NINE

1.3K 91 0
                                    

D'an k'aramin tsaki yaja, tare da harar hanyar da yaga tabi sannan ya juya shima ya tafi, yana tafiya yana mulmula wajan da suka yi gwaran dan ba k'aramin zafi yaji ba shima. Kai tsaye bedroom d'insa ya nufa ya cire kayan  jikin sa, ya zamana daga shi sai boxer da bak'ar vest ya nufi bathroom dan yin wanka, haka kawai yaji yana mamakin yarinyar, wato su mata idan suna so suyi wani abun da kai duk ta hanyar da suka san zasu samu abin sai sunyi, yana kyauta ta  zaton wannan yarinya ta bigesa ne kawai dan ta tab'a jikinsa, kamar yadda yasan mata suna sha'awar yi masa hakan dan dai baya basu fuska ne kawai.

A 'bangaren Islam, kuwa da gudu ta shiga gida duk a tunanin ta zai biyo ta gashi unguwar babu mutane kartaje ya danneta ya cuceta, tunda taga ita haka samari da magidanta suke yi mata, wani kallo na a huta da ita, ba wai kallo na kauna ko soyayya ba bare akai ga yin aure.

Numfashi taja mai tsawo tare da furzar da iskar da ta shak'o tana k'ok'arin warware tufk'ar da tayi ma gashinta, cilli tayi da ribbon d'in a kan gado sannan ta karasa ta d'akko towel ta d'aura ta nufi wajan madubi ta na kallan fuskarta zuwa sassan jikinta da inda sukayi gware da Saifullah, ta mulmula gurin yafi sau biyar kafin ta murgud'a baki tace a fili.

"Wallahi da ace inaji da rashin kunya babu abinda zai hanani yiwa mutumin can ita, dan iskanci kana ganin mace na tafiya baka sani ba matar aure ce, ko budurwa ko kuma bazawara kawai kazo ka bigeta dan salan iskanci, hmmm wallahi kaci sa'a da babu abinda zai hanani sharara maka mari a duka kumatunka sakarai kawai.'"

Tayi maganar tana yatsina fuska tamkar da wani take yi a wajan, ta d'auki comb ta shiga toilet ranta duk babu dad'i babban haushinta yadda boobs d'inta suka tab'a kirjinsa wannan abun yayi mugun b'ata mata rai sabida gani take kamar ya sake rage mata farashi. (Wa yaga sakarai).

Hutun mid semester suka samu, a lokacin kuma saifullah ya gama sati ukun sa na camp, ya tafi Lagos. Duk meyiwuwa yayi kan yakoma Lagos yayi one year service d'insa abu yakiyi, place of primary assignment d'insa still Abuja ne. Nan SMEDAN branch dinsu na wuse. Lagos Islam tayi tafiyar ta hutu, a lokacin Saifullah shima ya koma gida kafin ya dawo ya fara ppa d'insa. Unguwa d'aya suke gida biyar ne tsakanin gidan Ya Bala dana su Saifullah. Su saifullah idiroko 12b, su Ya Bala kuma 17b.

*LAGOS IDIROKO*



Haka suka ci gaba da fita motsa jiki anan lagos 'din. kullum shi Saifullah yana ganinta ko zai tafi ko kuma ya dawo, yarasa wane irin naccacciya ce, acewar sa da ganin sa saboda shi tazo lagos 'din. sab'anin ita da tun ranar da abin nan ya faru tsakaninsu a Abuja bata sake had'uwa dashi ba, sai wasu mazan daban wad'anda suke tare ta a hanya suna nuna mata wasu banzayen d'abi'u amman bata basu dama, Saboda yanzu itama tsoro takeji kar wani ya lalata mata rayuwa, daddyn su yayi mata aure da abokinsa kamar yadda aka yiwa su Hidayya da Hafsat 'yan uwanta.

Yau dai kam tare suka fito exercise d'in wato Saifullah da Khaled, jere suke suna d'an yin gudu kad'an-kad'an suna 'yar hira cikin tsantsar mamaki Khaled ya kalli can gefensa inda yake hango wata kamar Islam wadda suke tare da Riri ,sai ture-ture suke yi duk sun takurawa kansu wannan tana cewa ana tureta wannan na cewa Islam na takata dan kar su wuce junansu. Sake murza idanunsa yayi tare da kad'a kai ya kalli Saifullah tare da cewa.

'"Waccan yarinyar kamar Islam.'"

'"Wacece islam?"

'"Gata can nasan ta a abuja 'yar gidan makocin muce.'"

Mtscew Saifullah yaja tsaki, jin abinda Khaled ya fad'a, wai 'yar makocinsu a can abuja amman shine yake ta wannan fara'ar tamkar yaga wani abun daya shafesu. Kamar ance ya juya Saifullah ya kalli inda Khaled ya nufa kawai sai yaga wannan yarinyar ce da ta bigesa, wane tukukun bakin ciki ne ya tokare masa makogaro? Ya tab'e baki. tare da ci gaba da abinda ya fito dashi har ya nufi gida ba tare da ya tsaya Khaled d'in ba, kasan cewar besan lokacin da zai gama magana da 'yar makocin tashi ba.

SAIFUL_ISLAM..💞(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now