KOWANNE BAKIN WUTA

814 50 0
                                    

🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by
    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄​*

 
Dedicated👇🏻
     *Classic Feedoh*👌🏻

            
             97


Daga sama taji maganar dan haka tai saurin juyowa ta kalle shi, kana nufin Ummi ce ke da ciki??

   Kasa yakara yi sosai da idon sa sannan yace"

    Eh"

Shiru tayi zuwa can tace"

   Toh Allah ya rabasu lafiya"

   Can kasan makoshi yace ameen"

  Shiru suka sake yi, sai dai abin daya bashi mamaki Mommy bata wani nuna murnan ta ba, bayan kuma tace tana son taga 'ya',yan shi"

   Zuwa can ya mike Mommy sai da safe"

   Toh Allah ya tashe mu lafiya"

   Ficewa yayi dan haka Mommy tabi bayan shi da kallo, tare da fadin"

Allah sarki, Allah ya jarabce shi da son Ummin nan, jiba shi ko kunya babu wai Ummi fah ciki gareta, duk zufin cikin nashi yau ya ajeshi gefe, sai wani murna yake"

   Murmushi tayi  sannan tace"

  Dana sani na tambaye shi wata nawa ne, mikewa tayi ta nufi daki tana mejin annan shiwa acikin  zuciyanta"

  
      *****

Shima Abdulmajeed gida ya nufa tare da addu'an Allah ya sausauto da zuciyan Mommy"

   Da wannan tunanin ya isa gida, Ummi najin tsayon motar shi ta fito"

   Adai dai lokacin da shima ya fito, kureta da ido yayi  sosai dan haka kunya ta dabai bayeta"

    Fuskan ta dauke da Murmushi takara tare da kokarin amsan jakar dake hannun shi"

   Maza yayi ya mika mata sannan ya hada su ya rungume tare da lumshe idon sa"

   Ahaka suka shiga gidan, afalon ya tsaya zuwa can yajata kan kujera ya zaunar sannan ya kafeta da  ido"

   Kanta a kasa jefi jefi tana tana dagowa ta kalle shi fuskanta dauke da kunya

    Ganin bashi da niyyar bari kuma fuskan shi babu murmushi ko fara'a yasa Ummi ta rasa inda zata yi"

   Dagowa ta sake yi ta kalle shi, dariya ce ta kama ta tai saurin toshe bakin ta tare da fadi"

   Yaya meye haka cinye ni zaka yi ne?

  Idon shi daya ya make mata tare da cigaba da kallon ta"

   Murmushi tayi sannan ta sunkuyar da kanta, zuwa can ta sake dagowa, har yazon be dauke idon shiba dan haka tai saurin saka hannunta ta rufe idanun shi"

  Murmushi yayi sanna yasa hannun shi ya cire nata tare dacigaba da kallonta, cikin dariya tace"

   Yaya wallahi kabari"

  Kafadan shi ya make  guda daya dan haka ta dage ta huramai iskar bakinta"

  Dole yasa ya rufe idon shi, ummi ko mikewa tayi aguje ta bar wajen"

   Yanajin gudunta ya bude idosa fuskan sa dauke da murmushi, mikewa yayi ya wuce dakin sa yana mejin wani irin farin ciki"

   Itama Ummi tana zaune abakin gadon ta tana murmushi tare dajin wani irin son sa me zafi cikin zuciyanta"

KOWANNE BAKIN WUTAWhere stories live. Discover now