KOWANNE BAKIN WUTA

798 44 0
                                    

🔥 🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥
  _( da nashi hayakin)_
💨💨💨

               _Story & Written by_
    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄​*

         
            *73 to 74*


Yana sauke wayar suka hada ido da Ummi, afirgice ya ganta dan haka yai kokarin saita kanshi"

    Yaya Lafiya?

    Lafiya lau, tafiya ya fara tare da fadin barin je na dawo"

     Bin bayan sa ta sake yi, tana kira yaya yaya dan Allah ka gaya min neye ke faruwa?

     Nace miki ki jirani ina zuwa ko, cikin motar ya shiga ya zauna  sannan yace ki koma ciki yanzun Zan  dawo karki sake kice zaki fito"

    Jikinta babu kwari ta koma cikin gida"

    Atunanin ta Abbane bashi da lafiya domin taji ya abbaci Abba"

    Abdulmajeed na isa ya samesu cirko cirko, aharabar gidan duk su Mommy da daddy suna gurin"

    Karasawa gurin yayi ya tsaya cikin yanayin dake nuna yana cikin rudu yace"

   Wai yaya akayi haka ta faru, shi kadai yake tafiya makarantar ne?

    Ai ba ama kai ga zuwa makarantar ba, duk yadda akayi acikin gidan nan aka dauke shi, Umma ce ke fadin haka adaidai lokacin take share hawaye"

     Juyawa Abdulmajeed yayi ya kalli me gadin yace"

    Wani ya shigo ne?

   Babu wadda ya shigo gidan nan me gida, tuda nadawo masallaci nake zaune aguri na babu wadda ya shugo kuma babu wadda ya fita"

    Dakata Baba, kana nufin shi kadai zai dauki kanshi? Karka raina min hankali mana, duk yadda akayi kanacen kana gyangyadin ka natsiya wani ya shigo gidan nan, ko kuma yaron yafita"

    Abba ne yace"

  Bana tunanin haka Abdulmajeed domin yaron nan betaba fita gidan nan shi kadai ba, duk yadda akayi anshigo gidan nan ne aka dauke shi"

    Hannu Abdulmajeed ya dunkule sannan ya bugawa dayan hannun sa, zuwa can ya shafa kanshi cikin neman abin yi, afili yace ta ina Zan fara ne"

    Abba ne ya dafashi tare da fadin"

    Ka kwantar da hankalin ka Abdulmajeed mubi komai ahankali, Allah zai kawo mana mafita"

   Abba hankalin Ummi zai tashi ban son taji wannan maganar"

   Wani irin kallo duk suka mai Daddy ne yai karfin halin cewa"

    Kai ka nutsu bamu san shashanci, idan ta kama ta sani ai dole ta sani, idan har bamu sameshi ayauba dole za'a gaya mata, domin addu'an uwa akan danta babban sinadari ne"

   Jikin Abdulmajeed sanyi yayi sosai zuwa can ya nufa motarsa tare da fadin ina zuwa"

    Abba ne yace"

  Ina zaka?

  

    Har ya tada Motar Mommy ta tuna jiya fah Ummi tace wani mutum na binta, dakatar dashi tayi tare da fadin"

     Jiyafa Ummi tace wani mutumi ya biyota aguje"

   Dakatawa Abdulmajeed yayi bayan gajeran nazari yace"

    Bana tunanin haka Mommy waye zai kama binta haka kawai, nafi tunanin mahaukaci ne ya biyota"

    Ba lallai mahaukaci ba, akirata domin muji daga gareta"

KOWANNE BAKIN WUTADove le storie prendono vita. Scoprilo ora