FIVE

1.3K 83 1
                                    

Alhaji Muhammad Idris, 'dan asalin 'kauyen damboa ne dake jihar bornu. Kasuwancin bututun mai yake yi(oil mogul) yanada mata d'aya da yara biyar. Haj Latifa itace matar sa, yaran sa biyar 'din kuma uku daka ciki maza ne sauran biyun kuma, mata ne. Muhammad, Fatima, khaled, Humaira sai autan su Fahad.

Muhammad da Fatima kowannen su yayi aure, Muhammad na kaduna, Fatima kuma tana aure a kano. Khaled yana karatu a Spain. Gidah ya xama daga Humaira sai Fahad.

Unguwar su 'd'aya da gidan Dr Khaleel, amma su a 'kasan layin suke. Humaira itace sa'ar Islam domin makarantar su d'aya ma, ita Humaira na accounting shysa class 'dinsu ya banban ta, amma kawaye ne su tun suna 'kanana, komai tare ake musu, hakan yasanya aka sasu makaranta 'd'aya ta sakandire.

Sanadiyyar zazzafan 'kawancen su, hakan ya 'kulla babbar shak'uwa tsakanin iyayen su, sosai Dr Khaleel yake da share a d'aya daga cikin kamfanonin bututin man Alhaji Mommodu. Hajia Latifa kuwa 'kawance sosai sukeyi da Haj Aysa, kusan kullum tana gidan suna zantawa.

***

Shiryawa kowaccen su tayi cikin shiga ta alfarma, lokacin da xasu tafi gidan sunan a time din Marwa tadawo tana ta sauri flight dinta yakusa tashi xata koma 'kasar su, sallama sukai da Islam wadda duk tasake jin ba dad'i, ganin yanzu sai ita kad'ai babu kowa sai yan biyu dake 'dan 'dauke mata kewa suna tafiya ko'ina dan tuni har an yayesu, surutu a bakin su tamkar gidan radio.

Gidan sunan suka tafi, Farfajiyar gidan nan tasha decorations, ga abinci nan kowa xeyi serving kansa, masu jego sunci ado su Shema'u sai felek'e akeyi ita ga wadda ta haihu, 'Aunty Rama' ma tasha kyau, tana tsaye suna buga selfies da yan uwanta, wanda kallo ' 'd'aya xakai musu kasan ba 'yan Nigeria ba ne. Sashen 'Aunty Hafsy' suka shiga ganin bata wajen sunan, tana zaune tana gyara kwantacciyar sarkar gwal din ta,' mai makeup na gyara mata 'daurin 'dankwali ,

Tana ganin su ta fad'ad'a murmushin ta, tana musu sannu da xuwa,

"Kinyi kyau Aunty Hafsy" cewar Hafsat,

"Godia nake 'kanwata, baki da lapia ne?" Aunty Hafsy tafad'a tana 'karewa Hafsat kallo.

'Daga kai Hafsat tayi alamun eh, kafin tace,

"Eh wallahi Aunty, typhoid na keyi"

"Ayyah, Sannu Allah ya sawwake."

"Amin"yan 'dakin suka amsa.

Aunty Hafsy ta sake cewa,

"Sunan Daddy(Dr Khaleel) aka saka wa babyn, amma zamu dinga kiran sa da  'Sultan'" Ta d'ora da,

"Yammatan gidan mu, gaskia kunyi kyau, yadda muke da yammata zankad'a-zankad'a haka gaskia billionaires zamu samo duk mu aurar daku"

Yatsina fuska Islam tayi tana tura baki gaba, ita sam auren ma ya fice akanta, gani takeyi batada rabon yin sa, dubada ba wanda yake sonta, sai dai su so jikin ta, ita kuwa tafison wanda zai sota tsakani da Allah, ya 'kaunace ta ba dan yanayin siffar jikin ta ba, cikin 'kunkuni tace,

"Gaskia aunty a'a badai yanzu ba, duka-duka fa shekaran jia muka gama secondary school, talkless of university ga medical stuffs."

"Yen yen yen, Abeg duk kwayi a 'dakin maxajen ku" cewar Aunty Hafsy.

Ita dai Hafsat dake gefe danne-dannen wayar ta take yi, Hidaya ce ma mai saka baki, tana maganar ita kam ko gobe a 'daura mata aure a shrye take.

Sun 'dan taba shafta, kafin su sauka 'kasa wajen suna, an sha suna, anci an gyatse, an yi rabo, kowa ransa yayi fes, Nusrah ce kawai ke lallab'awa don itama takusa haihuwa, har aka gama tana zaune, sai da sukai isha'i sannan suka koma gidah.

SAIFUL_ISLAM..💞(COMPLETED✅)Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ