EIGHTEEN

1.1K 72 0
                                    

"Zan koma 'daki na Baba.."

"Masha Allahu, Toh Allah yasa ki koma a sa'a, Allah ya kad'e fitnah a tsakanin ku, ya baku zaman lapia mai 'dorewa, ya baku zuri'a ta gari, mai 'dimbin albarka, Ameen"

Kanta a 'kasa, cike da kunya tace,

"Ameeen..."

A lokacin kuma Alhaji Faruk suka shigo shi da Abbas, Bayan su kuma Saifullah ne. Da alama 'dakko su yayi daga asibiti, garin kallon Islam da Saifullah keyi sai da yayi tuntub'e zai fad'i, Abbas dake nazarin sa yai saurin rik'o shi yana daria kafin yace,

"Aboki! Easy mana..."

Gaishe su tayi kanta a 'kasa, Abbas yayi musu sallama ya tafi gidah, parlor yadawo daga Aji Mommodu sai Aji Faruk da Saifullah, sai Islam dake gefe, Haj Zuwairah ta fito daga mab'oyarta da Fatma wadda ta haye sama, ita kuma Mami tashiga parlorn tana murmushi kafin tace,

"Sannun ku da dawowa, ya jikin na ka?"

"Na warware first love"

"Masha Allahu! Allah ya 'kara afuwa"

"Ameen" suka amsa baki dayan su

Alhaji Faruk ya ajiye robar ruwan daya kwankwad'a kafin yace,

"Toh sai mu 'dora daga inda muka tsaya ko?.."

"Akan me fa?!"

Cewar Aji Mommodu dake gefe yana ajiye wayar dake hannun sa, Alhaji Faruk ya nuna Islam yana cewa,

"Ta Islam, tunda tace gwara ya s..."

"Tace zata koma 'dakin ta ai, mun gama magana.."

"Alhamdulillah abu yayi kyau, Toh Allah ya tsare gaba."

Alhaji Faruk ya fada, murmushi fad'ad'e a fuskar sa, Saifullah dake kan kujera ya sauka daga kai yayi sujjadar godia ga Allah, abisa wannan daddad'an labari daya doki kunnen sa, cikin hanzari ya mike yana cewa,

"Mungode Allah ya saka da alkhairi, Tashi mu tafi."

Ya karasa yana mai nuni da Islam wadda kunya ta mamayeta ganin idon Saifullah ya rufe ya ma rasa agaban su wa yake, su Haj Zuwairah kuwa baki bude suke kallon sa, Sai itace ma ta 'dan bata fuska kafin tace,

"Wai ni auta ina ka kai kunyar ka ne? Agaban namu kake cewa ta tashi ku tafi? tukunna kai ka kawo ta ne? Toh ba zata tashi ba sai..,"

Aji Mommodu ya dakatar da ita, ta hanyar daga hannun sa da yai mata alamun ta dakata kafin yace,

"Toh tunda yace haka ku bashi itan mana.."

Suka 'kyalkyale da daria dukan su, Saifullah ya fara sosa 'keya da alamun ya manta a gaban su wa yake, Haj Zuwairah tayi murmushi kafin tace,

"Zata je ma gidan barkar matar yayan su data haihu, anan Ganges street dake maitama ko auta ta?!"

Cike da kunya Islam ta 'daga kanta alamar Eh, kafin tace.

"Eh Mami.."

"Yawwa to ga abinci can a dinning, Daddyn su da Abban Khaled ku ci kar yai sanyi dan Allah.."

Mikewa sukai su ka nufi dinning area, Haj Zuwairah ta shiga serving 'din su abincin, Islam tai kitchen tana had'o musu lemonade Saifullah ya shiga, rufe 'kofar yayi ya 'karasa da sauri yai hugging dinta, Sam bata san da mutum a bayanta ba, sai ki tayi an bata wani huge mammoth hug, 'Kara zata yi yai saurin rufe bakin ta da hannun sa, a rad'a-rad'a yace mata,

SAIFUL_ISLAM..💞(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now