KOWANNE BAKIN WUTA

827 50 0
                                    

🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by
    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄​*

  Salam mabiya KOWANNE BAKIN WUTA a page din baya nayi kuskure wajen sunan Abokin Abdulmajeed *Sadiq*, nasa Faruk to ayi hakuri kuskure sunan sa *Sadiq* ne ba Faruk ba👏🏻

    *77 to 79*


Girgiza kai tayi da saurin ta tare da zobowan hawaye"

      Kallo yabita dashi dashi na tsayon wani lokaci, sannan ya mika hannun shi ya rungume ta"

     Wani irin kukane yazo mata me karfi Abdulmajeed be hanataba domin yana ganin kukan zaizama sauki azuciyarta"

    Bude baki tayi sosai tana raira kuka, duk da cewa tuni taso tai irin wannan kuka yaki zuwa amman kalamin Abdulmajeed ya fittar dashi"

     Yana nufin idan inaso yaje zaije ne?,  indai ko hakane wancen karon ma danni yaje badan su Abba ba kamar yadda yake fada ko yaushe, kuma indai zai min haka lallai bakaramin sona yake ba, daman andade ana gaya min sona yake yi bana yadda"

     To shi me yasa baya son nasa ni?, me yasa yake boye son da yake min?

    Adai dai lokacin da take wannan tunanin taji yana shafa bayanta tare da fadin"

    Ya isah haka Ummi, indai kina son inje zanje, amman karki sake yiwa kanki fatan komawa wata halitta daban, in kika koma haka mu kuma 'yan uwan ki yaya zamu yi?, koko mu bakya tuna nin Mu?, eyye Ummi Ahmad ne kadai azuciyar ki KO ???

   Tana kwace akirjin shi take girgiza Kai, tare da share hawaye"

      Shiko kara shafa bayan ta yake, tare da fadin hakane mana"

     Wani irin sanyi taji azuciyarta ganin inda Abdulmajeed yake rarrashinta, ji tayi tamkar duk duniya bata da wadda yafishi, son shi me zafi taji yana shigarta, samun me irin halinsa sai Antona"

    Ahankali tace"

  Bahaka bane yaya, kawai ban son ya kasance agarin ne, wlh yaya daya kasance agarin gara nasan mutuwa yayi"

     Shiru yayi zuwa cen yace"

  Zainab nasan idan ba ganin yaron ki kayi ba hankalinki bazai kwanta ba, kin dole zan tafi"

   Girza kai tayi a'a yaya baxaka ba, bon son kowa yaje, domin nasan yanzun sun gama shirya mana, babu abun da baxasu yiba akan duk wadda yaje, Yaya wallahi jiya nayi dana sanin auren Mukhtar"

    Wani irin sanyi yaji axuciyar shi, dan haka ya kara rungume ta, lamo tayi tamkar me bacci har na tsayon wani lokaci sannan ya dagota yana kallon fuskanta Ummi ina son na leka Office, amman bazan dadeba zan dawo"

    Mikewa sukayi tare yana tafe yana waiwayen ta kasa cewa komai tayi yana fita tace"

   Allah sarki, Ashe yaya Abdulmajeed yana da kirki haka?, hawaye ne sukayi ta zubo mata tana sharewa nan ta zauna tacigaba da tunani, harta dauki tsayon lokacin da bata sani ba"

    Sallaman Mommy ne ya katseta, cikin sauri ta mike tana yake"

   Mommy ma tana murmushi tace"

    Kin samu sana'a KO? hannunta ta ruko suka zauna akan kujera, daidai lokacin Abdulmajeed ya dawo, dan haka duk suka maida kallon su gareshi"


Mommy ya gaidar sannan ya nemi guri ya zauna"

KOWANNE BAKIN WUTAWhere stories live. Discover now