KOWANNE BAKIN WUTA page 5 to 6

2.2K 128 2
                                    

🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by
*Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄​*

Wattpad @fadeelalamido

5-6



🔥" Shiko Abdulmajeed yana daf da isa kofar falon Ummi ta fito tana zuba kamshi, daganin ta tana cikin farin ciki, kallo yabita dashi harta karaso daf dashi dan haka ta kyauce dan gudun karta gogi jikinsa"

"Harta gotashi yajuya yasa hannunshi ya jawota, tare da hadata da bango ya matseta, take Ummi taji tashiga wani yanayi wannda bata saba jinsa ba, domin hannun Abdulmajeed na sauka ajikinta taji kamar wuta ya jata"

"Banda zaro ido babu abinda Ummi take, tuni jikinta ya dauki yarawa dan inda wani ne yace mata Abdulmajeed zai yi haka zatace karya ne"

"Runannun idanunsa ya zuba mata, cikin daure fuska yace"

"Ina wasa dake ne??

"Cikin sauri ta girgiza kai"

"Wato dan kina murna saurayin ki yazo shine zaki angajeni ki wuce gurin wancen dan ciranin, kin wani sako turaren 'yan kuli, kenan adole zaki birge saurayi, ban da wari da karni babu abin da kike yi"

"Hawaye ne suka fara zubo mata, domin ita tasan bata gogi jikin shi ba, neman fitina kawai yake, ganin inda ya tsureta da ido yasa tace to kayi hakuri dan Allah"

"Dallah rufe min baki, banza mummuna kawai, me kama da mayu"

"Ran Ummi ne ya fara baci, dan haka ta sukuyar da kanta kasa, tare da zunburo baki"

"Wa kike murgudawa baki??, Abdulmajeed ya fada tare da kara matseta jikin bango"

"Sosai takejin wasu kasusuwa na jikinta na mata zafi, saboda matsan da yayi mata"

"Yan yatsunsa ya hada guda biyu ya d'ane mata baki, tare da fadin Mara kunya kawai, 'yar rainin hankali"

"Sosai taji zafi dan haka ta fashe da kuka tare da rike bakinta, jitayi har gurin ya kunbura"

"Cikin Zare ido yace kuma daga yau karna kuma ganin wani yazo gurinki da rana, me zai sashi zuwa da rana idan ba iskanci ba" wlh idan nakuma ganin sa daga ke harshi d'an ciranin sai kunci uban ku, sakinta yayi sannan yayi gaba ya shige cikin falon"

"Itako Ummi ganin inda ta koma firgai firgai yasata ta kasa fita, kuka take sosai dan haka takira mukutar awaya ta fadin mai abin da Abdulmajeed yayi mata, adabur ce yace, ya kuke dashi???

"Yayana ne, yaron wan Abba ne, shine wadda nabaka lbr"

"Cikin daburcewa ya sake yace"

Ummi bana son na rasa ki, idan na rasaki Ummi tamkar na rasa rayuwata ne, bazan iya rayuwa babu keba, dan Allah karki bari narasaki"

"Haba Mukhtar ai nagaya maka, anjenye zancen shi, ka kwatar da hankalin ka"

"Ummi ina tunanin idan iyayen ku suka fuskaci yana sonki zasu iya dawo da zance"

" Ai ba sona yake ba, shi dai kawai dan neman balaki ne, idan beyi ba bejin dadi"

"Waye ya gaya miki?, wlh Ummi Son ki yake yi"
Yanzun kina ina?

"Share hawaye tayi sannan tace, gani nan tsaye ina hango ka, bazan iya karaso wa bane, ya kunbura min baki, sannan yace ma wai wari nake"

"Dan murmishi yayi kadan, sannan yace, toh ki karaso mana Ummi, ni ke nake so, ba kwalliyar ki ba, kun buren bakin ki bazai sa inga munin ki ba, dan bashi bane agabana"

KOWANNE BAKIN WUTAWhere stories live. Discover now