THREE

1.9K 102 1
                                    

*WASHE GARI*

   *D*a wuri aka sallamo Haj Aysa suka rankayo dukkan su suka koma gida, kafin nan babu yadda dr Khaleel bai yi ba da Haj Karimatu taje asibitin taga yaran tare da duba Haj Aysan amma kememe taki, ta kafe akan batada lapia ba zata iya fita ba, to hakama Yafendo itama bataje ba, nata uzurin ta bayar, a dole dr Khaleel ya kyalesu domin shi mutum ne da bayason rigima, ba kuma yasan hayaniya kwata-kwata,

Shi yasa kawai ya kyale su, saboda idan ya matsa suje, ba suje d'in ba to rayukan mutane da yawa ne xasu b'aci, saboda babban mataki yake yankewa idan ransa ya kai 'kololuwar b'aci,

Shi yasa farkon rigimar da Karimatu da Yafendo sukai masa, makota ne suka raba su, yana xuwa da labarin yazo kunnen sa, ya dankarawa kowaccen su saki d'aya, dama ita Karimatu ya taba yi mata d'aya lokacin da taiwa Safa 'yar Hajia Aysa sharri.

Gayawa mai karatu yadda aka sake gyara b'angaren Haj Aysa bata lokaci ne, domin kunsan dai yadda gidan yake, kuma kunsan yadda Dr Khaleel yake burin samun d'a namiji, Toh Allah ya cika masa burin sa, d'aki d'aya a 'kasan ta aka gyara shi da gadajen babies maza komai blue, abun dai sai wanda yagani kawai.

Cima kala-kala Dr Khaleel yasa ake jibgewa a gidan, ga abokanan sa da matan su sai kara-kaina suke agidan, sosai Haj Aysa ke samun kayan barka, tun abun nabata mamaki harta dena,

A kuma ranar ne Dr Khaleel ya tura zungureriyar mota taje Gazarganu Road Area: Bulabulin, Maiduguri, Borno State,Nigeria. Asubar fari tayo lodin yan uwan Haj Aysa, domin suma sunce baxa'a barsu a baya ba,

Tuni parlor ya kacame da 'yan uwa sai yarawa suke yi ana cin cima kala-kala, jarirai kuwa sai nan nan ake dasu, a yinin ranar dr Khaleel yayi zarya agidan nan yafi a 'kirga,

Kuma duk dan dai ya sake ganin yara sa ne, duk universities dayake lecturing ya bawa students kowa kyautar maki biyar, yayi sadaqa kala-kala a masallatai,

Yaya Bala ma yazo da matan sa duka su ukun, Haj Halima da Haj Nafeesa, da Haj Nabeelah. Haj Halima nada 'ya'ya biyar maza uku mata biyu, da Mubassher da Mudasser da Mu'utaseer sai matan da Aneesa da Meena sai 'ya'yan Haj Nafeesan su hudu ne kuma duk maza ne Kamaludden, shamsudden, Nuraddeen da Najibulla sai Haj Nabeelah ita matan ta biyu namiji d'aya. Saifullahi, Amina sai auta Nadia.

Ba laifi gidan Yaya Bala yafi d'an zaman Lapia amma suna d'an tab'a nasu ruguntsumin, saboda duka kishin su na ilimi suke yi, babu hayaniya sai dai ayi gogayya ta nuna fini da kaza na fiki da wannan, sai 'dan abunda ba'a rasa ba na gutsiri tsomar yau da kullum, Yaya Bala 'ya'yan sa goma sha biyu,hudu daga ciki mata ne wanda dukkan su sunyi aure Nadia cema bata jima dayi ba.

Wanda sauran takwas d'in duk maza ne, biyu daga ciki sunyi aure, hud'u daga ciki agidan Dr Kabeer suke da xama, biyu na aiki a company din baban su na canji wato mudasser da mu'utaseer, biyun kuma d'aya banker ne anan zenith bank wato kamaluddeen dake abujan sai saifullahi dake lecturing a baze university, lecturer ne na Mbbs wato medicine.

Sauran hud'un kuma d'aya na lagos mubassheer kenan mijin Safa 'yar gidan Haj Aysa, da Shamsudden sune a lagos, Nuradden kuma yana aiki a kaduna, sai engineer najibulla dake kasar Manchester yana aikin wani company wanda shine mijin Marwa 'yar gidan Haj Aysa..

Toh abun dai sai sam barka kawai, amma wasu daga cikin iyaye mata na mazajen su Safa basu so auren ba, Haj Halima da Haj Nafeesa, hak'ik'anin gaskia saboda wani kuduri nasu na daban,

Inna Bilkisu zaman ta ya koma hannun Yaya Bala, tun mutuwar mijin Hansa'u kanwar su Dr Khaleel. Ya rasu ya barta da yara biyar wanda uku daga ciki maza ne biyu kuma mata ne.

Akwai Shema'u, wadda ta canxa sunanta xuwa shamie baby, acewarta wancen sunan yan kauye ne, da tana da wayo akai rad'in sunan ma da babu abunda xai hanata canxawa, sai Aysha wadda akewa laqabi da sholey, sai mazan Kabeer Kb, da Khaleel wanda yaci sunan Dr Khaleel ake ce dashi Ibrahim sai autan su Yusuf.

SAIFUL_ISLAM..💞(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now