SIX

1.4K 95 3
                                    

*GIDAN AJI MOMMODU MELE*

  Shirye-shiryen dawowar Khaled akeyi daga 'kasar Spain, gaba d'aya masu aikin gidan ne keta kara-kaina a kitchen suna had'a masa abinci komai atsare. Lokaci zuwa lokaci Haj Latifa (mahaifiyar sa) kan shiga kitchen 'din don ganin anyi komai a tsare, kuma cikin tsafta.

Haj Latifa na tsaye jikin kitchen cabinet, tana gyarawa wata mai aiki yadda xata hada 'coleslaw'. Humaira tashiga cikin kitchen 'din, tana tafe tana gyara zaman agogon ta dake 'daure a wutsiyar hannunta. Sanya take cikin abaya baka tayi rolling kanta, hannun ta rike da y'ar purse 'dinta.

Hannu tasa ta 'dan gutsiri maras da ake yayyan kashi ta jefa a bakin ta, kafin tace,

"Umma. Zanje gidan su Islam, zandawo kafin a 'dakko Ya Khaled a airport."

Kad'a kai Haj Latifan tayi, kafin tace,

"Karki jima Humaira, nasan halin ku idan kuka had'u da Islam."

"Insha Allah Umma.. Sai na dawo" ta fada tana ficewa daga kitchen din

"Allah ya tsare... "

Sai kuma ta juya wajen Kande mai aiki, tana gyara mata yadda take 'kokarin danna naman akan abun gashi.

"Ha'a Kande ki bari naman yayi marinating kafin kiyi grilling mana haba."

*DR KHALEEL's*

A kitchen Humaira ta tarar da Islam tana tuk'in tuwo, ta rage gas tana jiran ya turara ta sauke shi, da gudu Islam tai hugging Humaira cike da jin dad'i, Humaira ta yatsine fuska tana bin Islam da kallo,

"Ke kam kinason girki, 'karama dake kike girki? bayan ga masu aiki."

Girgiza kai Islam tayi, tana jaddadawa Hari mai aiki ta kwashe tuwon, cikin murmushi tace da Humaira,

"Babes, wallahi tun banaso sai da na koya, Ammi tace hakan nada kyau idan nayi aure na huta, Ai kuwa tuni yanzu kinga yadda na iya abinci kala-kala kuwa?"

Tabe baki Humaira tayi, kafin tace.

"Hu'uhm! Ni kuwa na tsani girki, kuma idan nayi aure masu aiki Umma xata dakko su dinga yi mun"

Kad'a kai kawai Islam tayi, taja hannun ta sukai sama, dakinta suka shiga, Animation cartoon ta saka musu na 'princess and the frog'. Suna cikin kalla Lee tazo, nan suka kafa dabar hirar school,  zancen auren su Hidaya ya shigo, Humaira ta tsunture da daria tana rufe baki, kafin tace.

"Naga mazajen su Hafsat a album na 'daurin aure, wannan ai sun haife su."

Lee ce ta amshe tana,

"Maganin su kenan, sun janyo at early age anyi musu aure."

Islam dake gefe ta katse su tana daga hannuwa,

"Abeg abeg, enough. Su ai yanzu sun huta tunda sunyi auren su."

Lee da Humaira suka tafa, suna kyalkyala daria, kafin Lee tace.

"Kowa zeyi ai, ni kin tunomin ma Dawood ya isheni da maganar aure wallahi, nace mishi ni ba yanzu xanyi aure ba yaki yadda"

Humaira ta kwashe da daria,

"Wallahi nima Yaseer ya isheni, nace mi shi sai na zama accountant tukun sa.."

Lokacin jin Islam ya dauke, tuni ta fada duniyar tunani. Ita kam haka xata xauna ba xatai aure ba kenan? Shin me tayiwa maza da ba sa sonta haka?, Ta jima tana tunani sai da zazzafan dundun da Lee ta zuba mata a baya ya dawo da ita dunia. Cikin daria Lee tace,

SAIFUL_ISLAM..💞(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now