KOWANNE BAKIN WUTA 29 to 30

748 64 1
                                    

*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by
*Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄​*

Wattpad @fadeelalamido



29 - 30



Komawa bayanshi tayi amman gani take kamar baya sauri, wanni irin tafiya yake ta takama gabanta"

Dole haka ta hakura tabi bayan shi, cikin tsananin fargaba, sosai Abdulmajeed ya kara kima a idonta, nan ta daukan makanta alkawri, duk zagin da Abdul zai mata bazataji haushi ba, domin tasan ta wahalar dashi"

Sunyi kamar tafiyan awa 4 zazzabi me zafi ya rufe Ummi, ban da rawan jiki babu abun da jikinta keyi, Abdulmajeed besan me take cikiba, domin shi yayi gaba, jin da yayi bejin takunta abayan shiba yasa shi juyawa"

Hangota yayi acan baya tana tahowa jikinta sai kerma yakeyi, sosai ta bashi tausayi, tsayawa yayi yana kallon ta harta karaso, ahankali yace"

Lfy kuwa??

Sanyi nakeji sosai Yaya"

Kauda kai yayi sannan yasa hannun sa ya taba jikinta, zafi rau yaji, dan haka yaji babu dadi ko yanzun yaya za'ayi kenan?

Cikin sauri ya Sakko da jakarshi ya dauko wasu magani tare da goran ruwa ya mika mata cikin rawan jiki ta karba ta rike ahannu, tare da fadin muje toh"

Muje ina??, magani fah na baki kisha kuma kina cemin wani wai muje"

Yamutsa fuska tayi nifa bana shan magani"

Ke! Karki kawo min iskanci maza kisha mu wuce mubar gurin nan"

Saka maganin tayi abaki, sannan ta zuba ruwan, kokarin kakarin amai take dan haka Abdul yace"

Wlh kikamin Amai saikin shanye shi"

Kara kunshe bakinta tayi, tare da zamewa kasa"

Kamar bazai taretaba, ahankali ya tsuna tare da kokarin dagata, amman Ummi kara kudundunewa take tamkar zata shiga cikin kasa"

Ganin haka yasa Abdul ya tsorata, rike cewa yayi saidai yana kokarin dannewa, cikin tausasasiyar murya yace"

Menene haka?

Sanyi nakeji yaya, bazan iya tafiya ba, dan Allah ka rufeni"

Dame zan rufeki Ummi, kin dai san babu wani abu anan gurin dan haka ki tashi muje"

Kara dunkulewa take guri guda, gashi yaron dake bayan ta ya dara kuka, babu yadda zaiyi dole ya dauke shi, hannunsa yasa ya kwace goyon ya dauki yaron, sannan ya mike ya rufeta da zanin, kin kallon fuskan yaron yayi duk da cewa yanata ma zuciyar shi fada ta bari ya kalli yaron amman ya gagara yin haka"

Akirjin shi ya kwantar dashi tare da buga bayan shi, harya samu yai shiru"

Juyawa yayi ya kalli inda Ummi take, tana rufe da bakin bayafi kalar kayan jikinta, amman jikinta bebar kermaba, kamar ma karuwa yake, tausayin ta yaji ya kamata, dan Allah wannan wacce irin rayuwa ce?, ahankili ya fara takawa inda take"

Tsugunawa yayi agabanta sannan yasa hannun ya taba jikinta, har yanzun zafin nanan "

Dan haka hankalin shi ya kara tashi, zama yayi agurin sannan ya dagota kwantar da ita yayi akan kirjinshi, sannan yasa hannun shi zagayeta, daga ita har Ahmeed lafewa sukayi akan kirjinshi, bayan ya gama kare mata kallo ya kwantar da kanshi akan nata"

Wani irin tausayinta yakeji wadda betabajin irinsaba, dan haka yaji kwala ta cika mai ido"

Mannewa Ummi tayi ajikin shi sosai, bakajin komai sai numfashin su"

KOWANNE BAKIN WUTAWhere stories live. Discover now