THIRTEEN

1.2K 86 1
                                    

Haj Zuwairah ta mike tana gyara zaman gyalen ta, kafin ta juya ta dubi Islam dake zaune a gefan ta a 'kasa, cikin murya mai bada umarni tace da ita,

"Auta ta, had'a kayan ki a akwati da duk abunda zaki buk'ata, zamu tafi gida na ne, idan kuma zaki bar sauran a zo a kwasa daga baya to, amma dai duk abunda kikasan zai miki amfani ki 'dakko kinji?"

Cikin sauri Islam ta mike tsaye, tana 'daga kanta, cike da ladabi ta furta,

"Toh Mami, Barin 'dakko."

Tana gama fad'a ta shige 'dakin 'kasa, Haj Zuwairah ta 'kara mamaki ganin dama Islam din har yanzu tana kwana a 'kasa kenan ita kad'ai? Jaddada kai tayi, Saifullah dake gefan Mami shima mikewar yayi ya haura sama. Bayan kamar minti talatin, Islam ta fito daga dakin ta da akwatuna guda uku da handbag, sai jakar laptop a 'dayan hannun. Haj Zuwairah ta karbi d'aya tana murmushi, a lokacin Saifullah ya sakko da na shi akwatin guda biyu da brief case. Haj Zuwairah ta saki baki tana kallon sa, cikin turo baki gaba yace,

"Muje Mami, tunda duk mun 'dakko komai, sauran kayan sai zuwa da safe xan 'dauka."

Wani kallo Mami ta watsa ma sa, na 'kama rai na mun hankali', ta dubi Islam dake janye da akwatunan ta kafin tace,

"Auta ta! Yi gaba da akwati d'aya, ki sasu a motar ki, daga nan ki turo me gadin ku ya 'dauki sauran.."

"Tohm Mami.."

Cewar Islam, da kallo 'daya za kai mata, kasan tana matuk'ar farin ciki da barin gidan da zata yi, hade da adduar Allah yasa ba 'daki d'aya xa su zauna da Saifullah ba., Hannu Saifullah ya sa zai karbi hand luggage din hannun Mami, murmushi fad'ade a fuskar sa yana cewa,

"Mami kawo na taya ki da wannan, sauran sai Lado ya kwashe su."

Wani kallon ka ma renamin hankali Mami tabi saifullah dashi, cikin fushi ta cire hannun sa daga kan jakar, cike da fad'a tafara magana,

"Kar ka 'kara 'dora hannun ka akai kaji na gaya maka, tunda ka bad'a 'kasa a idanunka ka nuna bamu da 'kima ai magana ta 'kare, kuma zuwan da nai dama dan na tafi da Islam ne kawai, kamar yadda muka yanke shawara ni da mahaifin ka, kuma ko da wasa kar ka zo mana da maganar dawowar Islam gidan nan, ta gama zama anan gidan, daga can sai gidan su.."

Baki,hanci, idanu,haka Saifullah ya zubawa Mami sarautar Allah,har ta gama, sai a sannan ya dawo hayyacin sa, yana duban mamaki da kyau amma a zahiri jinjina kalmomin data fada yake, cikin rawar murya yace,

"Mami wallahi 'karya take min, ki kira ta kiji idan gaskiar al'amarin ta gaya miki, wall..."

Be 'karasa ba Haj Zuwairah ta haushi da fad'a, ta inda take shiga batanan take fita ba, ta 'kar'kare da,

"Kuma Islam ta gama zama a gidan nan kenan, Saboda haka kaje ka auro SON RAN KA, tunda ZAB'IN IYAYEn (Son Rai ko Zab'in iyaye?!, (littafi na)) da mu kai maka bai maka ba, kaga tafiya ta.."

"Mami please.."

"Please 'din gidan ku, ku ma ka maida akwatunan da ka 'dakko, mu ba 'kananan yara bane, kunyar daka bamu ta isa haka, ka je ka auro wadda tai maka.."

Saifullah yai kasa'ke yana kallon Mami, Tana gama magana yashjga bata hak'uri, sam idanunta ya rufe masifa kawai take surfa masa, ya dafe kansa yana salati, bakin sa 'dauke da duk addu'oin da suka zo masa, gefen bango ya kalla yana nanata kalmar,

"So suffocating.."

Mami dake 'kule dashi, jin abunda ya fad'a yasata zabga masa harara, zatai magana Lado ya shiga parlorn ya 'debi sauran akwatunan, zai had'a dana gefan Saifullah Mami ta dakatar dashi,

SAIFUL_ISLAM..💞(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now