SIXTEEN

1K 76 0
                                    

'Difff...... Numfashin Saifullah ya 'dauke, wata razananniyar 'kara Islam ta saki tana 'dora hannuwa akai, Alhaji Faruk ya kira Mami ta janye Islam. Su kuma shi da Aji Mommodu suka 'dauki Saifullah kamar gawa aka 'dora shi akan kujera, ruwa aka yayya fa masa amma ko motsi ba yayi, Haj Zuwairah sai kai da komowa take yi a parlorn, tana adduar Allah ya tashi kafad'un Saifullah, ahankali numfashin sa ya dawo amma iya ciki kawai, cikin gaggawa suka 'dauke shi sai asibiti, dayar motar kuma Haj Zuwairah ce da Islam sai Fatima yayar Saifullah itama da tsohon ciki, haihuwa ko yau ko gobe. Ana shigar da shi asibiti likitoci sukai kansa, suna bashi temakon gaggawa, ai kuwa da taimakon Allah da oxygen da aka sanya masa yafara numfashi normal, amma jikin nasa is weak, Dr Jalaludden, shine likitan da ya duba Saifullah, a tsaye ya samu su Daddy sunyi cirko-cirko, Islam kuma na daga can baya ta kifa kanta tana kuka, Dr jalaludden ya nufe su yana murmushi, Aji Mommodu yai hanzarin cewa,

"Dr ya jikin Saifullah, ya farfad'o kuwa?"

Dr ya zare face mask din dake hancin sa kafin yace,

"Alhamdulillah ya farfad'o, sai kuyi wa Allah godia, dan gaskia condition dinsa bamu saka ran numfashin sa zai dawo normal ba, saboda sanda kuka kawo shi har ya shiga coma stage, Toh kuma dai Masha Allahu, numfashin sa yadawo normal, amma acikin ku waye mahaifin sa? Inaso muyi magana ne.."

Aji Mommodu yace,

"Nan duk iyayen sa ne, waccen yayar sa ce, ta 'k'arshen can kuma matar sa ce."

Ya 'karasa fad'a yana nuni da su Fatma da Islam. Likita yace,

"Allah sarki, Toh idan ba damuwa inason muyi magana da ku biyu mazan."

Kad'a kai su kai, suka bi bayan sa har ofishin sa, guri ya basu suka zauna, kafin shi ma ya zauna yana duban su da kyau, sannan ya fara magana da,

"Toh kamar yadda na fada muku Saifullah yana cikin critical condition gaskia, jinin sa ya hau da yawa, sannan akwai alamar dimbin damuwa atare dashi, ba ma wannan kad'ai ba, harda chronic ulcer. Garin yaya kuka bar matashi haka da wa'ennan tarin cututtuka dake barazanar 'karar da rayuwar sa akoda yaushe?"

Aji Mommodu ya dubu Alhaji Faruk, sukai kallon kallo, kafin Alhaji Faruk yace,

"Hau hawar jini fa kace likita...?"

Dr Jalaludden ya jaddada kansa alamar tabbatar da zancen da ya fada hakan yake. Aji Mommodu yai ajiyar zucia kafin yace,

"Amma likita a iya sanin mu babu wani abu da yake damun Saifullah, da har zai sanya kansa cikin damuwa haka.."

Alhaji Faruk ya girgiza kansa yana kallon agogon hannun sa, kafin yace.

"Toh ko zancen Islam ne?"

Dr Jalaludden yai hanzarin cewa,

"Wacece ita Islam 'din?"

"Matar sa ce, wadda muka nuna maka ita a waje..." cewar Aji Mommodu.

Dr Jalaludden ya jaddada kai kafin yace,

"Ko zan san meyasa matar sa ta zama wani 'bangare a sashen shiga matsalar sa?"

Alhaji Faruk ya hangame baki zai magana, Aji Mommodu yai hanzarin cewa,

"Da akwai y'ar matsalar da aka samu ne, shine muke tunanin rabuwar su zai fi, akan suci gaba da zama a inuwa d'aya.."

Dr Jalaludden yai shiru, yana kallon su, ya cire biron dake bakin sa, Daga kai yayi sama, kafin ya sake mai da duban sa gare su yace,

"Shin matsalar babba ce da har kuke maraba da ita? Yaron ku ya kamu da rashin lapiar dake barazanar farautar rayuwar sa, why.. why?"

Daga Aji Mommodu har Alhaji Faruk shiru sukai, suna raba idanuwa, dr Jalaludden ya saki dan karamin tsaki, kafin ya sake cewa,

"Toh ni dai abun da yasa na kira ku kenan, idan da hali dai ku ba shi matar sa pls, idan lefi yayi ku ke neman hukunta shi haka kuyi hak'uri dan Allah, rayuwar yaron ku itace gaba da komai agare ku yanzu, kuyi tunani akai Alhaji.."

Yana gama fad'a ya mike yana duba agogon dake daure a wutsiyar hannun sa, kafin ya sake cewa,

"Bari na koma wajen sa, maybe ko ya farfad'o.. Excuse me pls"

Cewar dr Jalaludden ya fice, rataye da stethoscope. Aji Mommodu ya dubi Alhaji Faruk, su kai kallon kallon, 'Ina mafita?'. Alhaji Faruk yai ajiyar zuciya kafin yace,

"Ya kake ganin za'ai, an ya idan muka tilasta yarinyar nan bamu cuceta ba?"

"Gaskia kam, sai ya d'au dangana, komai 'dan hak'uri ne, dama ba komai da kake so kake samu ba, akwai hills and valleys a rayuwa.. Allah ya zabi ahunda yafi alkhairi.."

Cewar Aji Mommodu, ya fad'a yana jinjina kansa, Alhaji Faruk yace,

"Kwarai kuwa, zab'in Allah shine mafificin alkhairi.. Muje Modu.."

Mikewa sukai, suka fita.. Yadda suka bar su Haj Zuwairah haka suka gan su yanzun ma, Islam still kanta a 'kasa, Dr Jalaludden ya fito yana zare safar hannun sa, kafin yace.

"Toh.. Alhamdulillah, Saifullah ya farfad'o and yana tambayan wata Islam, so please Islam taje kafin mu san matakin da zamu sa shi a kai.."

Haj Zuwairah ta dago Islam itada Fatmah, zasu shjga 'dakin dr Jalaludden ya girgiza kansa, alamun a'a, kafin yace.

"Mama kuyi hak'uri, Islam first,before anything else.."

Jaddada kai su kai, suka ja baya, ita kuma Islam ta shiga dakin gabanta na tsananta fad'uwa, ido hudu sukai da Saifullah, ya miko mata hannun sa a hankali , dr Jalaludden dake kallon su yai wani shegen murmushi, kafin ya janyo musu 'kofar ya kulle..

'Karasawa tayi, taki kallon sa bare hannun daya ke miko mata, ta mai da kallon ta ga window, a hankali tace,

"Ya jiki?!"

"Da sauki.."

Ya furta can 'kasan mokoshi, kallon sa tayi, idanuwan su suka sarqe dana juna, ta 'dauke da sauri saboda kwarjinin da yai mata, shi kuma ya shagala da kallon ta, mikewa tai zata fice ya rik'o hannunta, murya 'kasa kasa yace,

"Please stay...Please...Islam'"

Mutuniyar ku har cikin magudanar jininta taji dad'in yadda ya furta sunanta, ya ja laaam 'din kamar wani balarabe, dan bata rai tayi kafin tace,

"Me zan maka ne?"

"When you leave, I swear I can't breathe, Do you really care Islam?"

Kwace hannun ta tayi, zata gudu yai saurin jan mayafinta, luu tafada akan sa, baiwar Allah ta shiga neman kiciniyar kwace kanta, mutumin ku ya hana, ya kara mannata a jikin sa, yana shakar kamshin jikin ta, tsoro ya kama Islam jin saifullah na ajiyar zucia, zata tashi ya sake damke ta ajikin sa, cikin kunnenta ya shiga rad'a mata,

"Please calm down, gimme just 3mins.."

Shiru Islam tai, tana lafe a kirjin sa, jin kamar za'a turo k'ofa ya sa ta, saurin kwace kanta, suka shiga kallon kallo, ya saki lallausan murmushi, ta yatsina fuska tana kallon gefe kafin tace,

"Kar ka sake yi wa matar wani haka"

"Matar wani kuma?"

Yafad'a yana ware idanuwa, jaddada kai tayi alamun da gaskiyar ta ta fadi haka, murmushi kawai yayi, kafin ya sa hannu ya dafe saitin zuciyar sa, cikin lumshe idanuwa yace,

"Kece maganin zuciata Islam, I love you more than life itself. Pls kakki bari a raba auren mu Islam, nasan ada nayi kuskure amma wallahi yanzu na gyara, fiye da tunanin ki. Dan Allah ki bani last chance...Kinji?"

Yatsina fuska  tayi, duk da har cikin zuciar ta takejin dad'in kalaman sa amma afili kuwa kemad'agas tayi, tamkar bata sauraren sa, adai-dai lokacin akai knocking, Dr Jalaludden ne ya shiga shi da su Mami.....

SAIFUL_ISLAM..💞(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now