KOWANNE BAKIN WUTA

2.3K 142 80
                                    

🇺 🇼 🇦✨: 🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by
    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄​*

    Wattpad @fadeelalamido


            *22 - 23*





Eh akafa akeyinta dole, domin sun shaida min babu abin hawa ahanyar, kuma daji ne, babu gida gaba, babu gida baya"

    Nisawa Abdulmajeed yayi sannan ya sauke wayar ya kalli su Abba da suka tsare shi da idanu"

   Mikewa yayi yana shirin fita, Dadyy ya takatar dashi, tare da tambayan shi menene ke faruwa"

   Fuskanshi na dauke da damuwa yake sanar masu komai, game da garin, da Ummi take ciki, sosai hankalin kuwa ya kara tashi"

     Cikin kuka Umma tace"

   Anya kuwa Abdulmajeed za'abita garin nan, kaji fah ance akwai mayu aciki karkazo ka tafi ayi bawan ba kannin"

    Sunkuyar dakai Abdulmajeed yayi zuwa can yace"

    Zanje Umma ai bekamata abarta cikin wani haliba, duk inda take yanzun hankalinta ba akwance yake ba, ya kamata afiddata daga cikin damuwa"

     Daddy ne yace ai dole aje nemanta idan ta kama ma harmu sai mu tafi, kuma tunda yace zai iya inaga sai dai mumai addu'a, sannan asamo masa manin miyagu gurin Hajiya, saidai dole ya dage tafiyan zuwa gobe, domin mukarajin wani karin bayanin game da garin"

    Dahaka su daddy suka wuce gida, Abdulmajeed ko babu abin da yake Jinjina wa sai wannan tafiyan kafan domin shi be saba tafiya akafaba"

    Da yamma Sadiq ya ziyar ce shi, nan yake gayamai halin da Ummi ke ciki, ya nuna tausayawan shi agareta harma yace dashi za'ayi tafiyan"

    Mussaman Nafisa ta zubawa iyayenta karyan cewa, anzabesu amatsayin wad'an da zasu karaka doctor Abdulmajeed Habib wani babban Asibiti dake Niger domi kai ziyara ga marasa Lafiya kamar yadda ya saba"

    Dan haka batasha wahalan shawo kansuba suka amince mata"

     Shiko Sadiq sai da ya sanar da iyayensa gaskiya halin da ake ciki, hakama matarsa Fatima, rigima tasamai akan ita bata amince ba, ahankali yaita lallashin, tare da nuna mata matsayin doctor Abdulmajeed agurinsa, sannan ya shawo kanta ta amince"

   Daddy da kansa ya amsowa Abdulmajeed maganin miyagu gurin hajiya yasha ya turara wani sannan yabashi wani ya bawa abokin tafiyan sa"

    Washegari tunda asuba sukayi Sallama da kowa, suka dauki hanya, sosai sukasha addu'a agurin iyayen su"

    Tun dare Abdulmajeed ya zuba duk wani abu dayasan zai bukata acikin mota"

   Sudanyi nisa da gida Abdulmajeed yaja ya tsaya"

   Sadiq ne ya kalleshi yace"

   Muje mana yanaga ka tsaya ko har ka gaji ne??

    A'a ina jiran Nafisa ne"

   Nafisa kuma, mezaka mata Nafisa acikin halin yanzun?

   Juyar dakai Abdulmajeed yayi yana kallon waje, sannan yace"

   Munyi da ita Zata min rakiya ne"

   Subuhanallahi, Abdulmajeed wai meke damun ka?, ta yaya zaka dauki yariya budurwa kayi tafiya da ita, ina hankalin ka yaje?

KOWANNE BAKIN WUTAWhere stories live. Discover now