KOWANNE BAKIN WUTA 11 to 12

3.9K 218 53
                                    

🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by
    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄​*

    Wattpad @fadeelalamido


         11 - 12


Itako Ummi tunda ta tare agidan Mukutar yake tarairayanta, cikin kwana biyun nan Ummi taga soyayya agurin Mukhtar wadda batai tunanin samun sa ba"

      "Yaso ya kusanceta tun adaren farko da aka kawota gidan sa amman tunda ya kula tanajin tsoro yabarta"

     "Manne da juna suke kwaciya bayan sunci wasan su sungaji"

    "Tunda mukhtar ya fahimci Ummi mutunce ita mason wasa ya biye mata suke lalacewa gurin wasanni da guje guje kamar wasu kananan yara"

    "Yauma kamar kullum bayan sun gama breakfast Mukutar ya kalli Ummi yace"

     "Kin koshi kuwa?

      "Nakoshi mana, kai baka koshi bane?

   " Shagwabe fuska yayi sannan yace"

    " Nakushi amman bakina be koshiba"

     "Mikewa tayi tsam ta zagaya ta bayanshi, ta sagalo hannunta wuyan shi, sannan tasa bakinta saitin kunnen shi ta make murya kamar me rada tace"

     "Yanzun yaya za'ayi??

    "Kunneta ya jawo shima ya make tasa muryan yace"

   " Muje gado muyi wasa sai mu mufito na kara"

    "Matsawa tayi da sauri tare da make kafada, wai kai baka gajiya na wasan agado?

    "Yafi dadi Ummi"

   "Kara make kafada tayi ni dai banso"

   "Mikewa yayi ya jawota jikinshi yace toke fada wadda kike so?

   " 'Yar tsere zamu yi"

   " Hancinta yaja tare da fadin me wayo"

     "Yana rike da hannuta suka isa filin da aka tanadar domin motsa jiki"

  "Yar tsere  suka shiga yi, sai dai  duk Mukhtar ne keyin na farko, dan haka Ummi ta hade fuska kamar zatai kuka"

   "Shiko Mukhtar yanata kwasan dariya tare dayi mata gwalo"

    "Tun tana dagewa ita adole saita wuceshi har tagaji tace, Bana yi"

    "Dariya sosai Mukutar yayi, ganin inda ta bata rai sai kunbura take"

   " Bayan ya tsagaita da dariyar yace"

    "Sweetheart yi hakuri ki sake gwadawa,  wannan karon kila ki dace, danna fara jin yinwa"

   "Jin yace haka, yasa ta yadda aka kara, aguje suka kwasa, wannan karon Mukutar ahankali yayi dan haka Ummi ta wuce shi, shiko kafin ya kasara ya fadi, yana fadin"

    "Wash, nagaji Ummi, wash kafana, wayyo cikina sweetheart  yiwa nakeji"

   " Dariya Ummi tai tamai zuwa can tafara mai gwalo tare da fadin"

    Nafishi jarunta"

  "Shima Mukutar dariya ne fal cikin shi, cikin nuna jarunta Ummi ta tallabo shi, suka nufi palon su, yana cigaba da fadin wayyo Ummi cikina kafafuwana sun rike"

KOWANNE BAKIN WUTAजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें