Kowanne bakin wuta

790 45 0
                                    

🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by
    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄​*

    *88 to 90*



Sadiq kasan fa babu wadda yasan da zuwan mu nan, naso ne kawai na koma da yaron, hakan zai rage fushin su"

     Toh Abdulmajeed ai yanzun yazama dole akira su domin Susan halin da ake ciki"

      Bazan iya kiran shi ba, ka kira shi kawai"

    Shiru Sadiq yayi zuwa can ya  miki ya yabar wajen"

   Ba jimawa ya dawo, kallon Abdulmajeed yayi, yace nagayawa Daddy yace zasu taso yanzu nan"

   Da sauri Abdulmajeed ya kalleshi zasu taso?, me zasuzo suyi?, kace musu subar shi kawai, muma yau zamu taso"

   A'a kabar su suzo din kawai"

  Sadiq meye amfanin zuwan su akwai nisa fah"

   Sadiq ya bude baki zaiyi mgn wayar Sadiq tai kara, cikin sauri ya dauka ya kara akunnen sa"

    Sadiq Ahmad ya rasu ko?

  Eh Abba"

  Toh ina Abdulmajeed din hadani dashi"

   Abdulmajeed din ya mikawa wayar yana fadin ga Abba"

    Abdulmajeed tun da babu yaron ai sai ku dawo gida ko?, zaman me kuke yi agarin"

   Cikin kasa da murya yace"

   Yau zamu taso Abba, amman sai anyi zana'ida"

   Abdulmajeed ban son rigima, ku taho kawai, wannan garin ban yadda dashi ba"

   Toh kawai yace yana mikawa Sadiq wayan ya mike ya koma dakin"

   Ganin Ummayo yayi rungume da Ahmad tanata kuka yayin da jafaru da Saminu suke bata hakuri suma idon su dauke da hawaye"

    Sadiq ne yace"

   Yanzun meye Abun yi, lokaci na tafiya banga anfanin zaman ba"

   Saminu ne ya kalli Ummayo yace"

    Ummayo barin samu mota mu isa gida"

    Cikin kuka Ummayo ta gyada kai, Sadiq ne yai karfin halin cewa"

    Me zai hana arufeshi anan domin muna son ayi zana'ida shi damu"

    Fuskan Ummayo face face da hawaye tace"

    Saminu miko min zani nagoya shi mutafi ka daina sauraran wadan nan mutanan"

   Mikewa Saminu yayi ya isa inda Abdulmajeed yake,"

   Yana zaune yayi tagumi yace"

   Kaji wai cikin kyauyen nan zasu kai shi"

   Mikewa yayi da sauri tare da fadin bazai yiwu ba sadiq, mezai hana arufe shi anan?

    To haka dai suka ce"

   Komawa dakin sukayi tare nan sukaci gaba da ja inja tun suna yi ahakali har suka daga murya"

   Nan mutane suka fara ta ruwa, ko wanne na tufa albarkacin bakin shi"

    Ganin inda Abdulmajeed yayi zuciya yasa Saminu yajashi waje yana fadin"

KOWANNE BAKIN WUTAWhere stories live. Discover now