SEVEN

1.4K 89 0
                                    

Gyaren murya Ya Bala yayi, yana mai nuni da su Haj Karimatu. Da yatsan sa na biyu dake hannun daman sa, cikin muryar fushi dake tattare da damuwa yace,

"Hakika kun bani mamaki, yadda na 'dauke ku, ashe kun xarta hakan, wannan wacce irin musibace? Shin kuna tunanin duk abunda kuke yi Allah baxai kama ku da laifi ba ne ko kuwa? Wane irin haukan kishi ku ke yi ne ? Da ya xarta tunani? Ni da ku, shekarun baya na ja muku kunne, had'e da tausasa zuciyar Khaleel, ya hakura ya dawo da ku 'dakunan ku, dukkoda yadda kuka 'kulla sharri akan yarinyar da batada masaniya akan hakan, daga ni sai ku, sai su Khaleel, aka rufe maganar ba'a bari tafi to ba. Sai daga baya na gane ba kishi bane, tsantsar mugun tace.. Tirr! Da hali irin naku wallahi."

Shiru yayi, gaba d'aya ya rasa mai zai sake cewa, ganin haka, yasanya Inna Bilkisu dake gefe cewa,

"Duk dan akan kishi kuke hakan ko? Shinma menene kishi? Tunda naga kamar bakusan ma'anar sa ba, da yadda ake yinsa. Shi kishi wani yanayi ne na so  da kauna da burin kare abun da ake son daga kamuwa da cuta. Ana kishin kasa kuma ana kishin sana'a da abokan zama.. Duk inda akwai kishi mutane na ganin cewa akwai so, har ma wasu kan ce "kishi so ne". Duk dan Adam bai cika mutum ba sai ya kasance yana da kishi. Ko dai ya kasance yana kishin kansa, kishin iyalinsa da dai makamantansu.,

"Hausawa na cewa "kishi kumallon mata." Amma a zahiri ba mata kadai ke da kishi ba, har mazan ma suna da shi. Mutane da dama na ganin cewa maza sun fi mata kishi, kawai dai matan sun fi nunawa ne. Wannan abu ne da za a iya muhawara a kai. In har hakan ne, akwai abubuwa da dama da ke silar hakan. A addinin musulunci da kuma al'adar mutanen Afirka da yankuna da dama, maza ne suke auren mace fiye da daya. Su kuma mata miji daya kadai suke aure. Wannan shi ke sa mata su yi ta jin tsoron kawo musu abokiyar zama wadda ake kira kishiya. Kalmar kishiya kanta bai dace ana fadar ta ba, kasancewa zama aka zo yi tare da miji daya ba wai wasa ba. Ita kalmar ke kara wa mata da dama tsoro cikin zukatansu da zarar an furta ta. Sannan kuma maza da dama sukan fara wulakanta uwargida idan amarya ta zo. Ita da 'ya 'yanta su zama ko oho. Su ma amaren su yi ta jin dadi cewa ana wulakanta uwargida, ba sa tunanin cewa su ma idan aka yi sabuwa, haka za a yi masu. Hakan na matukar tsoratar da mafi yawancin mata, har ma ka ji suna cewa "ba kishiyar ake tsoro ba sai sharrin ta,

"Yarda da amincewa na da matukar muhimmanci a dukkan tarayya, musamman ma ta aure. Da zarar babu yarda a cikin zaman aure, zargi zai shigo ciki kuma ba za a taba samun zaman lafiya ba. Ya kamata mu rika gina aure bisa yarda da amincewar juna, don hakika su ne gishirin zaman aure. Rashin yarda ne ke kawo rashin jituwa har ta kai ga rikici, a wasu lokutan ma har da kisa,

"Kusani cewa, Kishi wata dabi'a ce da Allah ya halicci mata akanta, Nana A'isha tana cewa : "Ban taba yin wani kishi ba, irin kishin da na yiwa Khadijah, duk da cewa ban taba ganinta ba, saboda yadda na ji Annabi s.a.w yana ambatonta" Bukhari 1388, Kishi mai tsafta, shi ne : kishiya ta yi rige-rige da kishiyarta, wajan kyautatawa mijinsu, Akwai Jahilci : ta yadda mata da yawa suka jahilci, hikimomin da suka sa Allah ya yi umarni a kara aure, kamar;rage yawan zawarawa da 'yammata, da kuma yawaita zurriyar Annabi S.A.W.,domin da za su kalli wannan da kishinsu ya ragu. Mummunan zato, yawanci uwar gida tana tarbar amarya da mummunan zaton cewa za ta rainata, haka ita ma amarya ta kan zo da mummunan zaton cewa ba za su yi zaman lafiya ba da uwar gida, wannan sai ya sa daga zarar sun hadu babu wuya sun yi rigima.Amma idan da ace kowacce za ta tarbi kowacce da kyakykyawan zato, har ta ga kamun ludayinta da ba'a samu matsala ba.,

"Rashin adalci daga wajen namiji, yawanci maza su kan karkata zuwa amarya, wannan sai ya haddasa fitina, saboda uwar gida za ta ce ba ta yarda ba. Amma idan kuka duba anan zaku ga cewa, shi maigidan ku sam ba haka yake ba, hakika yana k'ok'arin adalci a tsakanin ku, Saidai abin da ya kamata mata su fahimta shi ne : babu yadda za'a yi namiji ya hada mata biyu face sai ya fi son daya, Annabi s.a.w. ya zauna da mata tara kuma ya fi son Nana A'isha, har ma mutane sun fahimci haka, wannan ya sa idan za su yi masa kyauta, sukan 'kirkidi ranakun da yake dakinta, don sun san kyautarsu za ta fi karbuwa a ranar, don haka idan kika ga mijinki ya fi son kishiyarki, ki yi masa uzuri kar ki tada fitina, saidai abin da sharia ta hana shi ne, rashin adalcin ya fito a hidimomin yau da kullum. Wanda ku Kan ku kunsan maigidan ku na kamanta adalci a tsakanin ku, sannan akwai Munafukai, masu cece-kuce, idan da ace kishiyoyi za su daina daukar guzuri-zoma, ta yadda idan suka ji magana za su tabbatar da ita kafin su yi hakunci ga kishiyarsu da hakan ya rage kawo matsaloli. Amma ku duk kunyi fatali da wannan idanuwan ku sun rufe, kun 'dauki zugar shed'an kun d'orawa zuciyar ku, kuna aikata shirka, domin wallahi had'a Allah da wanin sa shirka ne, zuwa wajen duba, da yan tsibbu suna gaya muku 'karya da gaskia, kuna zama akai, kun cusa mummunar 'dabi'a aranku, kun 'dau wani qudri na ganin kunyi mai yiwuwa kun fidda wasun ku daga gidan, to ku gayamin da ta tada rigima kar a auro ku, Allah ba za'a yin ba, dandai bakusan k'ok'arin da baiwar Allahn nan tai muku bane da har ta bari aka auro ku,

SAIFUL_ISLAM..💞(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now