TWENTY (FINALE)

2K 90 5
                                    

"Toh..Zan danja hankalinki akan yadda ya kamata ki dinga tarairayar Auta ta siga daban-daban kamar;  kissa, jan hankali da kuma ladabi da biyayya kowanne xan daukeshi d'aya bayan d'aya namiki bayani akansa, Kisani dukkan xamantakewar rayuwar aure ba xata yiwu ba saida kissa, idan akace miki kissa ta kunshi abubuwa da yawa, kissa ta kasu kashi biyu akwai kissa marar kyau akwai kuma kissa me kyau, Mara kyau itace ta shirye tuggu da makirci da sihiri, Za ki ga kishiya ta kullawa kishiyarta sharri ko idan ta daidaici ta gama girki taje ta tsuga mata gishiri ko yaji ko kananzir ko kuma tai k'ok'arin fitar da ita daga gidan ma gaba d'aya, zaki ga mace ta shiga tsakanin d'an mijinta da mijin,

"Ta cikin dabara ko mace tashiga tsakanin mijinta da iyayensa da makamantansu wannan kissa mara kyau sede muce tur da ita. Allah ka ganar da masu irin wannan kissa, Amma kissa mai kyau itace kulawa da mai gidah da tarairayarsa kamar kwai wanda daga ciki akwai, Kissar magana, kissar tafiya, kissar kwalliya, kissar abinci, kissar tsafta, kissar kallo mind you ba kallon film ba to kallon miji nake nupi, yawwa se kissar shagwaba da kissar kwanciya se kissar kula da jikin mai gidah suma xan d'auki kowanne nai miki bayani akansa Ina fatan kina ganewa?!,

Cikin k'asa da kai Islam tace,

"Eh ya Fati.."

"Kissar magana: idan xakiyi magana da mijinki ki kasance cikin nutsuwa da tauna magana da xaki gaya masa kafin ki fadeta don gudun gaya masa maganar da baxai ji dadinta ba ko bata masa rai, Ki dinga magana cikin sigar hankali karki dinga bud'e masa muryarki kala kala wani lokacin ki maketa wani lokacin ki dan budeta wani lokacin ki dinga yi a hankali kamar bakyason magana, wataran kuma idan kinason gaya masa magana mai dadi ko ta soyayya kice saiya baki kunnensa xaki rada masa. Sai kissar mu ta gaba,

"Kissar tafiya; idan xakiyi tafiya kuma kin tabbatar yana gurin ko yana kallonki daga inda yake ki dinga tafiyar da xata dauke masa hankalinki xuwa gareki misali ki dinga tafiya a hankali kamar bakyason taka k'asa wani lokacin ki dinga tafiya kina karairaya kina dan jujjuya jikinki wani lokacin kuma sauri sauri xaki dingayi kina juya maxaunanki idan ta gaba yake kallon ki kisan yadda xaki dan dinga girgiza kirjinki cikin hikima bata sigar da xai gane ba, amma fa Islam mijinki kad'ai xaki dinga yiwa wannan kala kalar tafiyar cux kikaiwa wani xaki dau zunubi ne,"

Cigaba da koyamata kissoshi tadingayi kama daga kissar kwalliya, da kissar abinci kissar tsafta, da kuma kissar kallo ciki harda kissar shagwaba data kwanciya, wanda sosai Ya Fati taja kunnen Islam akan kissar kwanciya ta kar kare mata da yadda xatai kissar kula da jikin mai gidah,

"Hope kingane?!"

"Nagane Ya Fati" cewar Islam datai wiki-wiki da idanuwa wai yau Ya Fati ce take hira da ita, hirar ma ta manya duk kunya ta davaibayetaa

"Yawwa to sai dan karin jan hankali daxan miki wanda idan kika dumfafi yinsa tabbas xaki xamo shalele awurin mijinki yaxamto ba wacce yakeso da gani sai ke hanyoyin jan hankalin sune,

"Kula da duk wani abu da mijinki yafi so,ki kula sosai da duk wani abun da bayaso ki lura da abinda yake damunsa da hanyar da xaki kula da iyayensa da danginsa da yadda xaki xauna lafiya da kowa babu ruwanki da wani kishi na banxa da wofi wanda xe kaiki ga hypertension, kishi dole ne ba ace karki ba amma akwai irin kishin da akeyi bana yanxu da yaxama na hauka ba, kede babu ruwanki don baki taso kinga anayi a gidan ku ba...

Islam ta daga kai, tana tuno irin buga kishin da ake a gidan su, Fatima ta ci gaba da cewa,

"Na ga, ga Ammi nan da Maman Arfat  kamar ya da kanwa haka suke abun sha'awa ba'a taba jin kansu ba ina fatan kina ganewa?!"

Kad'a kai Islam tai tana wasa da yatsun hannunta cikeda nutsuwa. Ya Fati  ta cigaba da yi wa Islam jan hankali akan rayuwar gidan miji ta k'ark'are da,

SAIFUL_ISLAM..💞(COMPLETED✅)Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin