KOWANNE BAKIN WUTA

855 48 0
                                    

🔥 🔥🔥🔥🔥🔥
*KOWANNE BAKIN WUTA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥
    ( da nashi hayakin)
💨💨💨💨💨💨💨

Story & Written by
    *Fadeela Lamido*

*​© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄​*

    *91 to 92*




Ummi na shiga ta hango Abdulmajeed na kwance idon sa rufe*

    Kusa da kujeran daya ke kwance ta zauna akasa sannan ta kamo hannun shi tana me zubar da hawaye"

   Cikin baccin daya dan fara diban shi yaji ana taba hannun shi, bude ido yayi ahankali ya kalleta"

   Wani irin sanyi yaji azuciyan shi, dan haka ya lumshe ido"

   Ummi kiwa tana kuka ne tana murza hannun shi"

    Zuwa can  ya bude idon sa yace"

    Zainab kinji mummunan labari ko, kiyi hakuri jarabawa ce daga Allah, duk abun da ya tsara babu me iya canzawa"

    Hawaye na tsiyaya afuskan ta tace"

    Yaya ba komai Allah yasa haka shine mafi alheri"

   Amin ya fada ahankali, shiru sukayi na wani lokaci, zuwa can Ummi tace"

    Nagode Yaya Allah ya saka maka da alheri, domin abin da kamin arayuwa bazan iya biyan kaba"

   Hawaye sosai yake zuba a idonta, dan haka Abdulmajeed ya tashi ya zauna tare da kama kafadun ta, yana kallon cikin idonta yace"

   Ai ba nayi bane dan ki biyani, zuciyata ce bata son ganin ki cikin damuwa dan haka daga yanzun bazan kara takura miki ba, duk abin da kike so shi zan miki"

   Wani irin kallo tamai, acikin zuciyanta tace ban gane duk abin da nake so ba?, afili kuwa binsa da ido take"

    Kula tayi har yanzun rawan sanyi yake yi, dan haka tace"

    Kasha magani kuwa??

   Nasha amman kinga har yanzun be sauka ba"

    Shiru tayi zuwa can ta kara yawan kukan ta"

   Mene ne kuma?

   Yaya ni tsoro nakeji"

Tsoron me?

  Yaya inajin tsoron kar wani abu ya faru dakai"

  Murmushi yayi kamar me misali?, mutuwa?

  Kaita daga mai alamar eh"

   Murmushi ya sake yi sannan yace"

   Ai mutuwa dole ce Ummi idan tazo babu yadda zamu yi"

   Kanta ta hada da kujera tare da sheshekan kuka"

   Kallon ta yayi yana me son ya gano wani abu, bayan ya gama nazari akanta yasa hannun sa ya dagota sannan yace"

   Ke wasa nake miki ba yanzun zan mutuba,  gajiya ce tamin yawa dazaran na samu bacci zan warware"

   Hannu yasa yana share mata hawaye, dan haka Mommy dake tsayi bakin kofa taja tsaki sannan ta juya tana kokarin fita tare da fadin,

   Banza salla mamme, ya zauna yar kankanuwa yariya tana mai abun da ranta keso, shiko kullum burinsa ya faranta mata rai, zanyi maganin ku in kusan wata ai bakusan wata ba"

  Itama Ummi fitowa tayi ta koma cikin jama'a"

  Shiko Abdulmajeed sai yamma ya samu zazzabin ya sauka dan haka ya fice babu wadda ya sani yabar gidan"

KOWANNE BAKIN WUTANơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ