TWO

2.1K 114 1
                                    

*SHAFI NA UKU (3)*



*B N A*..



     Elizabeth Arden's hostel...

*Z*aune Islam ta ke, hannun ta rik'e da littafin chimamanda mai suna 'purple hibiscus', kasancewar dare ne tuni yawan cin 'yan dakin sunyi bacci, da yake kowan ne d'aki mutum shida ne ciki. Da Ita kanta a cikin d'akin sai Lee da Hafsat da suke uba d'aya, sai Hafsat Rano da suke kira da HR, sai kuma Fatma bichi da suke kiranta Zarah, sai Iffy kawar Hafsat kanwar Islam sune a d'akin su 6, gabas da yamma kudu da arewa na dakin ko Ina gado biyu ne inda yayi making 6 bed kenan.

Had'add'an d'aki ne kai kace gida ne idan ka shiga, harda d'an parlorn su da tv a ciki, can gefe kuma study ne da bookshelves ajiki, kowa gadon sa da kalar sa, da mini cooler fridge kowan ne da nasa, ga kuma yalwataccen band'aki wanda yaji komai abun dai sai sam barka kawai, Domin makaranta ce mai karshen kyau, kuma ta amsa sunan ta don kwarai matuka suna samun karatu, kama daga na boko zuwa arabi ciki harda k'arin karantar harshen faransan ci (French).

Kasancewar shi harshe na biyu da ake ji dashi a duniya bayan English saboda mahimman cin sa a duniya ko a international court of crimes na duniya daga French sai English kawai ake yi. Wannan kenan.

Haleema Sameer Ameer 'kawar Islam itace ta fito daga band'aki, da alama wanka tayi dan gashi nan tana tsane kanta da karamin towel kafin ta d'akko dryer tana drying gashin kanta, duban Islam take da gaba d'aya hankalin ta na kan littafin da take karantawa, da alama ma ba ta san Haleeman ta shiga band'aki ba balle kuma fitowar ta.

"Aikin dai kenan" cewar Haleema ta ajiye dryer tana k'ok'arin daure gashin ta da ribbon..

"bae boo"cewar Islam tana k'ok'arin cigaba da karasa karatun ta,

"Wallahi baki isa ba"Lee ta fad'a tana wafce littafin daga hannun Islam,

"Ki dinga hutawa dan Allah, Shi kenan ke bakida aiki sai karatu ne?ko gajia bakya yi, beside ke fa ba Art student bace for heaven sake.."

"And so, reading is one of my fave hobby yarinya" Cewar Islam had'e da rolling idanuwanta cike da tsoka na,ta mika hannunta ta kwace littafin ta, hade da saurin mikewa tabar wajen Lee.

"Zaki dena ne..Ni bama wannan ba bari na dakko physics ki kara sa coaching dina"

Kad'a kai Islam tayi, ita kuma Lee ta tashi ta shiga study wajen karatun su inda books d'insu yake..

Tashin ta keda wuya Hafsat ta shigo d'akin tana wake-waken ta, sosai gaban Islam ya shiga fad'uwa don batasan yau kuma da wanne kalar rashin mutunci Hafsat din zatai mata ba.

Bata karasa tunanin da take ba, Hafsa ta dire mata plate akan littafin ta, har cheese na fallatsuwa a idanun Islam, da sauri Islam tasa bayan hannunta tana goge idanun ta, gashi tana da ciwon idanu lokaci d'aya ya karade ya zama ja..

Kwan chewing gum Hafsat ta saki guda uku lokaci d'aya ji kake k'as-k'as-k'as kamar tsohuwar karuwa. Hannu d'aya kuma tana danna waya, gashi an hana amfani da waya a sch din. Idan aka gani ma seizing ake yi, amma Hafsat da Hidaya asace suka zo da tasu, bayan ko agidah ma Dr khaleel bai basu daman rike wayar ba. yace kowannen su sai ya gama secondary school zai rike waya,

"Reheat that for me.."cewar Hafsat ga kuma harara tana makawa Islam din,

Islam bata ce komai ba ta ajiye littafin ta a gefe, ta mike da plate d'in a hannunta cheese burger ce akai, tafiyar daba tayi taku goma ba ta isa ga microwave d'in su dake gefen tv stand, tana k'ok'arin saka plate d'in aciki Lee ta fito daga study room.

SAIFUL_ISLAM..💞(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now