BA SON TA NAKE BA | ✔

By fadeelarh1

326K 25.5K 2.4K

"BA SONTA NAKE BA" Shin dagaske ba sonta yake ba? Shin ita din son shi take?? More

PROLOGUE
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
EPILOGUE

Chapter 7

6.3K 492 21
By fadeelarh1

Abu Hurayra reported that the Messenger of Allah, (PBUH), said, "The strong man is not the one who throws people in wrestling. The strong man is the one who has control of himself when he is angry." (Agreed upon)   

***********

Ruqayya dai samun kujera tayi ta zauna ta fashe da kuka yayinda ta dafe kai tana tunanin qaryar da zata yi ma Farouq domin kuwa rabuwa da shi is not an option for her.

Bata taba sanin cewa Farouq ya gane ba, sannan abinda ya fi bata mamaki shine yadda bai fadi mata ba sai yanzu.

Sai kyarma take yi yayinda take ta kuka. Bata ankara ba sai ganin shi tayi ya fito daga wanka inda ya cigaba da shirin shi hanakali a kwance.

Bayan ya kammala ne ya haye gadon shi ya kwanta.

Ruqayya ta miqe tsaye jiki a sanyaye ta nufi wurin shi tana share hawaye ta zauna a gefen shi tace “Honey let me explain what happened please listen to me”

Farouq wanda ya qagara ya ji bayanin ta yace “I am listening”

Ajiyar zuciya ta saki sannan ta fara bashi labari kamar haka:

A lokacin da mahaifi na ya rasu, ni da Hajjaju mun kasance mu kadai a gidan mu, sai mai gadi a waje. Bayan ya rasu da wata biyar ne watarana da daddare ‘yan fashi suka kawo mana hari har cikin gida. Sun kashe maigadin mu inda suka samu damar shiga har cikin gidan mu. A lokacin ne..”

Kasa qarasa labarin tayi yayinda ta ta fashe mishi da kuka..

Da sauri Farouq ya tashi zaune cike da tausayinta ya janyo ta ya rungume yana fadin “its okay, you don’t need to go further”

Ajiyar zuciya Ruqayya ta saki yayinda ta ji dadin kalaman shi.

A duniya zata iya yin komai don ta kasance matar Farouq, she cant afford to lose him. Right now ta tabbatar yayi buying qaryar da tayi mishi..

Cikin sanyin murya ne tace “Honey, Zara..”

Yana shafa gashin kanta yace “Zara what? Zara qanwa ta ce, she is my baby sister so relax, babu abinda yake tsakanin mu”

Qara rungume shi tayi yayinda take cike da farin ciki marar misaltuwa.

Aikuwa a wannan daren for the first time soyayya lafiyayya ta gudana tsakanin Farouq da Ruqayya domin kuwa Farouq ya cire duk wani zargi a ran shi ya rungumi Ruqayya a yadda take.

Ruqayya kuwa kamar ta zuba ruwa a qasa ta sha don farin ciki.. she has sealed the problem!

************

Bayan su Farouq sun wuce Germany da sati daya ne Sadiq ma ya koma makaranta.

Kamar kullum gidan ya koma daga mamy sai Zara domin kuwa Abba kullum yana tafiye tafiye. Idan har yana Nigeria ma ba’a ganin shi sossai domin dai yanayin aikin nashi baya bashi lokacin kan shi balle na iyalin shi. lokutta kadan ne zaka gan shi a gida cikin iyalin shi.

Zara dai har yanzu tana nan tana aika ma Farouq hotunan ta kamar kullum tare da bashi labarin abubuwan da take yi. A bangaren Farouq kuwa ko ya gani baya yi mata reply sannan ita kuma bata damuwa da hakan.

***************

BAYAN WATA SHIDDA

AL-HUSSAIN MANSION
MAITAMA ABUJA

Kwance take a kan gadon ta tana ta baccin ta cikin kwanciyar hankali.

Qarar wayar ta ce ta tashe ta daga baccin da take yi. Tsaki tayi sannan ta janyo pillow ta toshe kunnen ta da shi. Haka wayar tayi ta ringing tana tsinkewa bata daga ba.

Wuraren qarfe goma sha daya Mamy ta qwanqwaso qofar dakin ta shigo. Murmushi tayi ta nufi gadon ta zauna tare da zare pillow din da Zara ta rufe fuskarta da shi.

Motsi tayi ba tare da ta bude idanuwan ta ba tace “Mamy please”

“I thought kin ce zaki je gidan su Hafsat yau”

Da sauri Zara ta bude idanuwanta ta miqe tana fadin “oh my God, whats the time? Yau Hafsy zata ci qaniya na”

Mamy tana murmushi tace “its just past 11, maza je kiyi wanka ki sauko kiyi breakfast”

Zara ta sauka daga kan gadonta sannan ta duqo tayi ma Mamy kiss a kumatu tace “okay Mamy.. thanks for waking me up” ta nufi dressing room dinta don shirin wanka yayinda Mamy tayi murmushi ta miqe ta fita.

Zaune take a cikin qaton Jacuzzi din kewayen ta, qamshi kawai ke tashi kamar anyi barin turarruka, wasa take da ruwan kamar kullum. Idanuwan ta a lumshe suke yayin da take jin dadin ruwan da take ciki. Tayi kusan minti talatin a cikin Jacuzzi din sannan ta dauraye jikinta ta fito.

Tana zaune a gaban Vanity mirror tana ta shafe shafen mai da turaruka. Wayar ta ce tayi ringing, ta miqe ta nufi bed side drawer inda wayar take ta dauka.

Ganin sunan Hafsat ne yasa tayi murmushi ta amsa tare da fadin “Babes how far” a dayan bangaren Hafsat tace “wallahi if it were possible for me to change a friend I would have done so tuntuni Zara”

“toh ko zaki gwada ne?”

Hafsat ta ja tsaki tace “are you daring me?”

Zara ta fashe da dariya tare da hawa kan gadonta tace “sorry bestie, I love you”

“and I hate you, where have you been ina ta kiran ki tun dazu? Hala kina ta baccin nan naki na mamaki?”

“sorry babes gani har nayi wanka ma, as soon as I eat my breakfast zan qaraso”

Bayan sunyi sallama ne ta nufi closet dinta don daukan rigar da zata sa.

Tsayawa tayi tana bin kayan ta kamar kullum, wata farar long top ta hango can qasan jerin kayan ta. Murmushi tayi tace “its definitely you baby”

Dakinta ta koma ta latsa intercom, a dayan bangaren Larai ce ta amsa cikin girmamawa.

“please come”

Cikin mintuna biyu kacal Larai ta turo qofar dakin Zara cikin ladabi ta duqa har qasa tace “ina kwana Anty”

“lafiya Larai ba sai kin duqa ba kafin ki gaishe ni, zo ki cire mun wannan kayan”

Larai ta miqe ta bi Zara har closet dinta sannan ta nuna mata kayan da zata ciro mata ta juya ta koma dakin.

Zara ta sani sarai idan da kanta zata zaro kayan gaba daya sai ta birkita closet din shiyasa ta sa Larai ta dauko mata.

Tana nan zaune Larai ta fitar mata da kayanta sannan ta fita.

Bayan ta shirya ne ta dauki wayar ta tare da makullin motarta ta fita.

Ko da ta sauko straight dinning ta wuce ta zauna, kayan abinci ne aka jera kala kala kamar kullum.

Murmushi tayi ta sa hannu zata bude warmer din da ke gaban ta sai ga asabe ta shigo da sauri tace “Anty bari in zuba miki”

Cikin ladabi ta duqa har qasa tace “ina kwana”

Zara wadda ta fara gajiya da extra ladabin da masu aikin suke yi mata ce ta girgiza kai tace “tashi asabe, lafiya lau”

Plantain ta nuna mata tace “I will take this only”

Nan da nan Asabe tayi serving dinta sannan ta koma kicin.

Bayan ta gama breakfast din ne ta miqe ta wuce sashen Mamy.

Mamy tana zaune a kan daya daga cikin Royal chairs din falonta tana magana a waya... she looked super happy!

Zara ce ta nufi wurinta ta kwanta akan cinyar ta tana sauraren ta.

“yanzu next week din Ruqayya zata dawo? Toh kai kuma sai yaushe?” ta dan yi shiru tana sauraren shi sannan tace “okay toh Allah ya dawo mun da kai lafiya my prince”

Bayan sunyi sallama ne ta kalli Zara tace “my princess har kin fito?”

“yes Mamy, Ya Farouq ya kusan dawowa ne?”

“eh, next month yace amma dai Ruqayya tana nan dawowa next week”

Zara ta tashi tana turo baki tace “uhm, Mamy wallahi ni dai bana son Anty Ruky, batada fara’a. Shima dai ya Farouq duk matan duniyan nan ya rasa wadda zai dauko sai ita”

Mamy ta fashe dariya tace “Zara hoo”

“Mamy bari in je, I will be back much later”

“okay princess, be careful and have fun”

"i will.."

Haka Zara ta fita Mamy tana mamakin yadda bata son Ruqayya.  

Tunda ta fito harabar gidan securities din gidan suke ta gaishe ta, kamar kullum sai da ta amsa su cikin fara’a sannan ta nufi motar ta qirar Mercedes Benz ta shiga ta tada ta fita daga gidan.

**************

Tana kan hanyar zuwa gidan su Hafsy kawai ta tsinci kanta cikin farin ciki marar misaltuwa. Bata san lokacin da ta fashe da dariya ba tace “Finally he is coming back” kamar ta tuno wani abu kuma sai gani nayi ta faka motar ta gefen titi ta dauki wayarta ta bude camera tayi snapping selfies sannan ta yi dan gajeren rubutu ta tura mishi as usual.

♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤

KHALIL MANSION
MAITAMA ABUJA

Zaune suke a falon gidan su yayinda suke ta hira da Mom dinta.

Zara ce tayi sallama.

Cikin girmamawa ta gaida Mom.

“ya su Mamy?”

“they are fine Mom”

Daga nan Hafsat ta ja hannun Zara suka wuce dakin ta.

Zara tana kwance a kan gadon Hafsat yayinda ita Hafsat din take nuna ma Zara wasu kayan da ta siyo a India last week da ta raka Mom.

Zara dai gaba daya hankalinta baya tare da Hafsat, she was busy staring at something on her phone..

Hafsat wadda tayi noticing hankalin qawarta yayi nisa ce tace “babes ina ta magana kin share ni”

Kafin Zara ta amsa ta ne ta qwace wayar tana fadin “what is it you are looking at that is more important than what I am saying?”

Da sauri Zara ta miqe ta biyo Hafsat cikin fushi tana fadin “give me my phone” aikuwa nan da nan suka fara zagaye dakin yayinda Hafsat take ta dariya.

Da Zara ta gaji ne ta koma ta zauna yayinda Hafsat ta duqe tana mayar da numfashi.

Kallon wayar Zara tayi tana murmushi tace “dama na san bazai wuci hoton nan kike kallo ba... wai ke Zara I don’t understand you, ya akayi kika bari yayi aure bayan kin san kina son shi??”

“who told you cewa son shi nake? He is my brother for crying out loud, sau nawa zan fadi miki hakan”

“.....and you love him”

Zara ta bata rai tace “this is something I cant explain, the reality dai yanzu shine I am head over heels for Mahmood Tafida”

Tsaki Hafsat ta ja sannan tace “no babes, you are obsessed dai. Ni wallahi na rasa meye naki da maqale ma wannan yaron. Sai shegen girman kai”

Zara wadda ta fashe da dariya tace "bazaki gane ba bestie"

"tabbas bazan gane ba"

A haka dai suna hira har suka shiga rubuta list din abubuwan da zasu siyo na bikin Hafsat din wanda ya rage wata uku.

♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤

BAYAN SATI DAYA

Al-HUSSAIN MANSION
MAITAMA ABUJA

Zaune suke a dinning room suna breakfast suna hira.

Mamy ce tace “yace Mukhtar ne zai je ya dauko ta daga airport”

Abba yace “toh madallah, yakamata dai ya dawo gida haka nan. Mu da dan mu amma wasu su fi mu morar shi”

Mamy tayi dariya.

Zara ce ta shigo dinning din as happy as always tace “morning Sir” ta nufi wurin Mamy tace “morning Mamy” tare da yi mata kiss a kumatu.

Abba cikin fara’a yace “princess how are you, kin tashi lafiya?” tace “fine Abba” yayinda ta ja kujerar kusa da shi ta zauna.

Mamy ce tace “yau kin tashi da wuri, akwai lecture kenan”

“wallahi Mamy wani lecture ne muke da, idan mutum yayi latti bazai shiga ba. lecturer din is very strict”

Mamy tace “aikuwa gwara ki shiga da wuri because bana so kina missing lectures dinki”

Apple kawai ta janyo ta fara ci yayinda ta miqe tsaye.

"wont you have breakfast??" Mamy ta tambaye ta.

"No Mamy, I am okay.."

"toh still dai find something and eat anjima kin ji?" Abba ya fada.

"I will Abba.. "

Daga nan tayi musu sallama ta tafi.

Abba ya kalli Mamy yace “I really wanted her for him”

Mamy tayi murmushi tace “ban fitar da ran hakan zai faru ba Abba, Allah ya zaba mafi alkhairi”

“Ameen”

♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤

NILE UNIVERSITY
ABUJA

Hafsat da Zara ne zaune a cafeteria suna hira.

Zara ce tace “yau wannan matar mai baqin hali zata dawo”

“wacce mata kuma?” 

“Anty Ruky mana, ai gwara ma da ya koro ta yayi zaman shi can abinshi”

Hafsat wadda ta fashe da dariya tace “yau na ga ikon Allah, mutum da matar shi. toh wai ma tsaya me ya ruwan ki da ita ne?”

Zara wadda ta turo baki  tace “toh ba yaya na take aure ba, ni kawai bana sonta”

“babes you have a serious problem”

“I swear idan ta dawo ta nemi ta shiga tsakani na da Ya Farouq sai na taka mata birki don na kula bata da kirki”

“toh sau nawa kuka hadu da har kika san batada kirki?”

“haduwar da muka yi da ita baki ga kallon banzar da take yi mun ba?”

Hafsat wadda take ta kwasar dariya tace “ina na gani tunda bana wurin a lokacin”

Haka dai Zara ta cigaba da masifa yayinda Hafsat ta cigaba da kwasar dariya.

Suna nan zaune wata Ferrari ta danno kai a harabar wurin. Tuni idanuwa suka koma kan motar.

Zara wadda take sanye da gilas a idanuwan ta tayi saurin cirewa tare da fadin “oh my God, today is my lucky day”

Hafsat ce ta harare ta tace “lucky day my foot”

A dayan bangaren wani kyakyawan saurayi ne ya fito daga motar sanye cikin jeans baqi da wata T-shirt fara, qafar shi sneakers ne sannan yana riqe da tsadaddar wayar shi a hannun shi.

Mahmood Tafida kenan, babban yaro a Nile University, Yaron Senator Isah Tafida.

Friends dinshi ne suka qaraso wurin shi inda suke gaisawa.

Daya daga cikin abokanen nashi mai suna Nura ne yace “guy ga fa mutumiyar ka can a Caf”

Juyowa yayi ya hango Zara tare da Hafsat zaune.

Murmushi yayi yace “let me go check on her”

Munnir ne yace “abokina kana bani mamaki, ka dai san wannan yarinyar ba irin tamu bace ko?”

Mahmood yayi murmushi tare da buga kafadar Munnir yace “idan na same ta zan tuba”

Suka fashe da dariya.

Ganin Mahmood ya doso wurinsu ne yasa Hafsat ta miqe tace “ni kin ga tafiya ta, bana son harkar jan aji na banza”

Zara tana dariya Hafsat ta wuce wanda ko kallon shi bata yi ba.

Cikin sallama ya qarasa wurin Zara yace “how is my Cutie doing?”

Tana murmushi tace “she is fine and you?”

“I just got better after seeing my Cutie”

Kalaman shi ne suka sa tayi wata murmushin jin dadi..

“wai me nayi ma bestie dinki ne na ga kamar bata sona tare da ke? Ko dai wani take yi ma campaign ne?”

Zara tayi dariya tace “don’t mind her, kasan bikinta ya matso so she is a bit nervous about everything”

Murmushi yayi yace “Allah ya nuna mun ranar namu bikin mu ma”

“Ameen”

************

What??????🙄🙄🙄🙄
Did i just hear Zara say "ameen"????

Me hakan yake nufi????
Who is Mahmood Tafida????

Join me in the next chappy my friends...

Vote
Comment
And yes, share

One love❤
Fadeelarh1

Continue Reading

You'll Also Like

343K 35.6K 174
English Name: After Retiring from Marriage, I became the Favorite of a Powerful Minister Associated Names: 退婚后我成了权臣心尖宠 Chinese Author: Lan Bai Ge Ji ...
9.1K 644 95
*TIE ON YOUR SEAT BELT FOR THE JOURNEY IS YET TO BEGIN* I know most people would be wondering why the novel is been tittle "THE MAID" Hausa novel ne...
728K 56K 81
It is a story about a typical Fulani Muslim girl with a perfect background and up bringing from a very wealthy family, who later meet with a destiny...
352K 8.7K 80
တောင်ပေါ်သားနဲ့ မြေပြန့်သူ ဇာတ်လမ်းလေးပါရှင့်