Kowanne bakin wuta

924 49 0
                                    

🔥 🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥
  _( da nashi hayakin)_
💨💨💨

               _Story & Written by_
    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄​*

            *68 to 69*

Sakin Ummayo Saminu yayi Tabawa wai lfy kuwa?

     Bakinta narawa ta nuna kofa tana fadin Muntari"

   Muntari? yayi me?

    Ya dawo"

  Ya dawo ina?

   Kofar take nunawa adaidai lokacin da aka fara buga kofar"

   Fitsari ne ya fara zubuwa tabawa yayin da Cikin saminu ya murda"

     Ummayo ce ta taho tana kokarin budewa, yayin daga can waje ake cigaba da bugun kofar"

     Ganin Ummayo na kokarin budewa yasa yaminu ya rike Ummayo sannan ya karasa bakin kofar yace"

    Waye??

   Nine

Jim Saminu yayi yanason ya tattace muryan dan haka ya sake cewa waye?

    Nine ka bude kofar mana"

   Eh muryan tayi kama data muntari saidai ya jin shine din ahankali ya sake cewa kaine Wa?

    Shiru yaji zuwa can yaji ance wai waye ne, Ummayo bata nan ne?

   Jin haka ya tabbatarwa kansa ba Muntari bane dan haka yacire sakatar ahankali ya bude kofar

   *JAFARU*

Ummayo ta ambata tare da rungume mutumin"

    Shima Saminu jin Ummayo ta ambaci sunan Jafaru yasashi tonawa da yayan su Jafaru da yabar gari tun bashi da cikkaken wayo"

     Tabbas kamar su da Muktar tabaci saidai Jafaru yafi Muktar baki kuma Jafaru fuskar shi akwai tabbai na yanka alamar anyi rashin ji"

    Shima rungume jafaru yayi, sun dade suna koke koke yayin da tabawa ta zama yar kallo"

    Bayan sun sarara daki Ummayo ta Jawo Jafaru har yanzon taki sakin sa"

    Kallonshi kawai take zuwa can tace Jafaru daga ina kake"

    Cikin wata irin murya yace"

    Kinaji KO Ummayo, ki basar da wannan zancen yanzun dai yaya kuke, ya kowa da kowa"

   Kowa Lafya Jafaru, saidai Muktar ya rasu tuntuni"

   Mikewa yayi cikin azama, nan danan ya fara tsiyayar da hawaye"

   Hakuri Hajiya ta shiga bashi tare da bashi labarin Muktar"

    Bayan ta gama faiyace mai komai ya fara share hawaye tare da fadin"

     Kinaji KO Ummayo ki kwantar da hankalin ki, bawani shegen dazai tabaki nabarshi, kin gane KO Ummayo, Ahmad zai dawo cikin kankanin lokaci, dama baki zubar da hawaye ba Ummayo, dama bakiyi kokaba, nake gaya miki KO bangon duniya suka kaishi sai sun kawo shi dan Uwar su"

      Sosai hankalin saminu ya tashi, cikin in ina yace"

     Ai Yaya ka kwantar da hankalin ka ma, indai jinin mune zai biyomu watarana"

     Jafaru ne ya kalleshi, banni dasu Saminu duk wani dan iska nine baban shi, kin gane KO Ummayo kibani sati biyu nake nake gaya miki, komai zaizama tarihi"

KOWANNE BAKIN WUTAWhere stories live. Discover now