KOWANNE BAKIN WUTA PART 1

7K 329 10
                                    

🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by
    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄​*

    Wattpad @fadeelalamido

*Bismillahi Rahamanir Rahim*

      
                1-2



🔥"Wata kyakyawan mota ce ta faka Awani dankareren gida, medan  karan kyau"

     "Motar ce tafi daukan hankalina dan haka ita na zubawa ido"

     "Zuwa can wani Zafgegen saurayi ya sakko daga ciki, Mai da hankalina nayi gurin kallon shi"

   " Dogone fari tas, shekarun shi zasu kai irin talatin da wani abu din nan, ga wani irin kyau da Allah ya zuba mai, kai kace balarabe ne"

      "Abu daya ya bani mamaki, fuskanshi babu fara'a ko kadan"

    "Zuwa can ya nufa cikin gidan, cikin zafin nama, tafiyan shima abin kallo ne, domin kuwa daka ganshi dole ka kauce ka bashi hanya"

    
       " Yana isa kofar da zata sadashi da falon ya ya tura kofar tare da sallama cikin wata siririyar murya"

     "Wata hamshikiyar mata nagani, cikin fara'a take amsawa tare da zuba mishi ido"

        " Kujeran dake kallon tata ya zuna, sannan ya bude baki daker yace"

    "Sannu da gida Umma"

   
    "Cikin fara'a matar tace"

     "Yauwa sannu *Majeed*, ya wajen aikin naka?

    "Murya ciki ciki, yace"

    " Lafiya Alhamdulillahi"

     "Yayi kyau, matar ta fada sannan ta dauki wayarta dake gefe ta fara dannawa"

    "Shima wadda aka kira da suna *Majeed* komawa yayi ya kwanta ajikin kujeran  tare da rufe idon shi"

     "Suna cikin haka wasu 'yan mata su biyu suka shigo, tare da cakakin surutun su, tare da shewa"

      "Wannan shewa tasu ita tayi sanadin bude idon *Majeed* tare da kara shan kunu"

    " Wata kyakyawan yariya nagani wacce tai tsananin Kama da wannan saurayin da aka kira da *Majeed*"

     "Sai dai tana ganin *Majeed* ta shanye dariyarta, dayar yariyar da take bayanta kuwa kallo tabi *Majeed* dashi sosai har ta fara mance a inda take"

      "Sai da ta gaban ta jawo hannunta sannan ta farga, dan haka suka karasa tsakiyan falon"

    " Umma ce tace ku kuma fah? kamar anjeho ku"

    "Fadawa jikin Umma tayi, ta kwanta, tare da fadin wlh Hajiya mun gaji ne, dayar ko zama tayi akasa cikin girmamawa ta gaida Umma "

    "Ahankali Umma ta fara shafa kan yariyar tare da fadin"

  "  *Ummi* wai bakiga *Majeed* bane???

"Batare da ta kalli *Majeed* tace"

  "Ina wuni?

    "Lafiya, ya fada ahankali, tun daga haka *Ummi* bata sake cewa komai ba" dan haka itama dayar tace"

    Ina wuni?

   " Lafiya, yace kamar yadda yacewa *Ummi* dan haka itama taja tai shiru, sai dai taso gaisuwan ya wuce haka"

     "Umma ce ta sake cewa, Ummi tashi ki haduwa *Majeed* abinci"

KOWANNE BAKIN WUTAWhere stories live. Discover now