Kowanne bakin wuta

1.1K 75 1
                                    

: 🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by
    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄​*

    Wattpad @fadeelalamido


    *SADAUKARWA*
Hannatu Adam
Faiza Musa Bunu
Maman Zaran
Hussaina Faji
Mmn kayra
Mmn Fahad
preety Zeee
Mariya
Deejahr
Nanacy
Beauty
Hadiza Tinau
      &
Hafsat Yusuf
👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻

          *21 - 22*




Dariya sosai Sadiq yayi zuwa can ya dakata da dariyar yace"

   Abdulmajeed kenan wani lokacin kana bani dariya, kamar yadda wani lokacin kake bani haushi, amman koma dai menene nan gaba zan tabbatar dashi, yanzun dai meye abin yi?, ko zamuje na rakaka kabawa Momy hakuri ne?, amman saika min alkawarin bazaka kara shan sigari ba"

    Cikin sauri yace nayi insha Allahu zanyi kokarin ganin nabarta"

     Dahaka suka kama hanyan zuwa gurin Momy, tana zaune apalo ganin Abdulmajeed tare da Sadiq yasa ta daure fuska"

    Nesa da ita Abdulmajeed ya zauna sannan Sadiq ma ya zauna tare da mika gaisuwa"

    Cikin daure fuska Momy ta amsa, sannan shiru ya ziyarci palon"

     Ganin inda Momy ke daure fuska, shi kanshi Sadiq ya tsorata, dan haka daker ya iya bude baki yace"

   Momy munzo ne domin mubaki hakuri, dan Allah kiyi hakuri Abdulmajeed yayi alkarin bazai kara ba"

  Hmmm, Sadiq, kaima haka kake?, karka yadda ka biyewa Abdulmajeed ku zama makaryata kuma munafukai, ko bakaga shi ko aure ya kasaba?, kasan me yake aikatawa? tunda har ya iya busa hayaki Allah kadai yasan abin da yake aikatawa, wlh Abdulmajeed yabani tsoro"

    Baya aikata komai Momy, auren ma ai ya kusa yi, ya samu yariya, dazanran sun gama daidaitawa zai kawo zancenta gida"

    Kauda kai Momy tayi sannan tace shi dai ya sani, kuma nariga nagaya masa indai yana son yagani kamar dah sai ya gyara halin sa"

     Ai yama bari Momy insha Allahu"

    Dahaka Momy tabar su afalo, Abdulmajeed ko be iya cewa komai ba"

   Washegari Abdulmajeed ya tashi ta tunanin hanyar dazaibi ya gano garin su Mukhtar, besan meye dalili ba, hakanan yakejin yana son yasan inda Mukhtar yakai Ummi har tsayon wannan lokaci basu dawo ba"

       ** **

Itako Ummi rayuwa ta mata tsanani, tunda kawayen Ummayo suka sa aka sakata wani daki wai da sunan dakin takaba, saita wuni bataga gilmawan mutum agurin ba, ko Ahmeed ba sosai ake batashi ba, yana gurin Ummayo so daya ake batashi arana kuma baya wuce awa daya take dawowa ta dauke shi, su biyu ake kawo mata abinci arana tun bata iya ci  harta saba"

    Kullum cikin hawaye take tare da data sani me tsanani, sai dai kuma mafiya yawan lokuta tanajin kewan Mukhtar na tsananin damunta, tare da tausaya mai, akowane lokaci tana mai addu'a domin kafin zuwanta wannan kyauye taji dadin zama dashi, bazatace ga wani abu mummuna wadda Mukhtar ya taba aikata mata ba, kuma ta tabbatar wa zuciyarta ba'a son ransa yabarta acikin wannan garin ba, asalima beso zuwa ba, dan babu yadda zaiyi ne, dan haka batajin zafinsa' tasan kaddara ita ta kawota garin nan tare dabin son zuciya"

   Irin wannan tunanin Ummi ke wuni tana yi tare da zubar hawaye"

   Tunawa tayi da lokacin da zasu shigo wannan kyauyen yadda Mukhtar yaita tarairayanta, har takalmin kafarsa ya cere yabata shiya tafi haka, sannan yaki nuna gajiyar sa duk da cewa yagaji din, amman be nuna ba haka ya dauketa daga ita har Ahmeed ya goya, yai tafiya me tsayi bace ya gaji ba"

KOWANNE BAKIN WUTAWhere stories live. Discover now