ELEVEN

1.3K 103 1
                                    

Tuni an sallamo Karimatu daga asibiti, domin kudin jinya ya 'kare. 'Yar wayarta tuni ta siyar da ita, da wanda 'yayanta suka tallafaa mata dasu duk sun 'kare a magani. Kamar kullum a sheme take kwance kamar shekararriyar saniyar dake jinya. Lokaci zuwa lokaci takan saki murmushin takaici, da alama dai mutuniyar taku tuna baya take yi.

Wata waya 'kirar nokia wadda akewa laqabi da rakani kashi ta 'dakko a gefan inda take kwance, tasha 'dauri da kyauro, gefe da gefe kuma an nane da super glue. Can 'k'arshen wajen chaji kuwa an nannade da salatef (seal-tape). Duk screen 'din ya faffashe kana hango cikin wayar, madannan sun goge sai da biro aka zana kowacce lamba. Dakyar ta iya gano lambar Sidiya, takira ta yafi sau goma kafin ta 'dauka dakyar,

"Toh baxan 'kara ba, sai kinzo."

Shine kawai abunda Karimatu tace, ta ajiye wayar a gefe. Can wajen bayan minti talatin sai ga Sidiya tana cika tana batsewa, kallo 'd'aya taiwa 'yan gidan ta 'dauke kanta. Hajia dake gefe ta tab'e baki kawai tana ci gaba da 'kulla alala a leda. Kamar yaki Sidiya tashiga 'dakin da Karimatu take tana wani yatsina fuska, gashi ta tsaya 'kerere akanta. Ganin ta yasanya Karimatu 'dan muskutawa ta gyara zaman ta dakyar.

"Ki zauna mana Sidiya."

"Kai gaskia a'a, kin ji wani shegen zarni dake tashi a jikin ki kuwa, kuma fa nagaya miki kidena kirana da yawa, fisabilillahi baban Gali(mijin ta) sai fad'a yakemin, nifa gaskia ba zaki kashemin aure ba Karime"

Shiru kawai Karimatu tayi, tana sauraron masifar da Karimatu ke zazzaga mata, babu ma Yaya da take kiranta a da, sai Karime gatsal. Tana cikin tunani, muryar Sidiya ta dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi.

"Wai me zan miki ne da tun asubahi kike dokawa waya ta kira?"

Cikin taushasshiyar murya Karimatu tace,

"Da..Da..Dama kudi zaki aramun asiyo min gurasa da..."

"Kutma.. Cab lalle ke dinnan ma, kiji da kudin lapiar ki ma a'a sai ta biyewa dad'in baki? To wallahi bani dashi, ni idan kin samu ma ki biyani dari uku na ta shekaran jia, bazan iya da cin bashin ki ba."

"To ko zaki aiko mun da abincin da ki kai?"

Kyakkyawar harara Sidiya tayiwa Karimatu, kafin ta buga zani kawai, ta fice abinta, girgiza kai Karimatu kawai ke yi, ganin yadda Sidiya ta juya mata a baya, ada itace gatanta, ta'dauke 'dawainiyar 'ya'yanta ma gaba ki d'aya. Tana cikin tuna baya, Alawiyya tashiga 'dauke da kwano sai 'kamshin man 'kuli ne ke tashi. Shinkafa ce da wake na gidan asabe mai abinci.

"Gashi inji Hajia.."

cewar Alawiyya, ta duk'a ta ajiye tafi ta.  Cikin hanzari jiki na bari Karimatu ta bude kwanon abincin, shinkafa da wake da yasha man 'kuli da yajin tafarnuwa, sai yankakken tumatir da albasa, ga maggi guda d'aya a gefe. Kamar mayunwacia haka Karimatu ta shiga 'durawa cikinta abincin, tana kad'a kai da alama yai mata dadi. Ashe Hajia duk taji yadda sukai da Sidiya, uwa mai dad'i, ta ciri dari biyu cikin kudin alalar tabawa Alawiyya ta siyo mata abincin. Ko kad'an ba tabada sigar da su Alawiyya xasu rena Karimen ba, dukkoda tarin abubuwan da ta yiyyi musu. Tana gama ci ta koma ta kwanta da 'd'ayan barin, domin 'barin hagun ta baya aiki sam. Shiysa takan sau fitsari wani lokacin a zaune idan robar fitsarin ta goce.

Gaba d'aya hakurin Khaled ya 'kare, domin duk kawaicin da yake musu yaga basa ganewa, a bashi matar sa an 'ki, tun shekaran jia aka kawota amma ko fuskarta 'kememe an haramta masa ganin ta, zaune yake akan kujerar 'dakin sa shida Saifullah dake sketching wani zane . Sake sakin tsaki Khaled yayi a karo na ba adadi kafin ya turo baki gaba cikin tausayawa yace,

"Saboda tsabar an tsaneni ba, Wannan ai rashin adalci ne."

Saifullah daya gaji da mitar Khaled ya mike yana tattara kayan sa zai bar masa 'dakin, cikin azama Khaled ya riko shi yana rausayar da kai,

SAIFUL_ISLAM..💞(COMPLETED✅)Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum