1

5.8K 201 10
                                    

بسم الله الرحمن الرحيم



*ABUJA*

   

   *A* jiye yaron da ke hannunta tayi akan gadon sa tare da d'ora kansa akan pillow irin na jarirai dinnan, wanda lokaci d'aya ya keta sharar baccin sa, ta shafe shi da addu'a,sannan ta dauki macen dake ta faman wangale wawulon bakin ta da babu hakori a ciki.

Kallo d'aya zakai wa yaran kasan cewar 'yan biyu ne.Tashi tayi ta dinga zagaye parlorn da yarinyar a hannunta, tana d'an jijjiga ta har sai da tayi bacci, sannan ta kwantar da ita a kusa da tagwai d'in ta.

Komawa tayi gefen su ta rage volume d'in tv da ketayi a tashar Africa magic yoruba. 'jenifa's diary' ake yi lokaci zuwa lokaci take d'an murmusawa, da alama sosai take jin dad'in drama series d'in.

Wayar tace ta fara rurin kara 'Miftahul qalb' shine sunan dake ta yawo a samab screen d'in wayarta ta, da azama ta d'auka tare da karawa a kunne had'e da mikewa a hankali tabar wajen gudun kada ta tashi yaran nata dake ta baccin su.

"Assalamu Alaikum Qalb.."

"Wa'alykm Salam sugar, yanzu na sauka fa" Cewar *SAIFULLAHI* dake janye da akwatin sa madaidaici a harabar airport d'in Lagos .

"Wayyo! Sannu qalb.. ka sauka lapia?!

Ubangiji Allah yasa albarka a abinda akaje nema, rabbi ya dawo daku lapia, yanzy dai ka samu abinci kaci banda shan abu mai sanyi dan Allah...kaji?"

Ajiyar zucia ya sauke, Allah ya sani yana matukar son matar sa da yaran sa, dole ce tasa yake nisa da su saboda yanayin aikin nasu, muryar tace ta sake dawo dashi daga tunanin su daya tafi ida take cewa.

"Kaji Zawj?"

"Na..Naji Love! Insha Allah bazan sha ba"

"Toh! Bari na kyale ka, ka huta tukunna anjima sai na kiraka muyi video call kaga 'yan biyun ka dan tuni sunyi bacci babu dadewa"

Shafa kwantaccen sajen sa dake kwance luf-luf a saman fuskarsa yayi, dan ba kad'an ba yana jin wani shaukin sonta na kuma ratsa shi yana lalata duk wani jini dake shiga jikinsa..

Cikin kasalalliyar murya ya furta,

"Okay love..! Yanzu zamu wuce ikoyi da Abbas anjima kuma zamuje ikeja filling station d'innan saboda traffic d'in lagos da safe..will call you when I'm done idan dare be yi nisa ba.."

"Okay zawj.. I love and miss you sai anjima.."

Sallama suka yiwa juna, bayan kowannen su ya sakarwa d'an uwansa zazzafan kiss ta wayar, cike da kadaicin junan su kowannen su ya katse kiran had'e da nannauyar ajiyar zuciya.

Komawa tai parlor wajen 'yan biyun ta dake ta bacci cikin nutsuwa. Tuni har angama shirin jenifas diary an shiga yin wani kuma, kallon agogo tayi 11 saura.

"Wai..haka dare yayi?.."

A gaggauce ta dau yaran nata ta takai d'aki, bayan ta canza musu kaya izuwa kayan bacci, band'aki ta fad'a wandake cikin d'akin tayo wanka hade da dauro alwala ta fito. Sai da tai nafilfilinta sannan ta koma kan gado tai azkhar na bacci hade da addu'oi na kariya ta tofe su sannan ta dauki wayar ta tana dannawa, ganin har sha biyu tayi bai kira ba, tasan lalle aiki ne ya rike sa. Gajeren message ta tura masa kamar haka,

_"Every day, I fall in love with you more. I don't know how that's even possible when I'm sure that I couldn't love you more than I love you now. I guess you just have this thing about you that makes loving you so easy and natural. I miss you already. Sleep now,honey. Sweet dreams. Allah ya yi jagora a abinda akaje nema"_

SAIFUL_ISLAM..💞(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now