KOWANNE BAKIN WUTA

837 49 0
                                    

🔥 🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥
  _( da nashi hayakin)_
💨💨💨

               _Story & Written by_
    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄​*

           *70 to 72*



Abdulmajeed tafe cikin motar sa, sake sake kawai yake bayajin zai iya rabuwa da Ummi"

    Wata zuciyar ce tace ka mata abin da take so kawai"

   Tsaki yaja afili tare da fadin"

    Hakan na nufin nina gaza kenan? Kai ina bazai yiwu ba, bazan saketa ba, Ummi tawace danni akayita, shima Muktar din gangaci yayi harya aureta"

     Zaro ido yayi lokacin daya hango Ummi tana gudu agaban shi, ko tantama bayayi Ummi ce"

     Meyasata gudu haka?, meya sameta? Wuta ya kara wa mutar , cikin kankanin lokaci saiga shi agaban ta"

    Arikece ta nufo motar tana mata mata mahaukacin bugu"

    Shima Abdulmajeed arikecen ya fito ya rukota, Zainab meya same ki?

    Kirjinsa ta fada mutafi muyi sauri mubar nan wajen"

     Hannuwan shi yasa ya rungumeta ki natsu kinji KO, ki gayamin menene ya firgitaki haka?

     Ban da yarawa babu abun da jikinta keyi, nidai mutafi wani mutum ne yake bina"

     Hanyar yabi da kallo yana shafa bayanta yace"

    Bakowa anan gurin Zainab, daman haka kike da tsoro?, duba fah kafarki babu takalmi"

    Umm mutafi dan Allah"

    Rabata yayi da kirjin sa sannan ya nufi motar da ita"

    Bayan ta shiga ta zauna ya rufe motar sannan ya zagaya yana kokarin shiga motar, tare da waiwayen bayan sa, jakar Ummi ya hango can nesa, dan haka ya karasa gurin ya dauki jakar"

     Lekawa cikinta yayi komai nata naci har phone dinta, amfani yayi da wannan damar yasa hannu cikin ya fara lalubawa, nan yaje ya tabo wata leda ahankali ya zarota"

   Tunkafin ya budeta ya tabbatar wa kanshi sune dan haka yayi jifa dashi sannan ya taho"

     Samun Ummi yayi tanata zazzare ido tana waige waige"

     Jakar ya mika Mata sannan ya zauna, har suka fara tafiya batabar waigen bayanta ba"

   Shikuwa Abdulmajeed dariya yake kyalkyatawa acikin zuciyar shi, kai mata suncika tsoro yanzun hakama mahaukaci ta gani"

    Juyawa yayi ya kalleta, ki natsu mana ki daina irin wannan tsoron waye zai biyo ki?, ke dai kin firgita ne kawai"

    Cikin zare ido tace wlh wani ya biyo ni, kuma yamin kama da wadda nasa ni, banga fuskan shiba amman wallahi kamar nasan shi"

    Jim Abdulmajeed yayi, yana nazarin maganarta, zuwa can yace"

      Toh kiyi tunani da kyau"

    Itako.Ummi tsoron furtawa take gaban Abdulmajeed Amman yanayin jikinsa yayi kama dana Muktar"

    Suyi nisa atafiya yace"

     Ina zan kai ki?

   Gidan Mommy zani"

    Kauda kanshi yayi can gafe tare da fadin ko kunya babu"

KOWANNE BAKIN WUTAWhere stories live. Discover now