FIFTEEN

1K 93 0
                                    

*A* razane Islam ta jiyo muryar Saifullahi cousin 'dinta yana cewa,

"Hello Islam, dan Allah number DOCTOR SAMEER AMEER( littafi na) malamin physiology 'din ku zaki bani, Kinga an kai Nusrah ne zata haihu a asibitin sa, Kuma wai baya kusa suna meeting ne, ni kuma bana garin, yanzu haka ina kaduna naje duba nuraddeen ne, Wai duk nurses din tsoran kiran sa suke yi, ni kuma da inada number 'din sa, amman babu yanzu. Dan Allah ki turo min please, tunda shine level coordinator d'inku.."

Cikin rawar murya, cike da tausayawa halin da Nusrah take ciki. Tace dashi,

"Eh shine, Bari na turo maka, Allah ya sauke ta lapia. Ameen!"

Cike da hanzari ta nemo number a contact's log 'dinta, ta tura masa, bakin ta 'dauke da adduar Allah ya sauki yayar ta ta lapia.

    'Bangaren Saifullah kuwa a razane ya 'daga idanun sa yana kallon mahaifin sa, cikin rawar murya yace,

"Saki? Daddy saki fa kace."

Ya fada a 'dan razane, jaddada kai Alhaji Faruk yayi alamun tabbacin da gaske yake, cikin rawar jiki Saifullah ya 'kara matsawa kusa da mahaifin nasa, yasa hannuwan sa duka biyun yana rik'o 'kafafuwan mahaifin nasa, sai kace mai neman gafara, gaba d'aya ko Ina ajikin sa rawa yake, tamkar mazari na kad'a shi..Cikin rawar baki yace,

"Dan Allah Daddy kuyi hak'uri, hukuncin ku yayi tsauri, wallahi wallahi Daddy bana zargin Islam, kafin muyi aure ne dai tunda na gan ta a bakin wani joint, shi... shine zucia ta take zaton ko bata jin magana ne, amma Allah bayan nan Daddy wallahi ban 'kara zargin ta ba, ko dana ganta a school dinsu da wani thou nasan shi a wani wajen, Allah banyi mummunan zato akan haka ba, kawai dai bana sakar mata fuska ne, wai ko rashin sakin fuskar zai sa ta hankalta ta de na, k..."

Kafin ya 'karasa Alhaji Faruk ya 'daga mai hannu alamar ya dakata, cikin yatsina fuska yace dashi,

"Daga ganin sarkin fawa sai miya tai dad'i? Kenan daga ganin ta a bakin joint sai kai mata kallon mummunan zato? Wallahi kabani kunya Saifullah, da ilimin ka da komai kake jahiltar abu? Wannan wane irin duhun kai ne da kai? Meyasa da kake zaton hakan baka same ta ka tambayeta ba? Sai kabar abu acikin ranka kana muzguna mata, shashasha, sakarai, sullutu kawai, wanda ilimin sa bai 'kare shi da komai ba sai bakar zucia da duhun kai. Sakar min kafa ni, kafin nasa d'aya na ham'bare ka."

Saifullah yaja baya a hankali yana zare hannuwan sa daga kan 'kafar Alhaji Faruk. Cikin muryar tausaya wa yace,

"Abba dan Allah kuyi hak'uri, wallahi wallahi Ina son Islam yanzu, da 'dinma shed'a..."

"Kar kayiwa she'dan sharri Saifullah, wallahi wannan wata aqidar kace ta daban, andeji kunya wallahi, Allah ya kyauta"

Cewar Hajia Zuwairah, ta 'karasa fada tana zabga masa harara. Shi dai Saifullah hak'uri kawai yake ta basu, gaba d'aya bashi da kuzari, ambaliyar hawaye ne ke reto a kyakkyawar fuskar sa na nadama da dana sani, cikin haka Islam ta fito daga 'daki, batasan da zuwan Saifullah ba, kusa da Haj Zuwairah ta xauna daga 'kasan ta, kafin tace da Alhaji Faruk kanta a 'kasa,

"Daddy barka da rana.."

Murmushi kwance akan fuskar sa yace,

"Barkan mu Islam, kina Lapia?

Kanta a 'kasa tace,

"Alhamdulillah Daddy.."

Saifullah ya zuba mata idanuwan sa yana kallon ta 'kasa-k'asa, ta dauke kai kuwa hade da shan kunu, dan karma ta gaishe shi, Haj Zuwairah ta dubeta tana fadin,

SAIFUL_ISLAM..💞(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now