mai jikin??"

"Alhamdulillah.."

Gani nayi ya kalli Zara wadda ta sa mishi idanuwa babu ko qyaftawa..

"how are you?"

Tashi tayi zaune tace "I am feeling better Yaaya amma dai I am a bit weak"

Qarasowa yayi ya zauna a gefenta tare da dafa goshin ta don jin temperature dinta...

Kallon shi ta cigaba da yi yayinda take admiring kyan shi.. A duniya dai bata taba ganin wanda ya kai Farouq kyau ba. like everything about him is perfect.. she could spend her whole life looking at him ba tare da ta gaji ba...

Bata ankara ba ta ji Hafsat ta girgiza ta tace "babes ya haka?"

Da sauri ta dawo daga duniyar da ta shiga..

Wayam!! bata ga Farouq ba...

"Bestie ina yake?"

Hafsat ta fashe da dariya tace "he left"

"when?? he was just here fa.. shine ko sallama bai yi mun ba??" ta fada tana turo baki kamar zata yi kuka.

Hafsat tana dariya tace "Lallai kam, yanzu dai na tabbatar there is more to this.. Babes you couldn't even control yourself a gaban shi, kin ga irin kallon da kike ta yi mishi kuwa??"

"toh wa yace yayi kyau dayawa??" ta fada tana hararar Hafsat wadda take ta yi mata dariya.

Wayar Zara ce tayi ringing.

Hafsat ta janyo wayar ta duba ta ga sunan Mahmood.

Tsaki ta ja tace "sarkin jan aji"

Zara wadda ta karbi wayar tana dariya tayi answering.

*************
*************

A yau Zara tana zaune a dakinta tana duba saqonnin mutane wadanda suke taya ta murnar zagayowar shekaran haihuwar ta.

Text messages, instagram, facebook, twitter sannan wasu suna ta kiran ta a waya.

Daddy, Anty da 'yan biyu duk sun kira ta sunyi wishing dinta. Sadiq ma ya kira ta har yana fadin idan ya dawo sai ta bashi cake dinshi tunda za'a yi babu shi... Kai hatta Granny da dangin mahaifiyarta sun kira ta..

The one message that she was looking for she didnt see.. Message from Farouq!

Jefar da wayar tayi ta miqe tsaye tana fadin "kowa ya aiko mun best wishes banda shi.. Yanzu haka ma bai sani ba saboda bai damu da ni ba"

A haka tana ta masifa tayi shirin wanka ta shiga bathroom..

Tana zaune a gaban Vanity mirror tana shafa mai ne Mamy ta shigo dakin tace "Birthday girl kin tashi?"

"Na tashi Mamy, ina kwana"

"lafiya lau, Happy birthday, yau shekarun ki ashirin cif cif. My princess ta girma, sai aure"

Zara ta turo baki tace "Mamy ba yanzu ba, sai na gama masters dina"

Mamy tana murmushi tace "toh shikenan princess... Allah ya kai mu"

"Ameen"

Ta janyo spray tana fesawa ne tace "Mamy kin ga kowa yayi wishing dina amma banda Ya Farouq ko? ban san meyasa baya so na.."

Bata qarasa magana bane Mamy ta miqa mata wani dan qaramin kwali wanda bai wuce girman kwalin agogo ba, anyi packaging dinshi simple amma yayi kyau sossai!!

Zara ta karba tana kallon Mamy confusedly.

"dazu ya aiko driver dinshi ya kawo miki"

Tsalle na ga tayi cike da murna ta rungume Mamy tana fadin "Alhamdulillah, Allah nagode maka.. I am so happy Mamy"

Mamy tana dariya tace "Princess wannan irin murna kamar kin bude kin ga abinda yake ciki?"

Breaking hug din tayi tace "ai Mamy ko ma me ke ciki I am glad it came from him.. it means bai manta ba"

Mamy dai mamaki take yi yadda Zara take girmama Al'amuran Farouq.

Bude kwalin tayi ta ga makullin mota qirar BMW.

Zaro idanuwa tayi tace "what??? a car key??"

Da sauri ta juya zata fita daga dakin yayinda Mamy ta riqo ta tace "da towel zaki fita?"

Kallon jikin ta tayi tace "oops" sannan ta koma a guje ta dauko hijabin sallan ta dogo har qasa ta fice.

Mamy tana ta dariya ta bi bayan ta.

Zara tana fitowa tayi tozali da wata brand new BMW baqa wuluk sai qyalli take yi.

Ihu ta saki yayinda gaba daya masu aikin gidan suka taso suna kallon ta suna ta yi mata dariya.

Zara kam zagaye motar ta dinga yi tana kallo sannan daga qarshe ta bude ta shiga.

Mamy tana tsaye a kan porch din gidan tana kallonta.

Bayan ta gama kalle kallen ta ne ta fito da gudu ta dawo wurin Mamy ta rungume ta tace "Mamy you know what? Wannan dream car dina ne, ya aka yi Ya Farouq ya sani? I am soo happy"

"You must have told him right??"

Shiru ta dan yi kamar tana tunani sai kuma tace "I really cant remember if I did.. but idan har na fadi mishi kenan bai manta ba??"

"yanzu dai kin tabbatar ya damu da ke ko?"

"in his own way Mamy, he is kinda weird but I still love him. Bari in shirya in je inyi mishi godiya"

♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤

CENTRAL HOSPITAL
MAITAMA ABUJA

Cikin sabuwar motarta ta shigo asibitin yayinda aka dinga kallon motar, wasu ma har nuna motar suke ana yaba kyan tsarinta.

Mai karatu babu shakka motar Zara ta hadu, it's the latest BMW wadda nake kyautata zaton sai kayi dagaske zaka ga irinta tana yawo a kan titin birnin tarayya.

As usual dai tana tafe ana ta gaishe ta tana amsawa cikin fara'a...

Secretary dinshi kuwa ko da ta gaisheta ta amsa she wanted to tell her cewar he is not on seat amma kamar kullum Zara didnt wait ta shige ofis din..

Aikuwa sai da tayi kusan awa daya da rabi tana jiran shi ne ya bude qofar ya shigo.

Riqe yake da wayar shi yana typing don haka he didnt even see her..

Qamshin turaren ta ne da ya ji ya sanya shi dago kai da sauri wanda kafin yayi wani motsi ya ji ta rungume shi ta baya.

"Ya Farouq thank you very much for the gift"

A daidai lokacin Dr. Ibrahim ya shigo ofis din.

Ganin Zara maqale a jikin Farouq ne ya dan koma baya yace "oh sorry" sannan ya fita yana murmushi.

Farouq wanda ranshi yayi matuqar baci ne yace "wai ke me ke damun ki ne? me yasa ba kya jin Magana ne?"

"Ya Farouq me nayi??" ta tambaye shi while still hugging him

"Zaki sake ni ko sai na mare ki??"

Da sauri tayi breaking hug din ta dawo ta gaban shi tana kallon shi tace "Ya Farouq is it a crime don nayi hugging dinka?"

Ran shi a bace yace "kina nufin baki san hakan ba? you are not a child anymore don haka start behaving like a grown up"

Hannun shi ta kamo ta riqe gam sannan tace "sorry big brother, dama na zo inyi maka godiya ne akan birthday gift din da ka bani. Thank you very much, I love it"

Farouq dai mamaki Zara take bashi, yanzu ya gama yi mata fada akan hugging dinshi da tayi and just few seconds later she is holding his hands.. lafiyarta kuwa???

Hannun shi ya fizge yace "Okay.. you can go"

Ya wuce ya zauna yayinda ya fara duba wasu files a laptop dinshi.

Zara wadda take tsaye bin shi tayi da idanuwa tana mamakin halin shi.. Sossai ya bata haushi don haka ne tayi deciding ita ma ta rama Instantly!

Murmushi na ga tayi sannan ta zagaya ta gefen shi ta duqa tayi mishi kiss a kumatu tace "I love you big brother... bye" tare da birkita gashin kan shi.

Da sauri Farouq ya dago ya kalle ta yayinda ta kashe mishi ido daya harda yi mishi gwalo ta ruga ta fita.

Daskarewa yayi a zaune yayinda halin Zara ya fara bashi tsoro, ya kula ma gaba daya ta daina jin tsoron shi kamar da. Abun ya kai ga haka yanzu??? ya zai yi da ita toh?? Sossai ta bata mishi rai amma ya matse.. He will deal with her!!


************

Zara dai tuni tayi posting din hoton sabuwar motar ta a instagram tana fadin her birthday gift from her Cousin 'Farouq' yayinda mutane suke ta yi mata congrats.

Mahmood ma cewa yayi he is jealous domin kuwa ya gano cewar akwai aure a tsakanin ta da Farouq wanda yake qorafi akan kada ayi mishi juyin mulki.

Hakan kuwa ya ba Zara dariya sossai yayinda ta jaddada mishi cewar shi take so.

♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤

ALHAJI ABUBAKAR BULAMA MANSION
MAITAMA ABUJA

Ruqayya tana zaune a falon Hajjaju riqe da wayar ta tana duba Instagram ne ta ga hoton motar da Farouq ya ba Zara yayi popping up a 'search' page.

She had to quickly go to Zara's page to confirm cewar ita din ce.. aikuwa dai ita din ce!

Cikin tashin hankali tace "what? Honey ya ba Zara kyautar wannan motar? Ni fa?"

Hajjaju da take zaune tana lissafin wasu kudaden ta ne ta kalli Ruqayya tace "zauna nan dai, arzikin ma kin kasa ci. Haka dai kika ce bai damu da ita ba, ga zahiri kin gani. Mu ga hoton motar" ta miqa hannu alamar Ruqayya ta bata wayar ta gani.

Ruqayya hawaye na bin fuskarta ta miqa ma Hajjaju wayar.

"danqari, ai wannan ko shi baya da irin ta... babu shakka an sha da ke"

Ruqayya tace "wallahi bai isa ba, ni zai wulaqanta haka?"

Hajjaju ta miqa mata wayar ta tace "ai kam sai dai kiyi haquri"

"Hajjaju yakamata mu koma wurin bokan nan, Ni kawai ya nemi yadda zai yi ya batar mun da Zara, she is trouble in my life"

"kin manta abinda yace ne?"

"ai dole ne ya samo wata hanyar"

"toh ki bari idan na dawo daga Dubai sai mu je"

***********

Whoa... Zara tana wuta🔥🔥🔥
Toh amma fa gashinan Ruqayya zata halaka ta akan Farouq...🙄🙄

Tambaya anan shine shin Zara tana son Farouq ne????

Love, obsession, infatuation, care... (you name it)

Which one na????

***********
Kindly vote
Comment

And thank you very much for reading!

One love❤
Fadeelarh1

Continue Reading

You'll Also Like

3.2M 151K 62
Start Date>>>> 1.4.2020 End>>>20.5.2020 ကိုယ့်ဘက်က အချစ်တွေပေးခဲ့လည်း ပြန်ရခဲ့တာက နာကျင်မှုတွေတဲ့လား မင်းအမုန်း​တွေကိုထပ်ပြီးမခံစားနိုင်တော့လို့ ငါထ...
49.9K 5.2K 37
"Babu wanda ya ke tsallake kaddararsa a rayuwa Adda. Duk abunda kika ga ya faru dake to Allah ya riga ya rubuta tun kafin kizo duniyan nan. Hakuri za...
810K 26.3K 59
ကိုယ်ဟာ ကြိုးဝိုင်းထဲမှာ ကိုယ့်ကိုစိန်ခေါ်လာသမျှကောင်တွေအကုန် ထိုးရဲတယ် သတ်ရဲတယ် ကိုယ်နိုင်မယ်ဆိုတဲ့ယုံကြည်မှုရှိတယ် ကိုယ်မလုပ်ရဲတာဘာမှမရှိဘူးလို့ထင...
Rumfar bayi By mss hijabie

Historical Fiction

584K 48.9K 59
A historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid